Hikayata 2020: Labarin 'Rai da Cuta' da ya zo na ɗaya

Ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron labarin:

Bayanan sautiKaratun Labarin 'Rai da Cuta' wanda ya zo na daya a Gasar Hikayata ta 2020

Wannan labarin hakkin mallakar BBC ne. Ba a yarda wani ko wata su yi amfani da shi ta ko wane salo ba, ko da yaɗa shi ne ta shafukan sada zumunta. Idan aka yi hakan kuma, to BBC za ta ɗauki mataki har da na shari'a.

Na sake rufe idanuwana a karo na biyu sanadiyar ƙarfin hasken da ya gagari ganina.

Tun a duniya na san cewar Bil'adama ko Jinnu ba su iya gani ko jin Mala'ika, don haka na ƙara jan dogon numfashi ina jin yadda shaƙar isakar kabarin ya gagare ni, na ji tsoron kada hakan yayi sandiyar kasawata a karɓa tambayar ƙabari.

"Ya jikinki?"

Ya faɗa a cikin harshen da na tabbata ba Larabci ba ne, kazalika ba Hausa ba ne.

Ɗaya daga cikinsu ya iso ta gefena tare dafa kaina yana sake maimaita maganar da na fahimci tambaya ce, ba shakka sun ƙara dulmuyar da ni da rashin sanin al'amarin da ke faruwa.

Da ma akwai bambancin jinsi a Mala'iku? Na yi wa kaina tambayar ina kallon ta yadda a suturarsu na kasa bambanta su, amma a murya na fahimci mace ce da namiji.

Da alama neman ƙahon kare zai yi wahala.

Dukkansu suna sanye da fararen kaya ne da suka zarce jikinsu, yayin da suka rufe kansu da hular da ta ƙi ba ni damar ganin halittarsu.

Na buɗe baki da ƙyar na ce musu. "Ubangijina... shi ne... Allah…" Na faɗa yayin da numfashina yake katse kowace gaɓa daga jumlar.

Dariya na ji ɗayar ta yi sannan ta saki hannuna da ta riƙe, ta ja hannun ɗan uwanta suka miƙe a doguwar hanyar da suka ɓace wa ganina.

Ban sani ba ko hakan na nufin na tsira kenan. Na yi shiru na ɗan wasu daƙiƙu ina sassaita tunanina.

Na fara hasko fuskar mijina da yadda muka kasance a ɗazu.

Na fara tunano rikici da tashin hankalin da ya fara afkuwa a tsakaninmu tun bayan dawowarsa daga doguwar tafiyar da yakan shafe watanni bai waiwayo ni ba, kodayake, rikicin duniya da mai rai ake yi.

Wannan layi ne

Duk lokacin da duhun dare ya sallama wa gidajenmu, nutsuwar zuciya takan yi bankwana da ruhunanmu, mukan shiga jimamin da me gobe za ta fi yau, da yake abinda ya damu mutum da shi yake mafarki.

Na gincira a kan ƙofar kwanon da nake ji tamkar ta fi ni gata a doron ƙasa. Hawayen da na jima ina nema suka kwaranyo izuwa ga leɓena da ya bushe.

Na sanya hannayena na dafe tsohon cikina da yake juyi tare da jaddada mini rashin nutsuwarsa.

"Ka cutar da ni ka kuma cutar da abinda yake cikina."

Na furta kalaman ba tare da tunanin zai iya jiyo ni ba. Ga mamakina sai na jiyo shi yana buga ƙofar da saura ƙiris ya rage ta rasa garkuwarta.

"Azima, ki buɗe ƙofar nan, wallahi idan raina ya ɓaci na fito sai na lahira ya fi ki jin daɗi."

Na ɗan ja da baya sanadiyar sarar da kaina ya fara yi. Ina jin sa yana ci gaba da karanto mini irin sakamakon da zan fuskanta muddin ban biya wa ransa buƙata ba.

Tun bayan dawowarsa daga ci-ranin da yake zuwa a kudancin ƙasar nan na fahimci zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin kayar da shi.

Hankalina ya tashi, na fara zarginsa da kwaso cutar numfashin da ta zama ruwan dare game duniya musamman a yankin da ya fito Na ƙoƙarta tunkararsa da batun ta hanyar cewa.

"Isa, bayan zazzaɓin nan har da mura na damunka, kuma kullum a radiyo kana jin gargaɗin da ake yi mana, me zai hana ka je asibiti a duba ka?"

Ya miƙe yana ƙoƙarin fita daga ɗakin ya ce.

"Wane dare ne jemage bai gani ba. Ba abun da zai kai ni asibiti, salon su ƙara da ni a cikin ƙirgensu da suke yi a kullum. Ke ni fa bari kiji…"

Ya dawo ya zauna a kusa da ni bayan ya yi atishawa sau huɗu a jere.

"Ko da a ce koronar nan da gaske ce ba zan yarda in bi su asibitinsu ba, na ji labarin ko Ali da suka tafi da shi an ce ko abinci ba sa iya ba mutum."

"Ali dai da kuka tafi tare da shi?"

Ba tare da ya karanto tashin hankalin da ya bayyana a fuskata ba ya ce.

"Eh, sun kama shi."

Wannan layi ne

Sati ɗaya ya shuɗe yayin da duk wasu alamomin kamuwa da cutar numfashi suka bayyana a jikin mijina.

Hakan ya tilasta mini yin daidai ba abinda rai ke so ba.

Duk da cewar mijina ne amma ai an ce duk girman Sarki idan ba lafiya ya zama bawa, don haka na yi ɗamarar ɗaura wa kura aniyarta, kazalika gwara a kashe wuta tun tana ƙanƙanuwarta.

Na rufe shi a ɗaki tare da tabbatar masa da cewar zan je a kira mini hukumar lafiya kamar yadda aka sanar mana a rediyo.

"A bakin aurenki muddin kika taka ƙafarki a waje, ke ko wani kika yi magana da shi, na sake ki saki uku."

Sharaɗin da ya shar'anta mini kenan, wanda hakan ya toge duk wani taimako da nake ƙoƙarin yi domin ceto rayuwarsa.

"Azima duk ranar da kika kashe aurenki ki nemi gidan uba, amma ba ni ba."

Na tuna furucin mahaifina tun shekarun baya da na yi ƙoƙarin datse igiyoyin aurena a kan rashin zaman lafiyar da muka fuskanta a farkon aurenmu, kashe aurena daidai yake da zaɓin mutu da rayuwa ne.

Kazalika dole na yi taka-tsan-tsan domin tseratar da rayuwata da abinda yake cikina, da ma rayuwar al'umma baki daya.

Ta tagar ɗakin nake ciyar da shayar da shi. A cikin kwanaki biyar da muka kwashe a kaɗaice, tuni garkuwar jikina ta gagari ɗaukar nauyin cutar da na harbu da ita.

Sai dai da alama za ta fi yi wa rayuwata giɓi fiye da wanda ya harba mini. Yadda maƙoshina yake bushewa, ba na bambance ƙanshi ko akasin hakan.

"Isa dan Allah... ka bar ni in fita..."

Da ƙyar nake ɗaga muryata ta yadda zai jiyo ni, sai da na maimaita har sau uku gabanin ya leƙo ta tagar ɗakin yana cewa.

"Ba inda za ki fita. Yanzu ke ce annobar ba ni ba."

"Cikina..."

Na furta kalaman tare da riƙe cikina da ke matuƙar juya mini, duk lokacin da na yi atishawa nakan ji yadda abin da ke cikina yake nufatar hanyar da za ta kawo shi a duniya. Na rarrafa izuwa ƙofar na saka mukulli na buɗe masa tare da cewa,

"Ka rufe bakinka da hanci... Ka kai ni asibiti, haihuwa zan yi."

Duk da ya fahimci irin azabar da nake fuskanta amma hakan bai hana shi sharara mini mari har biyu ba. Tamkar kayan wanki haka ya watsar da ni a tsakiyar ɗakin tare da jawo ƙofa ya rufe yana mai cewa.

"Ki ɗanɗana kwatankwacin abinda na ji, ga ki 'yar yaƙin Yahudawa ko? Rufe ni a ɗaki tamkar fitsarin faƙo ne a wurinki."

Ina jin sa yana ƙoƙarin saka ɗan mukulli a ƙofar, can kuma sai na ji yana cewa.

"Su waye a nan? Dan me za ku shigo mini gida kuna ƙoƙarin tsallaka mini katanga..."

Ban ƙara jin maganarsa ba sai ƙarar bugu da na fara jiyowa da kuma ihunsa. Na rufe bakina daga ihun da nake ƙoƙarin kurmawa bayan sun turo ƙofar ɗakin suna leƙawa.

Su biyar ne a tsaye hannayensu riƙe da bindigogi.

Ba su gan ni ba sanadiyar duhun ɗakin, yayin da ni nake iya hango su a cikin hasken ƙwan fitilar da take falon.

Ban ji me suke cewa ba, suka fita bayan sun gyara rawaninsu. Na hango su suna bi ta katangar Alhaji Mamman maƙwabcinmu.

Na rarrafo izuwa ga Isa da ke kwance ina ƙoƙarin tashinsa.

"Wayyo Allah na shiga Uku!"

Na furta lokacin da na ga hatta ƙasusuwan fuskar Isa sun haɗe da juna, wanda hakan ya tabbatar mini ba ya numfashi.

Numfashina ya fara ɗaukewa yayin da abinda ke cikina yake buƙatar nishina. Na gagara jure azabar da nake ji, na cire ɗan kunnena ina fatar na iya huda cikina ko abinda ke cikina zai fito in sami salama.

Iyakar abinda na tuna kuma sai yanzu da na buɗe ido na ganni a lahira. Na sake rufe idanuna ina jiran sakamakon hisabina.

Wannan layi ne

"Yau satinki daya anan, jikinki bai yi kyau ba sam! Amma idan kika kwanatar da hankalinki zaki samu lafiya, sannan kuma jaririnki bai zo da rai ba sai muka hannunta shi ga yan uwanki."

"Ban mutu ba kenan?" Na furta da sauri wada hakan ya jazamin daukewar numfashi na dakiku.

"Eh, ba ki mutu ba, kawai an killace ki a nan ne har ki samu lafiya, sai dai kuma kin haɗu da matsalar yoyon fitsari sakamakon doguwar naƙuda, amma kada ki tashi hankalinki, 'yan uwanki suna zuwa kullum sai dai ba za su iya ganinki ba.

"Sun sanar da mu labarin rasuwar mijinki. Ance barayin da suka dauke makwabcinku ne suka kashe shi."

Na fara tarjamar kalamanta tare da tunanin ta ya hankalina zai kwanta bayan jerin bala'ukan da ta lissafa min?

Na koma na kwanta, ina jin yadda numfashi na ya zame min ciwo.

Anya ina farin cikin dawowata a duniyar da matattu suke rayuwa a cikinta?

"Corono gaskiya ce."

Na fada ina jin nauyin halshe na. Na rufe idanuna ina fatar samum salama.

Maryam Umar ce ta rubuta wannan labarin kuma ta shigar da shi gasar rubutun gajerun labarai ta BBC, Hikayata.