Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jubril Aliyu Kebbi: An kama kishiyoyi da uban yaron da aka ɗaure a turken awaki
Gwamnatin jihar Kebbi ta ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan abin da ta kira 'rashin imanin riƙon sakainar kashin da aka yi wa yaro', ɗan kimanin shekara goma mai suna Jibril Aliyu.
Cikin wata sanarwa da Aliyu Bandado Argungu, babban mataimaki na musamman kan harkar shafukan sada zumunta ga gwamna ya ce binciken zai yi ƙoƙarin bankaɗo sanadi da kuma gazawar mutanen da suka kamata su kare rayuwar ƙananan yara da ma manya a jihar.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana takaici da damuwa kan yadda Jibril ya shiga garari ba kawai a hannun iyayensa ba, har ma da gazawar maƙwabtansu da ma ɗaukacin harkokin gudanawar gwamnati.
Kuma a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na tiwita, gwamnatin Kebbi ta ce za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar yaron da kuma dawo da shi cikin hayyacinsa.
A cewarta, kishiyoyin babar Jibril ne da mahaifinsa suka ɗaure shi a turken awaki tsawon shekara biyu a unguwar Badariyya cikin Birnin Kebbi kafin kuɓutar da shi a ranar Lahadi.
Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an hukumar kare haƙƙin ɗan'adam suka kuɓutar da Jibril sanye da wata jar riga yana tafiya da ƙyar saboda sirancewa.
Barrista Hamza Attahiru Wala na hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ya ce sun samu Jibril Aliyu ne ɗaure a rumfar awaki, "muka yi magana da matan (gidan) suka ce eh yaron bai da hankali".
Ya ce: "Mun same shi yana cin kashi. Kashin busashe (dabbobi).... had da nashi ɗin, ci yake yi, saboda an ɗaure shi... ga shi nan da busashe kawai yake hurɗa".
"An ɗauke shi kawai marah hankali, gaba ɗai hurɗar shi da dabbobi ne gaba ɗai. Ko magana bai iya ba," in ji Hamza Wala.
Lauyan ya shaida wa BBC cewa iyayensa sun yi iƙirarin cewa Jibril Aliyu na da farfaɗiya kuma ba shi da hankali. "Amma mu hay yanzu ba mu gani ba".
Sai dai a wani bidiyo an ji ɗaya daga cikin kishiyoyin babar Jibril na musanta zargin ɗaure yaron. Ta yi rantsuwar cewa wallahi tana ba shi abinci.
Tuni dai 'yan sandan jihar Kebbi suka ce sun tsare uban Jibril tare da matansa uku don ci gaba da bincike kan dalilin da ya sa aka bar shi cikin mummunan yanayi tsawon lokaci
DSP Nafi'u Abubakar ya ce "Eh to, alhamdulillahi! Yanzu haka yana asibiti shi yaron.... muna so mu ji sakamakon asibiti me ze nuna ko rashin abinci ne da tsagwamawa suka sa shi halin da yake ciki".
Gwamnatin Kebbi dai ta kuma ba da umarni a titsiye tare da bincikar ɗaukacin ma'aikatan kula da walwalar jama'a na ƙananan hukumomin jihar.
Ya dai ɗora wa kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu Hassan Muhammad Shalla Gwandu da mataimakiya ta musamman kan harkar mata Hajiya Zara'u Wali da shugaban ƙungiyar ƙananan hukumomi Shehu Marshal da Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kebbi alhakin gudanar da binciken