Harin otel a Somaliya: 'Yadda na tsira daga hari a karo na huɗu'

Tsohon ma'aikacin BBC Mohamed Moalimu ya tsallake rijiya da baya a harin Otel da ka kai birnin Mogadishu na Somalia - karo na hudu kenan da harin mayakan al-Shabab ke ritsawa da shi a cikin shekaru bakwai.

Moalimu, wanda yanzu ke jagoranta kungiyar 'yan jaridar Somalia, ya shaida wa wakilin BBC Basillioh Mutahi yanayin da ya shiga da kuma yadda abokinsa ya kasance cikin mutum 20 da suka rasa rayukansu a harin Otel din Elite.

Jikina ya soma kakarwa. Zuciyata sai bugawa take kamar ana dukan ganga, sannan jikina na rawa. Wani irin hayaki ne ya turnuke sararin samaniya sai yanayin ya kasance ba a gani kwata-kwata.

Mutane na ta ihu. Ina iya ganin tasirin fashewar. Wasu mutane sun ji rauni da kwalaben tagogi da suka rushe, jini nata tsiyaya, wasu na ihun neman taimako.

Abokina, Abdirizak Abdi na son guduwa nan take. Ina son na dakatar da shi saboda karfin harbe-harbe da ake yi amma sai ya gudu ya bar ni, ta hanyar shiga Otel din.

Na tsaya domin nazarin daga ina harbin yake fitowa, saboda horon da na samu na abin da ya kamata ka yi idan ka shiga waje mai hadari.

Na shiga yanayi na taka tsan-tsan kuma hakan ya taimaka mun, saboda na duba me ke faruwa. Abin da ya cece ni kenan.

Na san inda zan gaggauta shiga, sannan ina gudu ina zilliya. Na yi tsalle na haye kan katanga, kana na diro kasa ta fuskar Otel din da ke kallon teku.

'Na cire rigata'

Na gagara yin gudu lokacin da na diro ta katanga. An yi ta harbin mutanen da suka yi kokarin guduwa a wurin da aka kai harin.

Nasan idan kana sanye da wani abu mai kala, kamar riga, hakan zai yi saurin jan hankali maharan. Ina sanye da koriyar riga don haka sai na cire ta na soma gudu a bakin teku. Babu takalma a kafata, domin na watsar da su.

An ci gaba da wannan harbi amma cikin ikon Allah na tsira.

A lokacin na yi kokarin kiran abokina amma wayar ba ta shiga.

Na yi kokarin cigiyarsa, ko yana da rai ko ya mutu. Na ga mutane da dama a kwance a kasa bayan harin. Wasu na ihu. Yanayin babu kyan gani.

Motocin agajin gaggawa sun soma iso wa wurin duk da cewa ana kan harbe-harben. Wani ya shaida min cewa Abdirizak ya jikkata kuma an tafi da shi asibiti.

Amma kash!, harsashin maharan da ke harbi kan mai uwa da wabi ya sami abokina. An harbe shi a ƙafa da ƙirji.

'Na je asibiti a gaggauce'

A lokacin, an takaita zirga-zirga kuma sojoji sun kwace iko sannan ana ta harbe-harbe.

Abdirizak, ma'aikacin ma'aikatar yada labarai ne, bai jima da zuwa gidana ba, ya dauke ni, ya tuka mu zuwa Otel din.

Tun da ba a barin motoci, a guje na tafi asibitin da aka kwantar da shi amma kash!, Abdirizak rai ya yi halinsa.

Ranar ta kasance mummuna - kuma karo na hudu da nake tsintar kaina cikin kazamin hari a Mogadishu.

Shi ne kawai lokacin da ban samu rauni ba ko guda.

A 2013 ina gaban harabar MDD lokacin da al-Shabbab suka kawo hari - ɗan ƙunaƙ baƙin wake ya ta da bam a jikin motata.

Sannan a 2016, a kusa da otel din Lido da ke bakin teku, an kai harin da na samu mummunan rauni a fuska.

Na kasance kwance jina-jina a cikin jini sama da sa'o'i biyu, na kwashe tsawon watanni a asibiti ina samun kulawa, a nan da Nairobi da kuma Landan saboda rauninkana su warke.

Na ji dan rauni daga baraguzai a duk jikina, har da tafin hannuna. Na samu na tsira daga ramin da ɗan ƙunar baƙin waken ya samar a jikin bango.

Wasu labaran da zaku so karantawa:

Wai a ce mutumin da abokinka ne, wanda kuma kuna aiki tare - muna tattaunawa irin ta abokai da shan shayi a ranar - yanzu ya mutu.

Ya mutu a cikin 'yan dakikoki. Ka yi tunanin munin yanayin. Na gagara bacci kwata-kwata. Na yi kokarin rintsawa amma na kasa. Harin ya rikitar da ni sosai.

Kusan mutum 20 aka tabbatar sun mutu, kari kan maharan hudu da wanda ya kai harin kunar bakin-waken.

'Iyalaina sun yi mamaki yadda na tsira'

Wannan adadi ne mai girma - mutane anan Mogadishu da ke wuni suna aiki, da rana haka sun kan ziyarci kantin cin abinci don shan shayi.

Akwai damuwa sosai kan aukuwar wannan harin. Ina ta fatan cewa abubuwa za su sauya ko a samu ci gaba.

Matata da 'yan uwana na yawan shawartata cewa na ƙauracewa kantunan sayar da abinci. Yanzu ya zama dole na bi shawararsu saboda wannan abu ne da ba za a daina ba.

A wannan karon iyalaina sun shiga kaɗuwa sosai domin sun san cewa Abdurizak ya rasu.

Lokacin da na kira su daga asibiti, sun gagara yarda cewa na tsira har sai da muka yi ido hudu.

Sun yi mamaki ganin cewa na tsira - a karo hudu daga irin wannan ƙazamin harin.