GGSS Jangebe : Yadda muka ji da sace ƴaƴanmu - Iyayen ɗaliban

GGSS Jangebe

Wasu daga cikin iyayen ɗaliban da wasu mahara suka sace a makarantar sakadiren mata ta GGSS Jangebe a jihar Za,mfara sun shaidawa BBC irin halin da suka shiga sakamakon faruwar wannan al'amari.

Ɗaya daga cikin su da muka sakaye sunansa ya ce wannan abu ne da a baya suke jin yana faruwa a wani wajen, kwatsam sai gashi ya juyo kansu, abun da basu taɓa tsammanin zai faru ba.

''Biyu daga cikin 'ya'yana aka tafi da su, akwai yar shekara 10, akwai yar shekara 13, bana gari a lokacin da lamarin ya faru, kawai sai wani malamin makarantar ya kirani yake faɗa mn cewa 'ya'yana na cikin daliban da aka sace'' inji shi.

A cewarsa zuciyarsa ta riƙa tafarfasa a lokacin da ya ji wannan labari, lamarin da ya sa ya kama hanya ya koma gida, kai tsaye kuma ya zarce zuwa makarantar, sai dai kayansu kaɗai suka kwashe suka mayar gida.

''Rabona da su tun ranar Litinin da zan yi tafiya, lokacin ne na fita na barsu, sannan lamarin nan ya faru ne ba jimawa da sake komarsu makaranta..

Sai dai yace duk da faruwar wannan al'amari hakan bazai rage masa ƙwarin guiwar tura 'ya'yansa zuwa makaranta ba, ko da yake ci gaba da faruwar hakan ba shakka zai kawo gagarumin naƙasu ga harkar ilimi.

Sh kuwa wani ɗaya daga cikin iyayen ya bayyanawa BBC cewa ''Wurin karfe 1 na dare ina zaune da iyalinna sai muka fara jin ƙarar harbe harbe ko ta ina, abin da ya ci gaba da ƙaruwa har zuwa kusan awa uku.

''Iyalina suka ce garin ga lahiya kuwa ?, nace musu kowa yaje ya yi adu'a ya koma ya kwanta, to ban sake samun labarin me yake faruwa ba sai da gari ya waye, bayan na je sallar Asubah, sai ake cewa yara ne aka sace daga makarantar mata'' inji shi.

Ya ce a lokacin da ya je sai ya tarar da cewa daliban da suka rage basu da yawa, an tafi da sauran, ciki kuwa harda ɗaya daga cikin 'ya'yansa biyu da aka tafi da ita.

Gwamnatin jihar ta rufe makarantu

Gwamna Matawalle na Zamfara

Asalin hoton, GoVMATAWALLE

A halin da ake ciki dai gwamnatin jihar a ta bakin gwamna Bello Muhammad Matawalle ta bada umarnin rufe dukkan makarantun kwana a jihar sakamakon wannan al'amari da ya faru.

A wani jawabi da ya gabatar wa al'ummar jihar ranar Juma'a da yamma, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tabbatar da isashshen tsaro a dukkan makarantun jihar.

Gwamna ya yi kira da a kwantar da hankali tare da cewa ana ƙoƙarin ceto ƴan matan da aka sace .

A nata ɓangaren rundunar yan sandan Najeriya ta ce tuni ta dukufa domin tabbatar da ceto daliban da aka sace lami lafiya.

Sai dai duk da haka iyaye da kuma 'yan uwan ɗaliban da aka sace a makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara sun bi sawun 'yan bindigar cikin daji.

Wasu daga cikin iyayen sun shaida wa BBC Hausa cewa sun yanke shawarar bin sawun yaran nasu ne da zummar ceto su daga hannun miyagun.

"Gaba ɗaya garin Jangebe ne muka tasan ma ɓarayin, ko mu dawo da ranmu ko a kashe mu," a cewar wani da aka sace ƙannensa biyu.

Timeline Factory

Hit link on top ⬆️ to find your timeline.