Hikayata ta 2020: Za a rufe gasar ƙagaggun labarai ta mata zalla

Gasar Hikayata 2020

Za a rufe shiga gasar Hikayata ta mata zalla da karfe sha biyu na daren Litinin, 24 ga watan Agustan 2020.

Hakan na nufin daga wannan lokacin ba za a sake karbar labarai don shiga gasar ba, kuma ko an turo da labari ba zai samu shiga gasar ba.

Shugaban sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce yanzu za a shiga mataki na gaba na gasar.

"Akwai kwararru da za su yi aikin tantance labaran da aka shigar gasar, su yi tankade da rairaya har a samu wadanda suka yi na daya da na biyu da na uku", a cewarsa.

A wannan matakin ne za a cire labarai 25 daga cikin duka labaran da aka aiko, sai a tura wa alkalan gasar wadanda za su fitar da ukun da zuka yi zarra da guda goma sha biyu da suke ganin sun cancanci yabo.

Aliyu Tanko ya ce bisa dukkan alamu gasar Hikayata na kara samun karbuwa a wajen mata masu amfani da harshen Hausa.

Ya ce: "Mun samu karin mata masu aiko da labaransu don shiga gasar idan aka kwatanta da bara da bara waccan. Wannan na nuna cewa sun yi na'am da ita kuma sun karbe ta hannu bibbiyu."

Sannan ya ce an samu mata masu shiga gasar daga sauran kasashen da ke makwabtaka da Najeriya akasin yadda ake gani a baya inda mafi yawan masu shiga gasar 'yan Najeriya ne.

Kawo yanzu dai an samu gwarazan gasar Hikayata 12 tun daga fara gasar a shekarar 2016- inda duk shekara a ke fidda mata uku a matsayin wadanda suka yi zarra.

Ana sa ran sanar da gwarazen gasar Hikayata ta bana a cikin watan Disambar wannan shekara a wani taron karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya, inda za a ba su kyautar kudi da lambar yabo.

A shekarar 2019, Safiyya Ahmad ce ta zo ta daya da labarinta mai suna 'Maraici', sai Jamila Abdullahi Rijiyar-Lemo ta zo ta biyu da labarinta mai taken 'Ba A Yi Komai Ba' sannan Jamila Babayo ta zo ta uku da labarinta mai suna 'A Juri Zuwa Rafi'.