Hikayata 2020: Gwarzuwar gasar ta biyu ta samu tallafin karatu

Surayya Zakari Yahaya wadde ta zo ta biyu a Gasar Hikayata ta gajerun ƙagaggun labarai ta mata zalla ta BBC ta shekarar 2020 ta samu tallafin ci gaba da karatun gaba da sakandare albarkacin nasararta.
Ƴar majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Dukku da Nafada daga Jihar Gombe, Hajiya Aishatu Jibril Dukku ce ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatun Surayya ranar Juma'a da dare yayin bikin karrama gwarazan.
Duk da cewa ba ita ta zo ta ɗaya ba, amma Honorabul Dukku ta yi hakan ne bayan da ta fahimci cewa Surayya marainiya ce wadde ta gaza ci gaba da karatu bayan kammala sakandare duk kuwa da cewa ta yi nasara a jarrabawar WAEC.
Shi ma tsohon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Barista Abdullahi Mukhtar ya sanar da cewa zai tallafa wa Surayyan a yayin ci gaba da karatun nata.
Sanar da wannan daddaɗan labari ke da wuya sai Surayya ta fashe da kuka, inda ta yi zumbur ta nufi teburin da Hajiya Aishatu take don nuna godiyarta, inda rungume juna cikin farin ciki.
Honorabul Dukku, wadde tsohuwar ƙaramar ministar ilimi ce a lokacin tsohon Shugaba Umaru Musa Ƴar'adua ta ce ta ga dacewar bai wa Surayya Zakari wannan tallafin ne saboda "ba ni da wani buri irin na ga ana tallafa wa karatun ƴaƴa mata.
"Don duk wanda ya ilimantar da ƴa mace to ya yi wani babban al'mari na ceton al'umma," in ji ta.
Da take tsokaci kan wannan babban al'amari, Hajiya Bilkisu Funtua, ɗaya daga cikin alƙalan gasar, cewa ta yi BBC Hausa ta zama zakaran gwajin dafi a fannoni da dama a arewacin Najeriya.
"Babu abin da za mu ce wa BBC sai Allah Ya sa ta fi haka. Ta taimaki rayuwar mata ta fannoni daban-daban, ga kuma alkairan da ke samuwa irin waɗannan a dalilinta," a cewarta.
Wace ce Surayya Zakari?

Surayya Zakari ta fito daga Jihar Kano sannan ta yi nasara ne da labarinta mai taken "Numfashin Siyasata", wanda Aishatu Dukku ta ce ta ji labarin tamkar ya taɓo wani ɓangare na rayuwarta ne a matsayinta na mace ƴar siyasa.
An haifi Surayya Zakari Yahaya ranar 1 ga Janairun 1995 a unguwar Ƙoƙi da ke ƙwaryar birnin Kano.
Ta yi makarantar firamare ta Festival daga shekarar 2001 zuwa 2007, sannan ta je ƙaramar sakandare ta Arabiyya a Ƙoƙi daga 2007 zuwa 2010 inda ta ƙarasa a Umma Zaria Secondary School daga 2010 zuwa 2013.
Mahaifinta ya rasu tana da shekara 20. Da ma can mahaifiyarta sun rabu da mahaifin nata kafin rasuwarsa, inda take aure a Jigawa.
A halin yanzu Surayya na rayuwa ne tare da dangin babanta a unguwar Ƙoƙi.











