Hikayata 2020: Labarai uku da suka cancanci lashe gasar

Alkalan gasar Hikayata ta 2020

Alƙalan gasar ta bana dai sun gama zaman tantance labarai guda 25 don fitar da gwaraza uku da ake ganin labaransu sun cancanci lashe gasar ta ƙagaggun labarai wato Hikayata.

Ko wane labarin ne zai kai ga ci?

A yanzu dai, alƙalan sun zaɓi labarin 'Numfashin Siayasa' da 'Farar Ƙafa' da 'Rai da Cuta' a matsayin labarai uku da suka cancanci lashe gasar.

Sun zaɓo waɗannan labaran ne dai daga labarai 25 da suka bi matakai daban-daban na tankaɗe da rairaya.

Jagorarar alƙalan, Hajiya Bilkisu Salisu Ahmad Funtua wadda aka fi sani da Anti Bilki, tsohuwar marubuciya ta ce "labaran na bana duk babu na yarwa. Da za a bar ni da na ce duka a ba su kyauta saboda babu marubuciyar da ba ta yi ƙoƙari ba."

"Saƙonnin da ke cikin waɗannan labaran da salon yadda suka rubuta su ya nuna cewa wannan gasa ta zaburar da mata sosai wajen isar da saƙonninsu ta hanyar rubutu", a cewar Anti Bilki.

Wannan layi ne

Numfashin Siyasa

Numfashin Siyasa labari ne kan wata matashiya da ta yi ƙoƙarin ceto al'umar ƙauyensu ta hanyar shiga siyasa.

Sai dai al'umarta ba ta shirya morar shugabanci daga hannun mace ba don haka sai ta juya mata baya.

A gwagwarmaryar siyasarta, tauraruwar labarin ta rasa iyayenta sannan ta fuskanci tsangwama da wulaƙanci daga mutanen ƙauyenta.

Wannan layi ne

Rai da Cuta

Labarin Rai da Cuta ya duba yadda mutane ba su yarda da cutar korona ba, cutar da ta zama annoba a duniya.

Tauraruwar labarin mace ce mai juna biyu da mijinta ya kamu da cutar korona amma ya ƙi kai ta asibiti har ita ma ta kwashi cutar.

Mijin nata ya kulle ta a ɗaki har ta kusa rasa ranta sannan jaririn da ke cikinta ya mutu.

Wannan layi ne

Farar Ƙafa

Wannan labari ne kan wata wadda illar yarda da camfi ya jefa ta a cikin mawuyacin hali.

Bayan aurenta mijinta yai ta gamuwa da jarrabawa iri-iri kuma ya camfa cewa tana da farar ƙafa shi ya sa waɗannan iftila'i ke hawa kansa.

Rahama ta sha tsangwama dalilin haka kuma aka yi mata laƙabi da mai farar ƙafa.

Wannan layi ne

Labarai sama da 400 ne aka shigar gasar ta Hikayata ta bana, kuma kafin a kawo wannan mataki sai dai aka tankaɗe labaran aka fitar da 25.

Wajen tantancewar dai an yi amfani da ƙa'idojin shiga gasar, musamman game da adadin kalmomi, da bin ƙa'idar rubutu, da amfani da daidatacciyar Hausa, da kauce wa amfani da kalaman da ba su dace ba da zarge-zarge, da ma tabbatar da cewa labarin ƙagagge ne.

Baya ga labarai ukun da alkalan suka fitar, sun kuma ayyana wasu 12 a matsayin waɗanda suka cancanci yabo.

Dukkan labaran 15 dai za a karanta su nan gaba a rediyo a kuma saka su a shafukanmu na intanet da na sada zumunta.

Gwarazan gasar Hikayata 2019
Bayanan hoto, Jamila Babayo ta zo ta uku, Safiyya Ahmad ta zo ta ɗaya yayin da Jmaila Abdullahi Rijiyar Lemo ta zo ta biyu a gasar ta 2019

Haka kuma, za a sanar da gwarzuwar Hikayata ta shekarar 2020 a bikin karrama gwarazan gasar da za a yi a watan Disamba a Abuja.

Gwarzuwar za ta samu kyatutar kudɗ dalar Amurka 2,000 da lambar yabo; wacce ta zo ta biyu kuma za ta karɓi kyautar kuɗi dala 1,000 da lambar yabo; sannan wacce ta hau matsayi na uku za ta karɓi kyautar kuɗi dala 500 da lambar yabo.

Wannan layi ne