Sheffield da Valencia na son Onyeka, United ta fasa sayar da Fernandes

Asalin hoton, Getty Images
Sheffield United da Coventry da Valencia na zawarcin danwasan Brentford da Nigeria Frank Onyeka, mai shekara 28 (Standard, external)
Aston Villa na zawarcin danwasan tsakiyar AC Milan da Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 29, domin ta inganta tsakiyarta. Wannan nada alaka da mumunan raunin da dan wasanta kuma ɗan Faransa Boubacar Kamara mai shekara 26 ya ji. (Telegraph - subscription required)
An kuma yi wa Manchester United tayin Loftus-Cheek inda suka tattauna domin samun bayyanai akan shi .(Talksport)
Villa ta tuntubi Fenerbahce kan danwasan gaba, Youssef En-Nesyri a cikin sa'oi 24 da suka gabata kuma dan wasan Morokon mai shekara 28 zai yanke shawara game da makomarsa nan bada jimawa ba inda Napoli da Juventus duk suna sha'awarsa. (Fabrizio Romano, external)
Tottenham na son ta sayi dan wasan West Ham da kuma Netherlands Crysencio Summerville mai shekara 24 kan fam miliyan 25. (Mail)
Liverpool na zawarcin dan wasan Tottenham da Netherlands Micky van de Ven, mai shekara 24, wanda kawo yanzu bai sa hannu kan sabon kwantaraginsa da Spurs ba. (Mail - subscription required, external)
Manchester United na shirin fadawa dan wasan tsakiyar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 31, cewa suna son ya ci gaba da taka leda da su na tsawon shekara guda kuma su na son ya yanke shawara kafin gasar cin kofin duniya ta bana. (ESPN)
Nottingham Forest za ta bar dan wasan Brazil Cuiabano, mai shekara 22, ya tafi wata kungiya a matsayin aro a wannan watan, yayin da take zawarcin dan wasan bayan Liverpool da kuma Girka, Kostas Tsimikas mai shekara 29, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Roma (Athletic - subscription required, external)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An yi watsi da tayin da Forest ta yi wa dan wasan Napoli Mathias Olivera , sai dai kawo yanzu tana ci gaba da tattaunawa da kungiyar kan dan wasanta dan kasar Uraguay mai shekara 28. (Tuttomercatoweb - in Italian)
Celta Vigo ta mika wa Wolves bukatar ba ta aron Fer Lopez , mai shekara 21 , kuma za ta biya dukkan albashin dan wasan tsakiyar Sifaniya da ke cikin tawagar masu shekara kasa da 21.(Sky Sports)
Real Madrid na son ta dauko dan wasan tsakiyar Portugal Ruben Neves, mai shekara 28, wanda ke son ya bar Al-Hilal, inda Manchester United ita ma ta na son tsohon kyaftin din Wolves . (AS - in Spanish), external
Dan wasan Chelsea da Ingila Cole Palmer, mai shekara 23, na son ya koma Manchester United, duk da cewa tsohon dan wasan Manchester City nada kwantaragi da Stamford Bridge wanda zai kare a shekarar 2033 . (Express)
Barcelona na son kyaftin din Manchester City , Bernardo Silva,mai shekara 31, idan kwantaraginsa ya kare a karshen kakar wasa. (Nacional - in Spanish)










