Gasar Hikayata: Ana daf da zaɓo labarai uku da suka yi zarra
Za a shiga wani muhimmin mataki a Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata Zalla wato Hikayata wadda BBC Hausa ke shiryawa a ranar Talata, inda alkalai za su fitar da labarai uku da suka yi zarra.
Za a zaɓo wadannan labarai ne daga guda 25 da alƙalan suka yi nazari a kansu, bayan sun bi matakan tantancewa daban-daban.
Idan ba a manta ba, a ranar 24 ga watan Agusta ne aka rufe karɓar labarai a gasar ta bana.
Fauziyya Kabir Tukur ta tambayi shugaban sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ko mene ne muhimmancin wannan mataki da za a shiga a yau?


Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata
Yardarki na da muhimmanci a garemu. Wannan na nufin cewa BBC ta daura damarar kare bayananki. Yana da muhimmanci ki karanta wannan sanarwar don sanin yadda muke amfani da bayananki da kuma dalilin da ya sa muke amfani da su.
Wannan sanarwa ta kunshi yadda muke karba da amfani da bayanai a kanki a yayin da kuma bayan mu'amalarki da mu, kamar yadda dokar tsare sirri ta tanada. Za ki iya samun karin bayani a nan.
Me muke karba kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?
Idan shekarunki sun kai 18 ko sun haura, muna maraba da shigarki gasar. Don shiga gasar, BBC za ta karba kuma ta yi aiki da bayanan da suka shafe ki wadanda kika aiko mana, ciki har da sunanki da lambar wayarki da adireshinki da adireshin email dinky da duk wani bayani da ya dangance ki da kika aiko mana dangane da shigarki gasar.
Za a yi amfani da bayanan da kika aiko mana a kanki da manufar shiga gasar. BBC ce 'mai iko' kan wannan bayani. Hakan na nufin cewa BBC za ta yanke shawarar abin da za ta yi da bayananki, da hanyoyin da za a yi amfani da su. Idan bukatunki ba su kere na BBC ba, BBC za ta yi aiki da bayananki dangane da wannan gasa bisa bukatunta (wato BBC) da ba su kauce wa ka'ida ba na nishadantar da masu bibiyarta da kuma ta shirya gasanni bisa gaskiya da sanin ya kamata.
Ajiye bayananki
Idan ke ce kika yi nasara a gasar, ko kuma kika zo ta biyu ko ta uku, ko kuma kina daya daga cikin mutane goma sha biyu da labaransu suka cancanci yabo za a wallafa labarinki sannan BBC za ta ajiye bayananki tsawon shekaru biyu.
Za a goge labaran da ba su yi nasara ba, bayan an sanar da wadanda suka yi nasara ranar 11 ga watan Disamba, 2020.
BBC za ta rarraba bayananki ga alkalan gasar wadanda kuma ba ma'aikatan BBC ba ne.
Ma'aikatan BBC da ke London da Najeriya za su ajiye bayananki a kamfutocin BBC tare da daukar matakan tsaron da suka dace.
Muna iya nemanki don tabbatar da shekarunki ko don mu tattauna kan labarin da kika shigar gasar.
Hakkinki da Karin bayani
Idan kina da wata tambaya kan yadda BBc ke tafi da bayanaki, ko kuma kina so ki san hakkokinki, ki ziyarci wannan shafin na BBC. Za kuma ki samu Karin bayani kan yadda BBC ke aiki da bayananki da yadda za ki iya aika sako ga Jami'in da ke Kula da Kare Bayanai na BBC.
Idan kika nuna wata damuwa dangane da yadda BBC ke aiki da bayananki kuma ba ki gamsu da amsar da BBC ta ba ki ba, kina da ikon shigar da korafi ga wata hukuma mai sa ido. A Burtaniya, hukumar da ke sa ido ita ce Ofishin Kwamishinan Bayanai (ICO).












