Daga bakonmu na mako: Kalubale ga marubuta labaran Hausa a kan yawaitar kagaggun labarai a shafukan sada zumunta
Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙuwarmu ta wannan makon Aishatu Shehu Maimota ta Sashen Hausa na Kwalejin Shari'a da Ilimin Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano.

Asalin hoton, Getty Images
Rubutaccen kagaggen labari na Hausa wani rubuti ne na adabin Hausa, shi kuwa adabin Hausa madubi ne da yake bayyana rayuwar Hausawa, wanda ya kunshi dukkanin hikimomi na sarrafa rayuwar wannan al'umma.
Haka kuma koyaushe adabin Hausawa yana kokarin tafiya da duk wani abu da al'ummar ta karu da shi sabo, daga wasu al'ummomin tare da hadawa da nata.
Abin lura dai a nan shi ne adabin al'umma yana bunkasa ne idan wannan al'umma tana cudanya da wasu al'ummomin tana karuwa da hikimomin sarrafa rayuwa na al'umma tana kara wa a kan nata.
Rubutaccen kagaggen labari rubutu ne da aka yi a shimfide ta sigar shafuka ko ya zo a tsari na zanguna, wanda ya kunshi labarin da ba lalle ya auku ba amma kuma akasari ana tsara shi a kan rayuwa ta zahiri, da nufin isar da wani saqo ga al'umma.
Za a kuma iya bayyana shi da wallafa da ake baje kolin hikimomi a zube, ba a tsari na waka ba, ba wasan kwaikwayo ba, ba kuma a siga ta alkaluman lissafi ba, sai dai yakan zo a zube, da zummar sadar da wata manufa da mawallafi ya kirkira.
Wannan takarda ta yi tsokaci ne kan samuwa da yawaitar wani nau'in adabi na kagaggun labarai ta yadda ake wata su a shafukan sada zumunta na intanet.
Haka kuma takardar hannuka mai sanda ce ga marubuta da masu sha'awar tsunduma harkar rubuta wadannan labarai, domin haska musu hanya ta gyara da inganta su, duba da yadda suka samu karbuwa a idon masu karanta su.

Shafukan sada zumunta
Shafin sada zumunta wanda da Turanci ake kira Social Media, fasahar sadarwa ce ta zamani da jama'a ke sada zumunci tsakaninsu daga sassan duniya daban-daban, ta hanyar amfani da cibiyar sadarwa ta zamani da aka fi kira da network, wanda yake aiki da intanet.
Jama'a daga sassan duniya suna samun damar sada zumunci ta hanyar tattaunawa wato, ta hanyar yin magana ko kiran bidiyo (Video Call) ko kuma tattaunawa ta hanyar musayar sako (chats).
An bayyana shafin sada zumunta da:
Dangane da tarihin samuwar shafukan sada zumunta na zamani kuwa za a iya cewa sun samu ne bayan yawaitar na'ura mai kwakwalwa da samun cibiyar sadarwa da kuma samun fasahar intanet.
Hanyar sadarwar da aka fara samu ta samu ne a shekarar 1997, wadda take bai wa masu amfani da ita damar samar da karamin shafi da aka fi kira da profile.
A shekarar 1999 ne kuma aka kirkiri damar samar da karamin shafi da ake kira blogging.
Bayan samuwar kananan shafukan sada zumunta sai kuma aka sami yawaitar shafukan sada zumunta musamman daga shekarar 2000.
Daga cikin ire-iren wadannan shafuka akwai: Yutub (Youtube) da Sinaf cat (Snap chat) da Fesbuk (Facebook) da Biba (Viver) da Tugo (2go) da Baduu (Badoo) da Waz'af (WhatsApp) da Wicat (We-chat) da Tuwita (Twitter) da Imo (Imo) da Instagiram (Instagram) da sauransu.
Bunkasar kagaggun labaran Hausa a shafukan sada zumunta
Kagaggun labaran Hausa na shafukan sada zumunta, wadanda da Turanci ake kira Online Hausa Novels, kagaggun labarai ne da ake rubutawa a shafukan sada zumunta na zamani.
Ana rubuta su yawanci a wayoyin hannu wadanda ake kira Android, tare da amfani da Cibiyar Sadarwa da ake kira Network, wadda take amfani da intanet.
Bayan an rubuta, marubutan na watsawa a kananan shafukansu ko su tura a zauruka na WhatsApp da Facebook da sauransu.
A wasu lokuta kuma masoyansu ke bude ire-iren wadannan zauruka su tura labaran.
Kamar yadda aka bayyana a sama, su dai wadannan labarai ba a littafi ake rubuta su ba, ana rubutawa ne a wayoyin hannu da ake kira Android.
Za a iya kiran wadannan labarai da "Adabi A Tafin Hannu", musamman idan aka yi duba da yadda waya take koyaushe a hannun jama'a yanzu.
Wadannan labarai an same su ne a karni na ashirin da daya.
Haka kuma marubuta wadannan shafuka suna bude kananan shafuka ne na kansu da ake kira blogs da wattpad da sauransu.
Dangane da tarihin samuwar kagaggun labaran shafukan sada zumunta na zamani, an samo bayanai daga bakin wasu marubutan wadannan shafuka da wasu masu karanta labaran, da cewa an fara rubuta su a shekarar 2013.
Tun daga wannan lokaci ake samun yawaitarsu.

Kawo yanzu, wadannan labarai kara bunkasa suke ta hanyar yawaita, tare da samun karuwar marubutan da makaranta.
Ana samun wadannan labarai ne ta hanyar intanet , wato bayan sun saka shi a kananan shafukansu da suka hada da blog da wattpad da wordpress da sauransu sai ya watsu ta Facebook ko a karanta kai tsaye ta intanet, wato ta Opera da Goggle da Chrome da sauransu.
Daga baya kuma wasu masoyansu sai su watsa a WhatsApp musamman a shafukan zaurukan, wato groups.
A wasu lokutan kuma su marubutan ne suke bude ire-iren wadannan kungiyoyi na whatsApp inda suke watsa wadannan labarai.
Akwai marubuta wadannan labarai da yawa, ga wasu daga cikinsu da sunayen kananan shafukansu da wasu labaran da suka rubuta;
i) Benaxir Omar, sunan shafinta [email protected] Labaranta sun haxa da: Ke Ce Gudalliya (2013) da Sirri Ne (2013) da Dangin Miji (2014) da Budurcina 'Yancina (2015) da Babu Ruwan Kwai da Aski (2016) da Ciwon Idanu (2016) da Abin Tsoro Kura a Rumbu (2017).
ii) Khaleesat Hydar, sunan shafinta https://m.facebook.com>permalink Labaranta sun hada da; Khaleesat (2015) da Inteesar (2015) da Ikraam (2016) da Dr. Khaleel (2016) da Capt. Ahmad Junaid (2017).
iii) Maryam Alkali wadda aka fi sani a shafin sada zumunta da Mamu, sunan shafinta, www.mrsjabo.wordpress.com, Labaranta sun hada da: Wa Zan Aura? (2014) da Surikar Zamani (2015) da Tafiya Mai Nisa (2015) da Mata Uku Gobara (2016) da Tabarya Mai Baki Biyu (2016) da Bakin Ganga (2017).
A tattaunawar da na yi da wasu marubutan shafukan sada zumunta, sun tabbatar da cewa, akwai kungiyoyi, kuma wadannan kungiyoyi suna dauke da marubuta masu yawa, misali kamar kungiyar Nagarta tana da akalla mambobi hamsin.
Haka kuma ire-iren wadannan kungiyoyi suna tattaunawa a tsakaninsu domin magance matsaloli da suka shafe su, kasancewar ba a raba ire-iren wadannan kungiyoyi da matsaloli.
Wadannan marubuta da labaransu suna taka rawa a duniyar adabi, domin a shekarun (2018) da (2020) su suka lashe gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata.

Kalubale ga marubuta labaran Hausa na shafukan sada zumunta
Hakika marubuta labaran Hausa na shafukan sada zumunta suna kokari wajen hasko matsaloli da suke addabar al'umma a wannan lokaci misali Gumin Halak na Batool Mamman da ya kalli matsalar fyade da yadda ake muzgunawa 'yan aiki.
Akwai kuma Kundin Kaddarata na Safiyya Abdullahi Musa Huguma da ya dubi zamantakewar rayuwa ta hanyar nuna irin sakayya da duk wanda aka zalunta yake samun riba a rayuwa bayan ya yi hakuri.

Asalin hoton, Aisha Shehu Maimota
Sai kuma Kainuwa na Ayusher Muhd da yake bayyana al'adun Hausawa da suk shafi sarauta.
Amma a bangare daya za a iya cewa ma fi yawan labaran da ake samar wa a kafafen sada zumunta na zamani suna karan-tsaye ga tarbiyya da aka san Bahaushe da ita.
Domin akan sami sakin baki wato, suna bayyana batsa da munanan dabi'u da suka samo wadanda ba na Hausa ba.
Haka zalika ba sa la'akari da yadda yara masu karancin shekaru ke shiga a dama da su shafukan sada zumunta, wanda hakan zai kawo nakasu ga tarbiyyarsu, kuma zai iya haifar da barna a tsakanin wannan al'umma.
Duba da haka wannan takarda ta yi wani tsinkaye wanda za a iya cewa "gyara kayanka' ne, wanda Bahaushe yake cewa '...ba zai zamo sauke mu raba ba.'
Ina gani da yadda wadannan labarai suke da tasiri kwarai a wajen matasa da sauran masu karatu, a ce marubuta labaran suna kokarin inganta wadannan labarai ta hanyar bayyana al'adun Hausawa na gargajiya a ciki, kama daga abinci da suturu da yanayin bukuwa da zamantakewa, ai kuwa da 'kwalliya ta biya kudin sabulu.'
Domin matasa musamman mata da suke kokarin kwaikwayar rayuwa ta cikin wadannan labarai za su inganta zamantakewar gidan aurensu, haka zalika su ma maza.
Sannan kuma hakan zai taimaka wajen magance matsalar mutuwar al'adun Hausawa na gargajiya.
A bangare daya kuma, domin a samu bunkasa da yaduwar adabin Hausa, zai yi kyau a ce ko da marubutan za su dauki al'adun wasu al'umomi makwabta na kusa da na nesa da Hausawa, sai su yi kokari su dauki nagartattu da za su kawo wa Hausawa cigaba ba koma baya ba.

Ƙarin labarai masu alaƙa












