Arewacin Najeriya na cikin halin ha'ula'i in ji Ƴan Twitter

Asalin hoton, Getty Images
Shafukan sada zumunta da muhawara sun ɗau zafi a Najeriya inda mutane suke kokawa tare da bayyana ra'ayoyinsu kan halin da yankin arewacin ƙasar ya samu kansa a ciki na rahin tsaro.
Wannan na zuwa ne bayan da aka sace sama da ƴan mata 300 daga makarantar sakandarensu ta Jangebe a jihar Zamfara a daren Juma'a, kwanaki kaɗan bayan sace wasu ɗaliban da dama a makarantar sakandaren Kagara a jihar Neja.
Lamarin ya ɗaga wa ƴan ƙasar hankali, shi ya sa ma wasu suka bazama shafukan sada zumuntar don bayyana ra'ayoyinsu da yin tur da Allah-wadai da "masifun" da ke faruwa a yankin.
An ƙirƙiri maudu'ai da dama don tattauna batun musamman a shafin Twitter, kamar su #North wanda aka yi amfani da shi sau fiye da 250,000 da #Zamfara da aka yi amfani da shi sau fiye da 50,000.
Wasu kuma sun yi ta amfani da #RescueJangebeGirls, wato a ceci ƴan matan Jengebe, sai masu amfani da #Bandits, wato ƴan bindiga.
Mafi yawan masu tsokacin suna kokawa ne kan rashin tsaron ya yadda ƴan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, sannan "gwamnati ta bar abubuwa na ci gaba da faruwa akai-akai ba tare da magance su ba."
Sannan lamarin a Tuwita ya so ya sauya akala ta inda ƴan kudancin ƙasar suke nuna cewa wannan matsala ce ta ƴan arewa kawai kuma su suka jawa kansu, "ga su da shugaban ɗan yankinsu amma suna ganin abin da suke gani."
Su kuwa ƴan arewa ba su ma bi ta ƴan kudun ba wajen mayar da martani, sun fi tofa albarkacin bakinsu ne kan kira ga hukumomi su ƙara ƙaimi.
Ga dai abin da wasu ke cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Aproko Doctor ya ce: "Satar mutane ta ko ina. Rayuka na cikin haɗari. Ilimi a arewa na fuskantar barazana. Duk saboda gwamnati ta gaza wajen yin abin da ya dace: Kare ƴan ƙasa."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Surayyah Ahmad ta ce: "Wannan ta'addancin duk sai ya cinye mu idan har ba mu farka mun yi magana tare da samun mafita daga gwamnati ba.
"Babu wata dukiya da yawanta zai samar mana da tsaro ga mu da iyalanmu a duk faɗin arewa. Wannan ba siyasa ba ce, rayuwarmu na kan siraɗi!"
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Shi kuwa Bello Shagari @Belshagy cewa ya yi: "A baya ɗan kudu ne yake mulkin ƙasar nan amma sai aka dinga zargin kafatanin kudancin ƙasar, yanzu kuma ɗan arewa ne yake mulki sai ga shi ana ta zargin dukkan yankin.
"Har yanzu ba mu koyi daina nuna wa juna yatsa da zargin juna ba. Gwamnati dai a can sama kanta a haɗe yake ko da kuwa waye yake mulki. Tare suke aiki!"
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Ayemojubar @ayemojubar ko cewa ya yi: "A lokacin Jonathan an sace ƴan matan makarantar sakandaren Chibok.
"A lokacin Buhari kuwa an sace ƴan matan sakandaren Dapchi da samarin sakandaren Kankara da na Kagara da kuma ƴan matan nan na Zamfara .
"Bai kamata a ƙyale Buhari kan batun nan ba, kuma har yanzu mamaki nake ko me ya sa da yawan mutanen arewa da abin ke faruwa suke yin shiru."