Boris Johnson ba zai kare muradun Birtaniya ba - Jeremy Corbyn

Jeremy Corbyn

Asalin hoton, PA Media

Shugaban jam'iyyar hamayya a Birtaniya Jeremy Corbyn, ya bayanna cewa zai yi duk mai yiwuwa, domin ganin cewa lallai Birtaniya ta kulla yarjejeniya kafin fitarta daga Tarayyar Turai.

Shugaban jam'iyyar ta Labour ya ce ficewa daga Birtaniya ba tare da wata kwakkwarar yarjejeniya ba, hakan zai jawo rasa ayyukan yi kuma zai sa kasar ta dawo tamkar baiwa ga Shugaba Trump ko kuma gwamnatin Amurka.

Ana sa ran Mista Corbyn zai tattauna da shugabannin 'yan hamayya a kasar a ranar Talata domin ganin cewa sun dakatar da hakan daga faruwa.

Sabon Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa Birtaniyar za ta fice daga Tarayyyar Turai a karshen watan Oktoba ko da kuwa bata cimma wata yarjejeniya ba a birnin Brussels.

Ko a 'yan kwanakin nan sai da shugaban majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk da Firaministan Birtaniya Boris Johnson suka yi musayar kalamai game da wanda ke da laifi idan Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turai ba tare da wata yarjejeniya ba.

Tun bayan da ya zama Firaminista, Boris Johnson ya sha nanata cewa babu makawa Birtaniya za ta fice daga a kungiyar a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2019.