Hikayata 2020: Maryam Umar ce gwarzuwar gasar

Hikayata 2020

Labarin 'Rai da Cuta' na Maryam Umar ya yi nasarar lashe gasar Hikayata ta bana, bayan haye matakai daban-daban na tantancewa.

Haka kuma, Maryam Umar ta samu kyautar kudi dala dubu biyu wato kusan Naira miliyan daya ke nan.

Surayya Zakari Yahaya ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna 'Numfashin Siyasata' kuma ta samu kyautar kudi dala dubu daya, sannan Rufaida Umar Ibrahim ta zo ta uku da labarinta mai suna 'Farar Kafa' da kyautar kudi dala dari biyar.

An karrama marubutan ne a wani bikin da BBC Hausa ta shirya a Abuja da yammacin Juma'a.

Wannan ne karo na biyar da Sashen Hausa na BBC ke karrama gwarazan gasar ta rubutun gajerun labarai ta mata zalla, wato Hikayata.

Hikayata 2020
Bayanan hoto, Hikayata 2020

Labarin 'Rai da Cuta' na Maryam Umar

Labarin Rai da Cuta ya duba yadda mutane ba su yarda da cutar korona ba, cutar da ta zama annoba a duniya.

Tauraruwar labarin mace ce mai juna biyu da mijinta ya kamu da cutar korona amma ya ƙi zuwa asibiti har ita ma ta dauki cutar.

Mijin nata ya kulle ta a ɗaki har ta kusa rasa ranta sannan jaririn da ke cikinta ya mutu.

Wannan layi ne

Labarin 'Numfashin Siyasata' na Surayya Zakari Yahaya

Numfashin Siyasa labari ne kan wata matashiya da ta yi ƙoƙarin ceto al'ummar ƙauyensu ta hanyar shiga siyasa.

Sai dai al'ummarta ba ta shirya morar shugabanci daga hannun mace ba don haka sai aka juya mata baya.

A gwagwarmaryar siyasarta, tauraruwar labarin ta rasa iyayenta sannan ta fuskanci tsangwama da wulaƙanci daga mutanen ƙauyenta.

Wannan layi ne

Labarin 'Farar Ƙafa' na Rufaida Umar Ibrahim

Wannan labari ne kan wata wadda yarda da camfi ya jefa ta a cikin mawuyacin hali.

Bayan aurenta, mijinta ya yi ta gamuwa da jarrabawa iri-iri kuma ya camfa cewa tana da farar ƙafa shi ya sa waɗannan iftila'i ke hawa kansa.

Rahama ta sha tsangwama dalilin haka kuma aka yi mata laƙabi da mai farar ƙafa.

Wannan layi ne
Bayanan bidiyo, Hikayata: Bidiyo bikin karrama gwarazan gasar 2020

Me ya sa waɗannan labaran suka fita daban?

Alƙalan gasar na bana dai su ne ita Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtua wadda aka fi sani da Anty Bilki, marubuciyar littafan Hausa da Dokta Hauwa Bugaje, malama a tsangaya harsunan Afrika a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da Sada Malumfashi, dan jarida mai zaman kansa, marubuci kuma manazarcin littafan Hausa.

Jagorar alkalan Bilkisu Salisu Ahmed Funtua ta ce "ingancin rubutun wadannan labarai ya fita daban. Marubutan sun kawo wani canji da zan iya cewa ba a taɓa gani ba a wannan gasa."

"Da za a bar ni, ko wacce daga cikin marubutan nan gwarzuwa ce saboda dukansu sun taka rawar gani," a cewar Bilkisu Salisu Ahmed.

Dokta Hauwa Bugaje ta ce "Jigogin da waɗannan marubuta suka fitar a labaransu ba irin waɗanda muka saba gani ba ne. A wannan karon, an samu ci gaba a salon rubutun da yadda aka aika sakonnin."

Shi ma Sada Malumfashi ya ce "Waɗannan labarai uku gaba ɗaya babu na yarwa. Marubutan ssun yi ƙokari tun daga fannin jigo zuwa salon rubutu."

Alƙalan sun ce labaran na bana sun yi magana kan abubuwan da suke damun al'umma kuma sun inganta labaran da salon rubutu mai ƙayatarwa.

Rufaida Umar Ibrahim, Surayya Zakari Yahaya da Maryam Umar
Bayanan hoto, Rufaida Umar Ibrahim da Surayya Zakari Yahaya da Maryam Umar su ne matan da labaransu suka yi zarra a gasar ta bana