Shugaban ƙasar Somali: Da gaske ya yi dambe da mataimakinsa a shirin talbijin na kai-tsaye?

Lokacin karatu: Minti 2

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya yi iƙirarin cewa Shugaban Yankin Somali, Mohamed Abdullahi Farmaajo ne suke dambata wa da mataimakinsa a wani shirin talabijin da ake yi kai-tsaye.

Wasu rahotanni sun ce faɗan ya ɓarke ne yayin da ake taron manema labarai, wanda shugaban yake jagoranta.

Wasu kuma suka ce sun dambata ne saboda yankin na Somali mai cin gashin kansa, ya gaza samun wani ci gaba tun bayan da ya ɓalle daga ƙasar Somaliya.

Sai dai wannan labari ba gaskiya ba ne.

Abin da muka binciko game da bidiyon

An fara wallafa bidiyon ne a shafin Dhamays Media Production na YouTube ranar 12 ga watan Satumban 2015.

Bidiyon mai tsawon minti 20, an kalle shi sau fiye da miliyan ɗaya.

Sun wallafa tare da rubuta kanu cewa: "Daawo Dagaalkii Shirgudonka Golaha Wakiilada Somaliland" abin da ke nufin "Kalli yaƙi tare da Kakakin Majalisar Wakilan Somaliland".

Binciken BBC ya gano cewa faɗan ya faru ne tsakanin Kakakin Majalisar Wakilan Somaliland, Abdirahman Mohamed Abdullahi da Bashe Mohammed Farah, mataimakin kakakin majalisar.

Wata kafar mai suna Star TV ta wallafa a YouTube ɗin tare da kanun: "Dagaalkii Iyo Gacan Hadalkii Shirgudoonkii Wakiilada Iyo Guushii Mucaaridka Somaliland," abin da ke nufin "yamutsi da hannun Majalisar Wakilai da kuma nasarar 'yan adawar Somaliland."

Abin da ya haddasa faɗan

Wata maƙala da muka samu daga shafin archives wadda aka rubuta ranar 13 ga Satmban 2015 - kwana ɗaya da ɓullar bidiyon - ta bayyana cewa an yi faɗan ne sakamakon zargin da aka yi wa Bashe Mohammed Fara da ɓata sunan Somaliland a idon duniya.

Wani rahoto ya ce mataimakin kakakin ya yi yunƙurin yin juyin mulkin majalisar ne kafin daga bisani a gano shi.

Ba su bari ya yi magana ba kafin a fara kai naushi yayin da kakakin yake yi wa 'yan jarida ƙarin bayani.

Saboda haka ba shugaban Somali ba ne suke faɗa da mataimakinsa kamar yadda mutane suka riƙa yaɗawa.

Somaliland

  • Yankin Somaliland ya ayyana samun 'yancin kai a shekarar 1991 daga ƙasar Somaliya
  • Sun ƙirƙiri takardar kuɗinsu
  • Suna gudanar da zaɓensu da kansu
  • Shugaban yankin na yanzu shi ne Muse Bihi da kuma Abdi Abdirahman Saylici a matsayin mataimaki
  • Sai dai ƙasashen duniya ba sa ɗaukar yankin a matsayin ƙasa mai zaman kanta.