Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya makon da ya gabata

Tun daga ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2020 zuwa ranar Asabar, abubuwa da dama muhimmai sun faru a Najeriya kuma sun ja hankulan 'yan kasar.

Mun tsakuro muku muhimmai daga cikinsu.

An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa bisa yin ɓatanci ga Annabi

A makon da gabata ne wata babbar kotu a Kano a arewacin Najeriya ta yanke wa wani matashi mai shekaru 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. tare da wani da ya yi ɓatanci ga Allah.

Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka ƙara.

"An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka," in ji Jibo Ibrahim.

Tun a watan Maris na 2020 ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta.

Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

An yanke hukuncin kisa kan tsohon da ya yi wa yarinya fyade

Kwanaki kaɗan bayan hukuncin da aka yanke a Kano na rataye wani da ya yi ɓatanci ga annabi, sai kuma wata kotun a Kano ta yanke hukuncin kisa kan wani tsoho da aka samu da laifin yi wa wata yarinya fyade.

Alkalin kotun, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, ya ce za a kashe mutumin, mai suna Mati Audu mai shekara 70, ta hanyar rajamu.

Kotun ta samu mutumin, wanda dan karamar hukumar Tsanyawa ne, da laifin yi wa wata yarinya 'yar shekara 12 fyade.

Mati Audu ya tabbatar wa kotun cewa shi ne ya aikata laifin, kuma sau hudu ana dage shari'ar domin alkali ya ba shi dama ko zai sauya matsayinsa, sai dai duk lokacin da aka koma kotu yana jaddada mata cewa shi ne ya yi wa yarinyar fyade. Amma ya bukaci a yafe masa.

Kalaman Obadiah Mailafia kan Boko Haram sun bar baya da ƙura

A makon da ya gabata ne hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai ta Najeriya ta ci tarar gidan rediyon Nigeria Info naira miliyan biyar, saboda zarginsa da yada kalaman ɓatanci bayan wata tattaunawa da ya yi da Dakta Obadiah Mailafia.

Dakta Mailafia, wanda tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ne, ya yi zarge-zarge da dama a cikin tattaunawar, ciki kuwa har da zargin ɗaya daga cikin gwamonin arewacin Najeriya da jagorantar ƙungiyar Boko Haram.

Bayan wannan tattaunawa ta karaɗe shafukan sada zumunta ne hukumar tsaro ta farin kaya a ƙasar wato DSS ta gayyaci Dakta Mailafia a ranar Laraba domin gudanar da bincike kan irin zarge-zargen da ya yi.

Obadiah ya ce a kasuwa ya tsinci zancen a bakin wasu Fulani.

An kama mahaifin da ya tsare ɗansa tsawon shekara uku a Kano

A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce an samu nasarar ceto wani matashi da aka tsare shi a cikin gidansu tsawon shekara uku ba tare da ba shi damar fita ba.

Tun da farko dai 'yan sanda sun bayyana cewa an tsare yaron tsawon shekaru bakwai, sai dai daga baya mahaifin matashin ya ce shekaru uku ne.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa BBC hakan ne a ranar Juma'a da safe.

A ranar Alhamis da yamma ne bidiyon da ke nuna yadda aka kuɓutar da yaron ya watsu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta da muhawara a faɗin ƙasar.

Gwamna Ortom ya bukaci a bar masu hankali su mallaki bindigar AK 47

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Binuwai,Samuel Ortom, ya bukaci gwamnatin tarayya ta bai wa `yan kasar da suka mallaki hankali lasisin mallakar bindiga samfurin AK47 domin su kare kansu daga hare-haren da miyagu ke kaiwa.

Gwamnan ya ce ba da lasisin ne kawai mafita, saboda manyan makaman da ke hannun miyagu sun fi karfin bindigar da doka ta ba da izinin mallaka.

Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya yi wannan bayanin ne a cikin wata ƙasidar da ya gabatar a wani taron gwamnonin Najeriya da aka yi ta intanet.