An shammace mu kan sabbin takardun kudi - 'Yan Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Babban bankin Ghana zai saki sabbin takardun kudi na Ghana cedi 200 da na 100 da kuma kwabon Ghana cedi 2 daga makon gobe.
Babban bankin ya ce sabbin takardun kudin za su taimaka wa jama'ar kasar wajen biyan kayayyaki masu tsada.
Amma takardun kudin sun kasance wata alama ta hauhawar farashi da karyewar kudin Ghana.
An samar da kudin Ghana cedi a 2007 ne bayan da babban bankin kasar ya soke sifili hudu daga tsohon kudin kasar.
Wannan na nufin cedi 10,000 ya zama Ghana cedi 1 ke nan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A wancan lokacin Ghana cedi 1 daidai ya ke da dalar Amurka 1, amma a yanzu ya fadi kasa zuwa senti 0.18.
Kafin fitowar wadannan sabbin takardun kudin, takardar Ghana cedi 50 ce mafi daraja a kasar, wadda ke da darajar dala 9 ta Amurka.
Gwamnan babban bankin Ghana, Ernest Addison ya ce "An yi tunani mai zurfi gabanin yanke shawarar fito da wadannan sabbin takardun kudin."
Amma wasu 'yan kasar Ghana sun soki matakin, inda suka ce sabbin takardun na iya sa 'yan kasuw asu kara farashin kayayyakinsu.
Amma babban bankin na Ghana na da yakini cewa sabon matakin da ya dauka na fitar da sabbin takardun kudin zai taimakawa mutane masu mu'amulla da takardun kudi masu yawa a kullum.











