Daga baƙonmu na mako: Yadda marubutan litattafan soyayya na intanet ke ciniki
Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙuwarmu ta wannan makon Aishatu Shehu Maimota ta Kwalejin Shari'a da Ilimin Addini ta Malam Aminu da ke Kano.

Asalin hoton, Aisha Maimota
Adabi shi ne madubin rayuwa wanda ya ƙunshi dukkanin hikimomi na sarrafa rayuwar al'umma. Adabin Hausa madubi ne da yake haska rayuwar al'ummar Hausawa, wanda ya ƙunshi tunaninsu da hikimominsu.
Haka kuma ko yaushe adabin Hausawa yana ƙoƙarin tafiya da duk wani abu da al'ummar ta ƙaru da shi sabo, daga wasu al'ummomin tare da haɗawa da nata.
Rubutaccen ƙagaggen labari na Hausa wani rukuni ne na adabin Hausa. Masana sun bayyana adabin Hausa ta hanyoyi da dama. A ganin malamai da dama adabi kalma ce da aka aro daga Larabci, wato 'adab' wadda take nufin walima ko liyafa.
A Hausa ana kallonta da hanya da take haska hikimomin da Allah Ya yi wa al'ummar Hausawa, a furuci ko a rubuce.
Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen kallon yadda alaƙar rubuta ƙagaggun labaran Hausa ta karkata zuwa shafukan sada zumunta na Intanet, tare da hasko irin gudummawar da waɗannan labarai suke bayar wa, wajen wayar da kan al'umma.
Sannan maƙalar ta bayyana rubutaccen ƙagaggen labari da duk wani rubutu da aka yi a shimfiɗe ta sigar shafuka ko ya zo a tsari na zanguna, wanda ya ƙunshi labarin da ba lalle ya auku ba amma kuma akasari ana tsara shi a kan rayuwa ta zahiri, da nufin isar da wani saƙo ga al'umma.
Haka zalika za a iya bayyana rubutaccen ƙagaggen labari na Hausa a matsayin wallafa da ake baza kolin hikimomi a zube, ba a tsari na waƙa ba, ba wasan kwaikwayo ba, ba kuma a siga ta alƙaluman lissafi ba, sai dai yakan zo a zube, da zummar sadar da wata manufa da mawallafi ya ƙirƙira.

Ƙagaggun labaran Hausa a shafukan sada zumunta
Shafin sada zumunta wanda da Turanci ake kira Social Media, fasahar sadarwa ce ta zamani da jama'a ke sada zumunci tsakaninsu daga sassan duniya daban-daban, ta hanyar amfani da cibiyar sadarwa ta zamani da aka fi kira da network, wanda yake aiki da intanet.
Jama'a daga sassan duniya suna samun damar sada zumunci ta hanyar tattaunawa wato, ta hanyar yin magana ko kiran bidiyo (Video Call) ko kuma tattaunawa ta hanyar musayar saƙo (chats).
Ƙagaggun labaran Hausa na shafukan sada zumunta, waɗanda da Turanci ake kira Online Hausa Novels, ƙagaggun labarai ne da ake rubutawa a shafukan sada zumunta na zamani.
Ana rubuta su yawanci a wayoyin hannu waɗanda ake kira Android, tare da amfani da Cibiyar Sadarwa da ake kira Network, wadda take amfani da intanet. Bayan an rubuta, marubutan na watsawa a ƙananan shafukansu ko su tura a ƙungiyoyi na WhatsApp da Facebook da sauransu.
A wasu lokuta kuma masoyansu ke buɗe ire-iren waɗannan ƙungiyoyi su tura labaran. Kamar yadda aka bayyana a sama, su dai waɗannan labarai ba a littafi ake rubuta su ba, ana rubutawa ne a wayoyin hannu da ake kira Android.
Za a iya kiran waɗannan labarai da "Adabi A Tafin Hannu", musamman idan aka yi duba da yadda waya take ko yaushe a hannun jama'a yanzu. Waɗannan labarai an same su ne a ƙarni na 21.
Haka kuma marubuta waɗannan shafuka suna buɗe ƙananan shafuka ne na kansu da ake kira blogs da wattpad da sauransu.

Asalin fara rubuta ƙagaggun labarai a intanet

Dangane da tarihin samuwar ƙagaggun labaran shafukan sada zumunta na zamani, an samo bayanai daga bakin wasu marubutan waɗannan shafuka da wasu masu karanta labaran, da cewa an fara rubuta su a shekarar 2013.
Tun daga wannan lokaci ake samun yawaitarsu. Kawo yanzu, waɗannan labarai ƙara bunƙasa suke ta hanyar yawaita, tare da samun ƙaruwar marubutan da makaranta.
Idan muka yi duba da tarihin samuwar wannan sabon nau'in adabi, sai a ga bai daɗe ba, domin kwata-kwata bai fi shekara bakwai, ba amma ya sami karɓuwa ƙwarai musamman a wurin matasa.
Haka kuma yawan marubutan da ƙungiyoyinsu ma zai sa a yarda cewa waɗannan labarai sun sami karɓuwa.
Ana samun waɗannan labarai ne ta hanyar intanet , wato bayan sun saka shi a ƙananan shafukansu da suka haɗa da blog da wattpad da wordpress da sauransu sai ya watsu ta Facebook ko a karanta kai tsaye ta intanet, wato ta Opera da Goggle da Chrome da sauransu.
Daga baya kuma wasu masoyansu sai su watsa a WhatsApp musamman a shafukan ƙungiyoyi, wato groups. A wasu lokutan kuma su marubutan ne suke buɗe ire-iren waɗannan ƙungiyoyi na whatsApp inda suke watsa waɗannan labarai.
A tattaunawa da aka yi da wasu marubuta waɗannan labarai, sun tabbatar da cewa kusan dukkan marubuta labaran ba su taɓa rubuta littafin ƙagaggen labari ba sai da aka fara rubutu a shafukan sada zumunta na zamani.

Nasarar marubutan a Gasar Hikayata ta BBC
A tattaunawar da na yi da wasu marubutan shafukan sada zumunta, sun tabbatar da cewa, akwai ƙungiyoyi, kuma waɗannan ƙungiyoyi suna ɗauke da marubuta masu yawa, misali kamar Ƙungiyar Nagarta tana da aƙalla mambobi 50.
Haka kuma ire-iren waɗannan ƙungiyoyi suna tattaunawa a tsakaninsu domin magance matsaloli da suka shafe su, kasancewar ba a raba ire-iren waɗannan ƙungiyoyi da matsaloli.
A binciken da aka gudanar an tabbatar da cewa waɗannan marubuta da labaransu suna taka rawa a duniyar adabi, domin a shekarar (2018) ma, su suka lashe gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata.
Waɗanda suka kai ga nasara akwai; Safiyya Jibril (Ummou Abdul) da labarinta "'Ya Mace" ita ce ta farko, sai Sakina Lawal da ta zo ta biyu da labrinta mai suna "Sunanmu Daya" sai kuma Bilkisu Abubakar da ta zo ta uku da labarinta mai suna "Zina".
Haka kuma akwai gasa da wata ƙungiya mai suna 'Tsangayar Marubutan Hausa' ta saka, aka fitar da zakarun da suka yi nasara ranar 30/12/2018, su ne: Kamal Muhammad Lawan da ya zo na ɗaya da labarinsa mai suna "Nakasar Zuci".
Sai Hassana Sulaiman Isma'il (Sanah) da ta zo ta biyu da labarinta mai suna "Kuskurena". Sai kuma Isah Muhammad Machina da ya zo na uku da labarinsa mai taken "Kukan Zamfara".
Ƙarin labarai masu alaƙa

Kuɗin shiga
Marubuta ƙagaggun labaran shafukan sada zumunta suna da ƙungiyoyinsu na marubuta, haka kuma akwai ƙungiyoyi da suke na makaranta labaran, waɗanda suke ƙunsar marubuta da makaranta a haɗe.
A irin waɗannan ƙungiyoyin na haɗaka makaranta na samun damar yin sharhi kan labaran da ake turowa. Suna buɗe waɗannan ƙungiyoyi ne a shafukan sada zumunta.
Daga cikin ƙungiyoyin marubuta kawai akwai; Nagarta Writers da Fikra Writers da Haske Writers da Pure Moment of Life da Exclusive Writers da Talent Writers da Elequent Writers da Online Hausa Writers da Queen Writers da Fantastic Writers da sauransu.
Dangane da yadda suke cinikin labaransu, bincike ya gano cewa tun da aka fara rubutu a shafukan sada zumunta waɗannan marubuta suna rubuta labaran ne kyauta.
Amma a ƙarshen shekarar 2018 ne marubutan Fikra su bakwai suka buɗe wani shafi na kuɗi, ta kafar WhatsApp, wanda duk mai so zai tura kuɗi ta asusun banki da suka bayar da lamba, bayan an tura wannan kuɗi sai a tura hoton shaidar an biya ga ɗaya daga wakilan shafin (admin) ita kuma sai ta saka mutum a ƙungiyar.
Sunan wannan ƙungiya 'Taskar Fikra (original) , marubuciya Lubna Sufyan ce ta buɗe ta ranar 25/11/2018 kuma wannan ƙungiya tana ɗauke da marubuta da makaranta (duka mata) 196, cikin mambobi har da ni.
An fara tura labarai a ƙungiyar ranar 01/12/2018 ana bayar da labarai guda bakwai kamar yadda na faɗa a baya, su ne kamar haka:
- Gumin Halak, na Batul Mamman
- Dr. Sheerah, na Jeedderh Lawals
- Alƙalamin qaddara, na Lubna Sufyan
- A Dalilin Ɗa Namiji, na Fareeda Abdallah
- Tani Yar Amana, na Rufaida Omar da Fulani Bingel
- Gidan Bunu, na Sanah Shahada
- Dan Makaho, na Biebee Isa
Batul Mamman ta buɗe kwatankwacin wannan ƙungiya ranar 04-02-2019, inda take tura labarinta mai suna "Ku Dube Mu" a kan naira 300.
Haka ita ma Zainab Idris Makawa ta buɗe irin wannan ƙungiya ranar 07-03-2019 inda take tura labarinta mai suna Sarautar Mata a farashin naira 300.
Ana tura wannan kuɗi ta lambar asusun banki da suke turawa. Kawo yanzu waɗannan marubuta na dabarar sayar da labaransu ta waɗannan dabaru ko kuma ta Okada.

Wayar da kan al'umma

Wasu daga cikin marubuta labaran shafukan sada zumunta suna ƙoƙarin kawo labarai da suka dace da matsalolin da al'umma ke fuskanta. Suna ƙoƙarin saƙa labaransu da ire-iren waɗannan matsaloli domin su faɗakar, wato, saboda jama'a su hankalta su gyara.
Misali a wannan zamani akwai ƙalubale da ake fuskanta kamar matsalar fyaɗe da ta zama ruwan dare. Akwai labari da ya bayyana irin wannan matsala ta fyaɗe, shi ne Gumin Halak na Batul Mamman.
A ɓangare ɗaya sukan rubuta labarai domin jawo hankalin hukuma kan wata matsala da take addabar al'umma misali labarin "Ku Dube Mu na Batul Mamman."
Haka kuma sukan yi hannuka mai sanda su fargar da al'umma kan wasu abubuwa da yinsu ko barinsu shi ne dai dai. Misali Takari na Zainab Idris Makawa da sauransu.
Tsokaci kan wasu labaran na intanet
Labarin Gumin Halak: Gumin Halak na Batul Mamman labari ne da ya yi duba a kan matsalar fyaɗe, tare da bayyana irin taskun da yara waɗanda suka sami kansu a wannan yanayi suke shiga, su da iyayensu.
An bayyana yadda yarinya ta tafi aikatau birni ta gamu da wannan matsala a wurin ɗan matar da take yi wa aiki, da yadda rashin gata ya sa mahaifiyar yaron ta so a rufe maganar. Dalilin haka matar ta sallami yarinyar zuwa ƙauye don magaanar ta mutu.
A ɓangare ɗaya an bayyana irin taskun rayuwa da yarinyar (Muwaɗɗa) da iyayenta da ma danginta suka fuskanta a ƙauyensu. Wato yadda mutane suke tsangwamarsu da ƙyamarsu, wanda hakan ya sa dole suka yi ƙaura daga mahaifarsu, zuwa birni.
Labarin Ku dube mu: Ku Dube Mu Labari ne da Batul Mamman ta rubuta, wanda yake hasko wata matsala da ta shafi sojoji. An bayyana yadda rayuwar wani soja ta kasance, bayan an tura su kwantar da tarzoma sai ya tsinci kansa a kurkukun wata ƙasa, sakamakon an zargi yana cikin masu lefi.
A nan Najeriya kuma an bayyana wa iyalinsa ya rasu. Tun daga wannan lokaci iyalinsa suka shiga taskun rayuwa. Domin gwamnati ba ta ba su haƙƙokinsu ba, bare ta kyautata musu.
Labarin Takari: Takari na Zainab Idris Makawa labari ne da bayyana illar tafiya aikin takari da matan Hausawa suke yi zuwa ƙasar Saudiyya.
An bayyana yadda wata mata Hajiya Mai Sharwali ta yi watsi da sana'ar da take, ta ɗebi yara ƴan aiki ta tafi da su da zummar su yi aiki su samar mata kuɗi. An fito da irin tarin wahalhalu da matsalolin rayuwa da suka shiga.
Kammalawa
Ƙagaggun labaran Hausa na shafukan sada zumunta nau'in adabi ne da ya samu a ƙarni na 21.
Duk da a ɓangare ɗaya jama'a da dama na kallon marubuta wannan nau'in adabi a matsayin suna yaɗa ɓarna kamar batsa da fitsara, haka kuma suna keta mutuncin ƙa'idojin rubutun Hausa.
Amma wannan maƙala ta hango irin ayyukan waɗannan marubuta da kuma gudummawar da suke bayar wa, wajen bayyana matsaloli da suke addabar al'umma domin kawo gyara da ci gaba.












