Bidiyo: Bahaushiyar da ke sana'ar tuƙa Keke Napep a Kaduna
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wata matashiyar Bahaushiya ta rungumi sana'ar tuka babur mai kafa uku domin neman abin kai wa bakin salati. Asiya, wadda ta shaida wa BBC hakan, ta yi kira ga mata matasa su kawar da girman kai sannan su rungumi sana'o'i domin bunkasa rayuwarsu.
A cewarta, takan fito tun da sanyin safiya domin gudanar da sana'arta kuma tana samun abubuwan biyan bukata.
Ta kara da cewa ba za ta daina wannan sana'a ba ko da ta yi aure.