Brexit: Theresa May ta cimma jituwa da ministocinta

Theresa May ta fuskanci mummunar hamayya kan yarjejeniya raba gari da EU

Asalin hoton, AFP/getty

Bayanan hoto, Theresa May ta fuskanci mummunar hamayya kan yarjejeniya raba gari da EU

Majalisar ministocin Burtaniya ta amince da wani daftari a kan ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Ministocin firaminista Theresa May, sun amince da tsare-tsaren dangantaka da Tarayyar Turai a nan gaba ta fuskar siyasa. Tuni dai aka wallafa daftarin.

Misis May ta ce matakin ya kunshi daukan matakai masu wuya, musamman a kan batun kaucewa amfani da jami'an fasa kauri da kuma sanya matakan tsaro tsakanin iyakar Ireland ta arewa da Jamhuriyar Ireland.

Firaministar dai ta fuskanci mummunar hamayya kan yarjejeniyar, har ma daga 'yan majalisa na jam'iyyarta.

Babban jami'in da ke shiga tsakanin na kungiyar Tarayyar Turai kan ficewar Burtaniyar daga kungiyar, Michel Barnier ya ce shawarar da Burtaniya ta yanke wani mataki ne mai muhimmaci a kokarin da take da raba gari da kungiyar.

Mista Barnier, ya ce dukkanin bangarorin biyu sun samu gagrumin ci gaba a kokarin cimma jituwa, sannan hakan zai karfafa shirya taron shugabannin sauran kasashe kungiyar 27, don ji ko za su amince da yarjejeniyar.

Hakazalika ya ce akwai yiwuwar shirya wani taro a cikin wannan watan, kafin daga baya a nemi amincewar bangaren majalisar Burtaniya da na Tarayyar Turan.

Yayinda matakin Burtaniyar na ficewar ya shiga matsayar karshe, har yanzu akwai bukatar sai sauran shugabannin kasashe 27 na tarayyar turai sun yanke shawarar ko za su amince da daftarin yarjejeniyar.

Hakazalika Misis May din na fuskantar adawa daga 'yan majalisar dokin Burtaniyan, wajen samun damar kammala yarjejeniya duk da cewa ta samu goyon bayan majalisar ministocinta.

Tun da farko Misis May ta fadawa Majalisar dokokin kasar cewa daftarin wanda aka yi shekara fiye da guda ana tattaunawar neman sulhu zai mutunta sakamakon zaben raba gardamar da aka yi game da ficewar Birtaniya daga EU.

Firaministar ta kuma ce iyakokinsu da dokokinsu da kudinsu duk za su koma karkashin ikonsu, kuma za su fice daga tsarin kamun kifi da na aikin noma tare da kare guraben ayuika da tsaro da kuma kimar Burtaniya .

Sai dai wasu 'yan majalisar dokoki ma su goyon ficewar Burtaniyar da kuma wadanda suke adawa da shi, da ke cikin jam'iyyarta ta Conservative sun ce ba za su goyi bayan matsayar da aka cimma ba.