Magajin Garin Landan: A sake duba batun ficewar Birtaniya daga Turai

Sadiq Khan
Bayanan hoto, Magajin Gari Khan: Ya kamata a sake zaben raba gardama kan ficewar Birtaniya daga Turai

Gwamnatin Birtaniya na ta kara samun kiraye-kirayen sake duba batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

Na baya-bayan nan ya fito ne daga Magajin Garin Landan, Sadiq Khan, wanda ya bukaci Firai minista Theresa May ta sake gudanar da wani zaben rabe gardama kan batun.

Jam'iyyar Liberal Democrats ma ta fito tana sukar batun.

Magajin Garin ya bayyana cewa Birtaniya na fuskantar zabi tsakanin ficewa babu shiri ko gurguwar ficewa nan da wata shida mai zuwa, lokacin da a hukumance aka shirya rabuwar kasar da Tarayyar Turai.

Ya ce baya tsammanin firai minista Theresa May na da amincewar 'yan kasar da ta ke caca da tattalin arziki da rayukan al'umomin kasar.

Ya kuma nemi a gudanar da sabon zaben ne domin a ba 'yan Birtaniya wata dama ta rungumar tsarin gwamnatin Conservative mai mulkin kasar ko Birtaniyar ta yi zamanta a cikin Tarayyar ta Turai.

Ita kuwa firai minista Theresa May ta soki wannan shawarar, inda ta ce gudanar da wani sabon zaben raba gardama tamkar cin amanar tsarin demokradiyyar kasar ne.

Amma da alama magoya bayan Mrs May na ragua matuka, domin jam'iyyar adawa ta Liberal Democrats ma sun bi sahun 'yan babbar jam'iyyar adawa ta Labour wajen kira da a sake gudanar da zaben raba gardama kan batun na Brexit.

'Yan jam'iyyar ta Lib Dems din na zawarcin 'yan majalisu daga manyan jam'iyyu biyu na Conservatives da Labour da su sauya sheka zuwa jam'iyyarsu idan ba su gamsu da inda siyasar kasar ta nufa ba.