Matar Sarki ta zama mace mafi girman muƙami a 'yan sandan Najeriya
Aisha Abubakar, mataimakiyar babban sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce tana matukar tsoron dan sanda lokacin tana yarinya.
A tattaunawarta da BBC, mace ta biyu daga arewa mafi girman matsayi a rundunar 'yan sandan kasar, ta kara da cewa iyalinta sun karfafa mata gwiwar shiga aikin na dan sanda.
A cewarta, babu abin da ke sanya ta dariya kamar 'ya'yanta.