Brexit: Abin da kuke son sani kan ficewar Birtaniya daga Turai

Bayan kwashe kusan kimanin shekaru uku ana ta dambarwar abin da ake kira Brexit, yanzu an yanke cewa Birtaniya na shirin fita daga Tarayyar Turai da karfe 23:00 GMT a ranar 31 Oktoban 2019.
Menene Brexit?
Brexit na nufin - fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai.
Mecece Tarayyar Turai?
Tarayyar Turai kungiya ce ta tattalin arziki da siyasa da ta kunshi kasashe 28 na nahiyar Turai da ake kira European Union, EU. Akwai damar saye da sayarwa da shige da ficen mutane tare da damar yin aiki tsakanin 'yan kasashen.
Birtaniya ta shiga tarayyar a 1973, a lokacin ana kiran ta da Gundumar Tattalin Arziki ta Turai. Idan Birtaniya ta fita a ranar 31 ga watan Agusta, ita za ta zama kasa ta farko da za ta fara fita daga tarayyar.
Me ya sa Birtaniya za ta fita?
An gudanar da zaben raba gardama wanda aka yi a ranar Alhamis 23 ga watan Yunin 2016, domin zabar fitar Birtaniya ko tsayawar ta cikin kungiyar.
Masu son ficewa ne suka yi galaba da kashi 52% a kan masu son tsayawa da suka samu kashi 48%. Mutanen kasa kashi 72% ne suka fito kuma sama da mutum miliyan 30 ne suka yi zaben inda mutum miliyan 7.4 suka zabi a ficewa.
Me ya sa har yanzu ba a fita ba?

Asalin hoton, Getty Images
An yi shirin ficewar Birtaniya ne a ranar 29 ga watan Maris din 2019. Kimanin shekara biyu ke nan bayan da Firai ministar lokacin Theresa May ta yi amfani da wani sashe da ake kira Article 50 wajen fita daga tarayyar wanda hakan ne ya haifar da yarjejeniyar ficewar. Amma an jinkirta lokacin fitar har sau biyu.
Birtaniya da tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya a watan Nuwambar 2018 amma 'yan majalisa suka ki amince wa da ita har sau uku.
Mene ne yarjejeniyar fitar ta kunsa?
Yarjejeniyar ta kunshi tsayayyiyar yarjejeniyar fita wadda ta bijiro da 'saki' da kuma fita a siyasance da kuma abin da ya shafi huldar saye da sayarwa a nan gaba.
Yarjejeniyar fitar ta kunshi abubuwa kamar haka;
- Hakkin 'yan kasashen tarayyar Turai a Birtaniya da turawan Ingila a tarayyar
- Kudaden saki da Birtaniya za ta biya tarayyar (ana tsammanin za su kai pam biliyan 39)
- Barin shige-da-fice a iyakar Ireland.
Me ya sa majalisa ta ki amincewa da yarjejeniyar fitar?
Babban lamari ga mambobin jam'iyya mai mulki da na DUP shi ne barin shige da fice a iyakar Ireland.
A yanzu, babu wasu shingaye da ke haifar da tsaiko ga shige da ficen mutane da kayayyaki tsakanin Kudancin Ireland da jamhuriyar Ireland. Saboda haka aka yarjejeniyar ta tanadi wani abu da ake kira 'Backstop' wanda ke nufin kandagarki ga ci gaba da hada-hadar jama'a da kayayyaki a kan iyakar ko da kuwa bayan Birtaniyar ta fice daga EU din.
Kandagarkin zai fara aiki ne kawai idan ba a cimma wata tsayayyar yarjejeniya ba tsakanin Birtaniya da EU. 'Backstop' din zai tabbatar da ci gaba da kasancewar Birtaniya a shige da ficen kaya na Tarayyar ta Turai, amma Arewacin Ireland din zai zama yana bin wasu dokokin Kasuwar Bai daya ta EU.

Asalin hoton, Getty Images
Ko Birtaniya za ta iya ficewa daga EU ba tare da yarjejeniya ba?
Firai minista Boris Johnson na son Birtaniya ta fita daga Tarayyar ta Turai ta cire batun kandagarki wato 'Backstop' daga yarjejeniyar. Yana son a bi wasu hanyoyin maimakon na 'Backstop' da kuma na fasahar zamani.
To sai dai Tarayyar Turai har yanzu ba ta amince da sauya batun kandagarkin ba.
Mr Johnson ya ce dole ne Birtaniya ta fice daga EU ranar 31 ga watan Oktoban 2019 ko da kuwa ba bu tare da yarjejeniya ba.
Hakan kuwa na nufin Birtaniya za ta fita daga tsarin shige da ficen kayayyaki da kasuwar bai daya na EU.

Asalin hoton, PA Media
Mene ne Kungiyar shige da ficen kaya da kasuwar bai-daya?
Kungiyar shige da ficen kayayyakin Tarayyar Turai dai na tabbatar da ganin dukkanin kasashen tarayyar na karbar haraji bai daya kan kaya da ke shiga cikin kasashen daga kasashe mambobi. Ba kuma sa sanya wa juna haraji.
Ita kuma kasuwar bai-daya na tabbatar da ganin cewa kayayyaki da abubuwa da ma jama'a na zirga-zirga tsakanin kasashen kungiyar 28 da kuma kasashe biyar da ba sa cikin EU amma suna cikin Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin nahiyar da suka hada da Iceland da Norway, da Liechtenstein da kuma Switzerland.
Kasashen da ke cikin kasuwar ta bai-daya na amfani da dokoki iri daya kan abin da ya shafi ingancin kaya da dai sauran su.

Asalin hoton, Getty Images
Ko ficewa ba tare da yarjejeniya ba ka iya haifar da matsala?
Idan Birtaniya ta fita daga kungiyar shige da ficen kayayyaki ta EU da kuma kasuwar bai daya, to Tarayyar Turai za ta fara sanya haraji a kan dukkanin kayayyakin Birtaniya. Hakan ka iya janyo tsaikon shigar da kaya a tashoshin jiragen ruwa da ma cunkosan ababen hawa, al'amarin da ka iya shafar tattalin arzikin Birtaniyar.
Mr Johnson ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya taushi mutane da su cire fargabar matsalar tattalin arziki daga zuciyarsu, inda har ya sanar da karin kudi har £2.1bn idan aka fice ba tare da cimma wata yarjejeniya ba a ranar 31 ga watan Oktoba.
Ina aka dosa?
Idan har ba a cimma komai ba to fa Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai ne a ranar 31 ga Oktoban na 2019.
To sai dai firai minista ya ce har yanzu yana son ganin an fice a ranar da aka sanya din kuma ba tare da kulla wata yarjejeniya ba, wani batu da 'yan majalisa da dama suka ce za su taka wa burki.
Da alama taka wa ficewa daga EU ba tare da yarjejeniya ba abu ne mai kamar wuya kasancewar Mista Johnson ya sanar da cewa zai kara wa 'yan majalisar tsayin hutun da suke yi da mako biyar.
Hakan zai rage yawan kwanakin aikin 'yan majalisar ballantana har su taka masa burki. Masu suka dai na ganin matakin da firai ministan ya dauka tamkar yi wa tsarin dimokradiyya karan-tsaye ne.
To sai dai gwamnati ta ce an yi hakan ne da manufar samun damar sake tsari da bujuro da manufofi dangane da ficewar kasar daga EU.

Asalin hoton, BBC/Guy Levy
Za a iya dakatar da ficewa ba tare da yarjejeniya ba?
Mafi rinjayen 'yan majalisar dokokin Birtaniya ba sa goyon bayan ficewa ba tare da yarjejeniya ba musamman bisa la'akari da yadda shugabannin jam'iyyun Labour da Lib Dems da SNP da kuma the Green Party suke adawa da al'amarin.
Hanyar da za a bi wajen hana ficewa ba tare da kulla yarjejeniya ba ita ce tumbuke gwamnati ta hanyar kada mata kuri'ar yanke kauna sannan a maye gurbinta da sabuwar gwamnatin da za ta nemi dan tsaiko dangane da ficewar kasar daga Tarayyar ta Turai, domin samun damar gudanar da babban zabe ko kuma sake yin kuri'ar raba-gardaba kan batun.
Hanya ta biyu kuma ita ce yin wata doka da za ta tilasta wa gwamnatin Birtaniya neman dagi dagaTarayyar Turai.
Tuni dai wasu masu fafutuka suka fara tunanin neman yi wa tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin rage kaifin ikon da firai minista yake da shi kan majalisar dokoki.
Akwai kuma yiwuwar 'yan majalisar za su iya hana ficewar daga Tarayyar Turai baki daya duk da cewa wasu sun ce za su goyi bayan yin hakan ba tare da bukatar wata yarjejeniya daga EU ba.

Asalin hoton, Thinkstock

Asalin hoton, EPA











