Boris Johnson shi ne sabon firaiministan Burtaniya

Boris Johnson

Asalin hoton, Reuters

Jam'iyyar Conservative ta Burtaniya ta zabi Boris Johnson a matsayin sabon shugaban jam'iyyar Conservative inda zai zama sabon Firaiministan kasar.

Mista Boris ya yi nasara a kan abokin takararsa, Jeremy Hunt bayan samun kuri'u 92,153 fiye da 46,656 da Jeremy Hunt din ya samu

A ranar Laraba ne dai Boris Johnson zai karbi ragamar shugabanci daga hannun Theresa May.

A jawabin da ya gabatar bayan an bayyana shi da wanda ya yi nasara, Mr Johnson ya yaba wa Theresa May inda ya ce " Abin alfahari ne yin aikin da na yi a gwamnatinta".

Mista Boris ya sha alwashin kammala fita daga tarayyar Turai sannan zai hada kan 'yan kasar tare da cin galaba a kan shugaban jam'iyyar adawa ta Labor, Jeremy Corbyn.

Firaiminista mai barin gado, Theresa May ta taya Mr Johnson murna, inda ta yi masa alkawarin ba shi goyon baya.