Majalisar Birtaniya ta yi watsi da shirin Brexit na Theresa May

Asalin hoton, PA
'Yan majalisar Birtaniya sun fitar da wasu sabbin shawarwari domin sauya makomar kasar a kan batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai wato Brexit.
Wannan matakin na nufin tarar numfashin firai minista Theresa May ne wadda ke shirin mika masu sabon shirinta a kan batun na Brexit.
Misis May za ta nemi amincewar 'yan majalisar, amma wasu 'yan majalisar tuni suka yi watsi da wannan sabon yunkurin nata, inda suka ce ba shi da bambanci da na da.
Duk wanda ya dauka cewa Firai ministar Ingila Theresa May za ta samar da wata dabara ta daban kan batun nan na ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai wato Brexit, bayan da majalisar kasar ta yi watsi da shirinta a makon jiya sai ya shirya shan mamaki.
Sabon shirinta na yanzu kusan daya yake da wanda majalisar ta yi watsi da shi, amma akwai bambanci daya:
Za ta sauya wani bangare na shirin nata da ya sha kushe wajen 'ya'yan jam'iyyarta ta Conservative da kuma 'yan karamar jam'iyyar nana ta DUP wadanda su ne dalilin da har yanzu ba a fatattake ta daga mulki ba.
A daya bangaren kuma, kokarin da ta yi na zawarcin jam'iyyun adawa domin su mara wa sabon shirin nata baya bai sami karbuwa ba, musamman daga babbar jam'iyyar adawa ta Labour.
Saboda haka tun da babu wani sauyi na a zo a gani, ban da na cewa lokaci na kara kurewa kafin ranar 29 ga watan Mayu wanda ita ce ranar da kasar za ta fice ko ta shirya, ko ba ta shirya ba.











