Zaben Kogi: Adeyemi ya kayar da Dino Melaye

Asalin hoton, @SenSmartAdeyemi
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC ta tabbatar da Smart Adeyemi na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma a kasar.
Nasarar da Adeyemi ya samu na zuwa ne biyo bayan zabe zagaye na biyu da aka gudanar a jihar bayan kotu ta soke na farko da aka gudanar a watan Fabrairun bana.
A ranar 16 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zaben zagaye na biyu wanda bai kammalu ba, hakan ya sa hukumar INEC ta saka 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a karasa zaben,
An gudanar da zaben ne a rumfuna 53 a kananan hukumomi 7 a jihar ta Kogi.
A zaben da aka gudanar wanda bai kammalu ba na 16 ga watan Nuwamba, Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ke kan gaba da kuri'u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam'iyyar PDP ke da kuri'u 59,548.
Hakan ya sa Smart ke kan gaba da kuri'u 20,570.
A karashen zaben da aka gudanar a rumfuna 53 a ranar Asabar, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 8,255, sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 2,585.
Baturen zabe a jihar Farfesa Olaide Lawal ya bayyana cewa Adeyemi ya samu jimlar kuri'u 88,373, sai kuma abokin karawar nasa wato Dino Melaye ya samu kuri'u 62,133.











