Hikayata 2020: Alƙalai sun fara aikin fitar da gwaraza

Alkalan gasar Hikayata

Alƙalan gasar rubutun ƙagaggun gajerun labarai ta bana wato Hikayata sun fara aikin tantance labaran da aka shigar inda za su fitar da labari uku da suka yi zarra a bana.

Daga nan ne kuma alƙalan za su amince da labarin da ya cancanci zuwa na ɗaya da na biyu da na uku.

Gasar ta bana ta samu masu shiga gasar kusan ɗari biyar da suka turo da labaransu.

"Wannan na nuna cewa gasar Hikayata na ƙara samun karɓuwa kuma kwarjinita na ƙaruwa idan aka kwatanta da shekarun baya", a cewar Aliyu Abdullahi Tanko, shugaban sashen Hausa na BBC.

Wannan mataki shi ne na ƙarshe a matakai daban-daban da labaran ke bi don zaɓo waɗanda suka yi zarra.

Daga farko an rairaiye labaran daga kusan 500 zuwa 30. Sannan ƙwararru suka sake rairaye guda 30 ɗin zuwa 25 da alƙalan suke dubawa a matakin na ƙarshe.

Dukka waɗannan matakai na aiki ne da ƙa'idojin shiga gasar da aka zayyano tun daga farkon buɗe ta wanda suka haɗa da adadin kalmomi, da bin ƙa'idojin rubutun Hausa da tabbatar da cewa labarin ƙagagge ne da dai sauran su.

Labarai 25 da alƙalan za su tantance:

  • Aikin Ƴa Mace
  • Baƙin Haure
  • Rayuwarmu
  • Ana Zaton Wuta A Makera
  • Dangin Babana
  • Nadama
  • Ƙaddara Ta Riga Fata
  • Aure Yaƙin Mata
  • Ciwon Ƴa Mace
  • Wata Duniyar
  • Aikin Kishiya
  • Rai da Cuta
  • Haifi Ka Yasar
  • Labarina
  • Tsalle Ɗaya
  • Gidan Aurena
  • Mace A Kaki
  • Wani Hanin
  • Wake Ɗaya Ke Ɓata Gari
  • Bayan Wuya
  • Labarin Falmata
  • Ƙuncin Rayuwa
  • Farar Ƙafa
  • Kishi Bayan Rai
  • Numfashin Siyasa
Jamila Babayo da Safiyya Ahmad da Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo
Bayanan hoto, Safiyya Ahmad ce ta zama gwarzuwar gasar a 2019 yayin da Jamila Abdullahi ta zo ta biyu sannan Jamila Babayo ta zo ta uku

Baya ga labarai 3 da alƙalan da za su zaɓa a matsayin wanda suka yi zarra, za kuma su fitar da labarai 12 da suke ganin sun cancanci yabo duk dai daga cikin waɗannan labarai 25.

A farkon watan Disambar wannan shekarar ne ake sa ran sanar da gwarzuwar gasar ta Hikayata a bikin karramawa da BBC za ta shirya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Duk wacce labarinta ya zo na ɗaya za ta samu kyatutar kuɗi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo; wacce ta zo ta biyu za ta wuce da kyautar kuɗi dala 1,000 da lambar yabo; yayin da mai matsayi na uku za ta karɓi kyautar kuɗi dala 500 da lambar yabo.

Wannan ne karo na biyar na gasar Hikayata kuma a bara Safiyya Ahmad ce ta yi nasarar zama gwarzuwar gasar da labarinta mai suna Maraici.

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta zo ta biyu da labarinta mai suna Ba A Yi Komai Ba yayin da Jamila Babayo ta zo ta uku da labarin A Juri Zuwa Rafi.

Alkalan gasar Hikayata
Bayanan hoto, Dakta Hauwa Bugaje da Bilkisu Ahmad Funtua (Anty Bilki) da Sada Malumfashi su ne alkalan gasar ta bana