Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kayyade kayan aure a Somalia
A wani gari da ke Somalia an hana bikin aure na kece raini, a wani mataki na bai wa matasa kwarin gwiwa su zauna a gida su yi aure maimakon yin kaura.
Cikin sabbin ka'idojin da aka gindaya sun hada da hana walimar aure a manyan otel da yanka akuyoyi uku na abincin biki.
Kwamishinan garin Beled Hawa, Mohamud Hayd Osman ya shaida wa BBC hakan.
Jami'in ya kuma bayyana adadin kudaden da za a kashe wajen kayan dakin amarya kada su wuce dala 600, yayin da dukiyar aure kuma kada ta wuce dala 150.
Gidan angwaye na kashe har dala 5000 a wajen bikin aure a Somalia.
Wakilin BBC Somali, Bashir Mohamed ya ce dokokin sun kunshi kudaden da ake kashewa da suka hada da dukiyar aure da walima da kayan sawa da gwala-gwalan amarya da kuma kayan daki.
"Musulunci ya nuna cewa bai kamata a dinga tsawwalawa ba a wajen aure" A cewar Malam Osman ya shaida wa sashen BBC Somali.
A cimma matakin rage kashe kudaden 'Kece rainin ne' bayan wata ganawa da jami'ai suka yi a sanadin haihuwar yara 150 ba tare da aure ba a garin.
"'Yan mata ba sa son yin aure har sai an kashe musu makudan kudade wajen sayen gwala-gwalai da kuma kayan daki. " In ji jami'in.
Ana cikin wani hali a garin na Beled Hawa da ke makotaka da kasar Kenya, saboda fari da kuma rashin aikin yi --ga tsadar aure, lamarin da yasa samari ke barin garin a cewar kwamishinan.
"Dole a taimakawa 'yan mata su auri zamarin da suke su saboda a samu ci gaba a al'umma," In ji shi.
Inda ya dala $600 zai isa sayen babban gado da teburi da kujeru da kuma sauran kayan girki.
A al'adance dai ana shafe tsawon mako guda ana bikin aure a Somalia.