Daga baƙonmu na mako: Yadda habaici ya koma dandalin WhatsApp da Facebook da Instagram

Umma-Salma Isa Aliyu, ɗaliba mai karatun digiri na biyu a ɓangaren Adabi a Jami'ar Jihar Kaduna, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harshe, ita ce baƙuwarmu ta wannan makon.

Umma-Salma Isa Aliyu, ɗaliba mai karatun digiri na biyu a ɓangaren Adabi a Jami'ar Jihar Kaduna, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harshe, ita ce baƙuwarmu ta wannan makon.

Asalin hoton, Umma-Salma

Bayanan hoto, Umma-Salma Isa Aliyu, ɗaliba mai karatun digiri na biyu a ɓangaren Adabi a Jami'ar Jihar Kaduna, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harshe, ita ce baƙuwarmu ta wannan makon

Kowace al'umma ta duniya tana da hanyoyinta na zantuttukan hikima da take amfani da su a cikin harshenta don nuna gwaninta da kinaya da dabara da ɓad-da-bami a cikin harshen yayin da buƙatar hakan ta samu.

Harshen Hausa cike yake da zantuttukan hikima na wanda za a iya cewa ana yin su ne ba kurum don nuna ƙwarewa da basirar sarrafa harshe ba, ana kuma yin amfani da su domin isar da sako cikin nishadi.

Kenan harshen Hausa cike yake da zantuttukan hikima masu ƙayatarwa, kamar su habaici da karin magana da kirari da sauransu.

Habaici abu ne mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar Bahaushe wanda ya kasance Bahaushe na yin amfani da shi a kusan dukkan ɓangarori na rayuwarsa da adabinsa da suka haɗa da waƙa da zube da wasan kwaikwayo da sauransu.

Habaici salon magana ne da Bahaushe ke amfani da shi wajen isar da wani saƙo a hikimance ta cikin zance. Wannan saƙon zai iya kasancewa gargaɗi, huce haushi, jan - kunne da sauransu.

Magana ce da ake yinta a cikin duhu, ma'ana, ba kai-tsaye ake fito da maganar ba, sai dai shi wanda ake yi dominsa ya san inda aka dosa.

Ko kuma idan abin ya shafi wani laifi ne da mutumin ya aikata, to duk wanda ya san ya aikata laifin shi ma zai iya sanin inda aka dosa. Amma in ba haka ba, sanin inda aka dosa cikin habaici yana da wahala.

Kenan Bahaushe na amfani da habaici ne domin isar da sako a kaikaice ta yadda idan ba kasan me ake nufi ko kuma ga wanda ake wa, ba lailai ba ne ka fahimta.

Short presentational grey line

Habaici jiya da yau

WhatsApp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, WhatsApp status a yanzu shi ne babban dandalin yada habaici

A da hanyoyin da ake bi wajen yin habaici sun haɗa gugar zana da karin magana da harbin iska, da sauransu.

Misali, idan wani ya sayi wani abu kamar abun hawa haka, ana iya bayyana hassadar da ake yi masa ta cikin habaici. Misali, a ce, mu ma dai mun kusa sayen motar nan.

Za a gane cewa hassada ce idan aka lura da cewa a nan mai faɗin maganar maimakon ya taya wanda ya saya murna sai ya ɓuge da cewa shi ma dai zai saya.

Idan wani ya shiga sabgar wani a wani lokaci, yana iya bari daga baya ya ce, daga yau in mutum ya ƙara shiga sabgata, sai na turmumusa shi ko ci masa mutunci.

Irin wannan jan-kunne ake yi amma ta cikin habaici, maimakon a ce wane daga yau in ka ƙara shiga sabgata zan yi maka kaza. Ko kuma a ce, wane, daga yau hawainiyarka ta kiyayi ramata ko idan mutum na cin ƙasa ya kiyayi ta shuri. A nan kuma an yi habaici ne mai kama da karin magana.

Idan wani ya nuna son ya mallaki wani abu, za a iya cewa da shi, nan gani, nan bari. Ko kuma a ce ƙwalele dokin Iliya, ba ni sayar da kai, ba ni ba da aronka, da sauransu.

Waɗannan duk misalan habaici ne a jiya ko a da, amma a yanzu kuma habaici an daina yinsa a gaban mutum ko kuma a bayansa ko a inda baya nan, sai dai yanzu an koma kan kafar sada zumunta, a can ake yinsa, kasantuwar sauyin zamani, kuma dama masu hikimar magana na cewa"zamani riga".

Sakamakon hanyoyin da ake da shi na sadar da zumunta musamman na WhatsApp da Fesbuk da Instagiram, wasu suna faɗin damuwar a nan wurin.

Cikin halin da ake ciki a yanzu da ya zama akwai hanyar da mutane ke nuna damuwarsu ba tare da sun faɗa wa wani ba fuska da fuska kawai dai sai dai su sa a Fesbuk dinsu ko a Whatsapp dinsu wanda a wurinsu su sun bayyana damuwarsu.

Wannan layi ne

Warware matsalar damuwa

Matsalar damuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matsalar damuwa kan sanya wasu amayar da damuwar tasu ta hanyar yin habaice-habaice a shafukan sada zumunta

Akwai mutanen da idan abu na damunsu, in dai suka bayyanawa ko da ga mutum ɗaya ne ko suka rubuta abin da da ke damunsa a wani wuri, za su samu saukin damuwa, wanda rashin bayyana wannan damuwar, yana sanya musu cutar damuwa wato 'Depression' a Turance.

An taɓa tattaunawa da wani masanin ilimin ƙwaƙwalwa wanda ya kammala Kwalejin Jinya kuma ya zauna a asibitin Malam Aminu Kano na AKTH, sashen masu taɓin hankali da kuma damuwa na ɗan wani lokaci, ya faɗi yadda damuwa da ke da alaƙa da hauka da kuma alaƙarsu da kuma bambancinsu.

Ya ce: "Hauka, jam'i ne na wasu ayyuka da suka saɓarwa hankali. A misalinsu akwai Mania, Depression (damuwa), Bipolar, Schizoprenia da yawa-yawansu.

Akwai bambamci a tsakanin depression din shi ma domin akwai depression ta psychiatric disorder, da kuma depression na yau da kullum.

Ita waccen akwai 'rasa kai……. Wato akwai rashin jituwa sosai tsakanin MOOD, THINKING da AFFECT….

Babu mahalukin da ba ya zama depressed. Ya danganta da zurfin depression ɗin.

Babban maganin depression su ne: ka da mutum ya ɓoye damuwarsa kwata-kwata, ya fada wa wani amini.

Ana so mutum ya yi cuɗanya da jama'a, wato ka da ya ɓoye kansa daga sauran mutune, ya ce shi ba ruwansa da kowa, ana so mutum ya karɓi ƙaddara a kan komai, sannan idan ciwo ne ke damun mutum to ya nemi magani da sauransu."

A sakamakon waɗannan kafofin na sada zumunta na zamani musamman na WhatsaApp da Fesbuk da Instagram, sun taka muhimmiyar rawa wajen yayewa mutane damuwarsu da ta addabesu a cikin zuƙatansu.

Domin sun bayar da damar da kowa zai yin tofa albarka cin bakinsa ko da kuma ta hanyar habaici ne.

Wannan layi ne

Sabon Salo Habaici a Kafar Sada Zumunta (Social Media)

Instagram

Asalin hoton, Getty Images

Kafar sada zumunta( social media), fasahar sadarwa ce ta zamani da jama'a ke sada zumunci daga sassan duniya daban- daban, wacce aka fara samunta a shekarar 1997.

Daga cikin ire-iren wadannan shafuka sun hada da;

Wassaf (Whatsapp) da Fesbuk (Facebook) da Tuwita (Twitter) da Instagiram (Instagram) da Yutub (YouTube) da Sinaf cat (sSnap chat) da Tugo (2go) da Biba (viver) da Imo( imo) da Wicat (we-chat) da sauransu.

Wadannan hanyoyin sada zumunta sun zamanto ababen da ake amfani da su wajen isar da sako ga wanda ake son a isarwa, musamman waɗanda suke ba da damar tura saƙo (chat) da kuma sakon na musamman na awa 24 wato (status )musamman ma a kafar sada zumunta ta WhatsApp da Fesbuk da kuma Tuwita.

Ana amfani da waɗannan kafafen ne wajen yaɗa habaici musamman idan husuma ta samu tsakanin abokai ko a zamantakewa tsakanin kishiyoyi ko tsakanin saurayi da budurwa ko ƙawaye ko 'yan siyasa da sauransu.

Sai su koma 'status' suna habaici, ba a fadi gaba-da-gaba sai a fada a nan duniya ta gani.

Alal misali, bari mu daukin kafar sadarwa ta WhatsApp, na taɓa gani wani saurayi da budurwa da suka yi fada, kasancewar dukkannin su ina da lambar wayarsu, hakan ya ba ni damar ganin sitatus dinsu. Ga kuma abin da ya wakana tsaninsu kamar haka:

"Banza a dai yi mu gani, ba dai sai na ba da kai bori ya hau ba tukunna, auren dai na fasa kuma ba mai sani dole". Wannan shi ne saƙon habaici da budurwar ta ɗora akan sitatus ɗinta wanda yake nuna da cewa saurayinta ya ɓata mata rai kuma ta yanke hukuncin fasa aurensa.

Ganin sakon habaici da budurwar ta sa a sitatus, sai wannan saurayin nata ya tura mata da amsar kamar haka "ai ni ne na gani na ce ina so ko? To na fasa idan mutun kuma ya ce zai min rashin kunya in kai ƙararsa kotu dawo min da duka kaya da duk kuɗaɗen da na kashe a kan mutum".

Wannan shi ne amsar da ya bai wa budurwa cikin habaici cikin magana, wanda in dai mutum bai san kan zance ba to, ba zai fahimci da wa ake ba, amma dai mutum zai iya fahimtar cewa ya yi faɗa ne da wata.

Bayan wanna kuma akwai wata kuma wacce ta ɗora a status cewa: "Na gaba ya yi gaba na baya sai labari, duk rashin kunyar yaro haka ya zo ya ganmu haka kuma zai tafi ya bar ni".

Wannan saƙon wata uwargida ce ta yi wa amaryarta bayan sun yi rikici amma aka sanya a sitatus. Tana faɗa mata magana cewa ita ce babba kuma babu yadda za a yi da ita.

Kenan maimakon ta je ta same ta gaba da gaba ta fada mata sai kawai ta koma sitstus ta bayyana wa duniya abin da ya faru.

A kafar sada zumunta ta Fesbuk ba ta sauya zani ba domin ana amfani da turaka(time line/profile) ana yaɗa habaici kuma ana turo saƙonnin a shafin da ya hada da habaici ga wanda ake san isarwa.

Wannan layi ne

Misalan habaicin daga kafar sada zumunta ta Fesbuk sun hada da:

"Taka ta Allah ce, wasu sun biye wa 'yan nanaye kwaɓarsu ta yi ruwa".

"An zo wurin, ashe wanzami ba ya son shaushawa! Sai ka kwashi adashen da ka zuba, ko ka ƙi ko ka so".

"A duk lokacin da aka bar damo har ya kai zama guza, to ƙarshe abin da ya ci doma ba zai bar awe ba".

Dukkannin waɗannan habaici duk an yi su ne da wata manufa ɓoyayyiya sai dai ba a fito fili an fadi manufar ba amma dai su wadanda aka yi don su za su fahimci ko me yasa aka yi wannan habaici.

Kuma dama maƙasudin habaici shi ne isar da sako a kaikaice cikin hikima wacce mutum bai san da wa ake ba, ba zai fahimta ba.

Akwai bambanci a tsakanin sitatus din WhatsApp da na Fesbuk, bambancin kuma ba wani abu ba ne illa shi na WhatsApp waɗanda kake da lambarsu kuma suke da lambarka su suke ganin sitatus dinka, amma a kafar sada zumunta ta Fesbuk zance ya sha bamban domin kowa zai iya ganin abin da ka saka musamman idan ya kasance yana biye da shi (following).

Haka kuma tsarin yake a Tuwita (twitter) da instagiram (Instagram).

Idan muka leka kafar Instagiram shi ma, ana yi habaici ko dai a sitatus ko kuma a shafin tsokaci(comment section) ko kuma bayan an tura wani hoto ko bidiyo. Misali akwai wani sakon da aka turo a wani shafi na Northern Hibiscuss.

Ita mai wannan shafin ta saka hoton da aka yi bayani kamar haka "A biya bashi ehe!!! Mun gaji da gafara sa".

A kasan wannan hoton sai ta sa "abin ya zama cin fuska Wallahi. Haba mana. Ka lallabo ka ce a baka bashi sai lokacin karbar bashi kai ta yau gobe yau gobe?"

Ko ba a ce komai ba kasan tana magana ne da masu taurin bashi, waɗanɗa take bi bashi kuma sun ƙi biyanta amma ba za ka san ko su waye amma dai mutum zai gane ta na magana ne kan masu bashi ko waɗanda take bi.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Shawara ga masu habaici a kafofin sada zumunta

Kowane abu a duniya yana da alfanu da kuma illolinsa. Kasancewar habaici na daya daga cikin zantuttukan hikima na Bahaushe wanda ya gada tun kaka da kakanni, kuma riƙe shi tamkar riƙe wani abu ne mai matuƙar muhimmanci daga abubuwan da aka gada, sai dai kuma a kula a kuma san yanda ya kamata a yi amfani da su musamman tun da ya shafi al'adar mal Bahaushe.

Ya kamata a ringa bin yadda tsarin da Bahaushe ya tsara na gargajiya. A kuma guji bin baƙin al'adu da ɗabi'un wajen gabatar da su.

Ina kira ga masu habaici musamman 'yan siyasa masu habaici a kafar sada zumunta domin kuwa yin haka ya bada tagomashi ga rashin tsaro a kasarmu Najeriya domin kuwa idan shugaba ko wani dan siyasa ya yi rubutun habaici a kafar sada zumunta, na daya dai bai fito fili ya fada ko waye ba.

Don haka ya budewa mabiyan kofar tunanin abubuwa dayawa. Idan mabiyan ƴan rigima ne, to daga nan za su fara mayar da martani ga mabiyan waɗanda suke tunanin shi ake wa habaici.

In su kuma mabiyan wance din su ma masu rigima ne, shi kenan rikici ya fara ke nan wanda idan ba ayi sa'a ba za ta iya kai ga rashi rayuwa ko kuma dukiya da sauransu.

Na biyu kuma mutuncinsu na iya zubewa musamman a gurin magoya bayan wanda aka ma habaici ko kuma wanda ake tunanin an yi wa habaici.

Ina ƙara kira ga iyayenmu mata musamman masu kishiyoyi ko abokan zama, mu rage ɗora habaici musamman a sitatus saboda ba mu san mai zai je ya dawo ba. Musamman ga yaranmu domin zai iya shafar tarbiyyarsu da kuma mutuncinsu.

Ina kuma kira ga samari da 'yan mata su guje yada zance musamman a kafar sada zumunta domin ba a san me zai je ya dawo ba.kuma zai iya zubar da mutuncinku da kuma ƙimarku musamman ga 'ya mace.

Zai rage mata daraja a idon mutane kuma za a ringa kallonta a matsayin marar tarbiyya.

Wannan layi ne