Sheikh Gumi: Shin malamin yana yin abubuwan da wasu gwamnatoci suka kasa yi ne?

Sheikh Gumi da tawagarsa tare da 'yan bindiga

Asalin hoton, Facebook/Sheikh Gumi

Bayanan hoto, Malamin ya ce Dogo Gide ya ba shi tabbacin daina kai hare-hare

A ci gaba da yunkurinsa na ganin 'yan bindigar da ke addabar arewacin Najeriya sun ajiye makamansu sun kuma rungumi zaman lafiya, fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya gana da 'yan bindigar da suka addabi jihar Neja a ranar Alhamis.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren Kagara da ke jihar ta Neja inda suka sace mutane 42 - dalibai 27 da ma'aikata uku da iyalansu 12.

Malamin ya gana da shugaban 'yan bindigar yankin wanda ake kira Dogo Gide.

A wani sako mai dauke da hotuna da aka wallafa a shafin Facebook na malamin ranar Alhamis, an nuna shi tare da Dogo Gide da tawagarsa a dajin Tagina da ke jihar ta Neja.

Dajin shi ne ya hada jihar Neja da jihar Kaduna ta bangaren Birnin Gwari inda 'yan bindiga suke yawan kai hare-hare.

Sheikh Gumi ya yi wa dan bindigar "nasihohi" game da muhimmancin yin sulhu da kuma haramcin yaki a watan Rajab da kuma rokonsu game da ajiye makamai da "haramcin yin fasadi a bayan kasa."

Malamin ya ce Dogo Gide ya tabbatar masa amincewa da yin sulhu yana mai cewa zai fara aiki domin ganin an cimma nasara, sannan ya gabatar da wasu bukatunsu ga gwamnati.

A baya dai Sheikh Gumi ya gana da wasu 'yan bindigar daji a jihohi irin su Zamfara da Kaduna domin kira a gare su da su ajiye makamai su kuma rungumi zaman lafiya.

Malamin ya roki hukumomi su yi afuwa ga dukkan dan bindigar da ya minace ya ajiye makamansa.

Sai dai a wata hira da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi da BBC Hausa ya shaida mana cewa ba da gaske 'yan bindigar suke ba domin kuwa sun sha cewa sun tuba amma su dawo su ci gaba da kai hare-hare.

Gwamnan ya ce yana da ra'ayin a buɗe wa 'yan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatinsa da masu garkuwa da mutane.

"Idan Gwamnatin Tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa ba, an shiga dazukan nan an kashe 'yan ta'addan nan a lokaci ɗaya, to za mu ci gaba da zama cikin matsala," in ji El-Rufai.

Bayanan bidiyo, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce babu haɗin kai tsakanin gwamnoni wajen yaki da ‘yan bindiga

Sai dai malamin ya ce irin wannan sulhu ya yi amfani a wasu jihohi don haka yake ganin ya dace a ko ina.

A cewarsa: "Akwai gwamnonin da kuma suke ganin sulhun shi ne hanya kuma sun yi sulhun an samu sauki. Idan ka je Zamfara, da tsakanin Gusau zuwa Shinkafi kamar hanyar Birnin Gwari ne. Amma yanzu idan ka je ga shi nan mutane suna kiwonsu suna noma. Ashe ka ga kenan sulhu yana amfani."

Wasu masana harkokin tsaro na ganin wanna aiki da Sheik Gumi yake yi yana da amfani sosai, suna masu cewa tamkar yana yin abubuwan da wasu gwamnatocin suka kasa yi ne.

Sai dai wasu na ganin shirin nasa na neman sulhu ba zai tabuka abin kirki ba ganin cewa 'yan bindiga da dama sun sha yin ikirarin tuba amma daga bisani su koma kai wa jama'a hare-hare.