GGSS Jangebe: Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata 317 a Jihar Zamfara'

Wasu rahotanni sun ce dalibai hamshin da hudu ne kawai suka rage a makarantar
Bayanan hoto, Wasu rahotanni sun ce dalibai hamshin da hudu ne kawai suka rage a makarantar

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace ɗalibai mata 317 daga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara.

Cikin wata sanarwa da kakakinta na Jihar Zamfara SP Mohammed Shehu ya fitar, rundunar ta ce jami'an tsaro na haɗin gwiwa sun bazama cikin daji domin ceto ɗaliban.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata kusan 300 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Gwamnatin jihar ta Zamfara ta tabbatar da sace daliban.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Abin da ya faru

Kabiru sani, mataimakin shugaban Muryar Talaka ta jihar Zamfara, wanda aka sace 'ya'yan dan uwansa uku, ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun soma fasa kofar shiga makarantar sannan suka ci karfin mai gadinta kafin su sace daliban.

A cewarsa, barayin sun kwashi 'yan mata "sama da 374, 'yan matan kuma na jihohi ne daban-daban; akwai na Kaduna, Sokoto, Kano, da Jigawa da Kebbi."

"Da suka shigo sai suka kewaye makarantar, suka kewaye duk inda suke tunanin jami'an tsaro za su bi. Sannan suka balla kofar makarantar. To, akwai mai gadi ya taso sai suka harbe shi, da ya ga sun fi karfinsa sai ya tsere.Kawai sai suka soma shiga hostel-hostel na 'yan mata suka rika cewa 'ku tashi, ku tashi Sallah za a yi. 'Yan matan na tashi sai suka gansu da bindigogi. Haka suka bi hotel-hostel suna tara su suna tafiya da su," in ji shi.

Kabiru Sani ya ce sauran matan da suka rage a makarantar "su hamshin da hudu ne kuma an tara su wuri guda."

Ya ce yanzu haka sun shiga daji domin bin sahun 'yan bindigar.

Haka kuma wani mutum da aka sace 'yarsa daya mai suna Bilkisu da 'ya'yan 'yan uwansa biyu, ya ce daruruwan 'yan bindiga ne suka isa makarantar inda suka soma da kai hari kan masu gadi kafin su yi awon gaba da daliban.

Dalibai na tserewa daga makarantar

Iyaye suna kwashe 'ya'yansu daga makarantar
Bayanan hoto, Iyaye suna kwashe 'ya'yansu daga makarantar

Wasu rahotanni da muka samu sun nuna cewa ragowar daliban da suka rage a makarantar sun soma tatara kayansu suna ficewa zuwa jihohinsu.

Sai dai ganau sun tabbatar mana cewa an jibge jami'an tsaro a ciki da kewayen makarantar.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan fashin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Gwamnatin jihar ta ce yin sulhu da 'yan fashin dajin shi ne mafita daga wadannan matsaloli duk da yake suna ci gaba da kai hari kan jama'a suna kashe su sannan su sace wasu.