Mrs May na fuskantar kuri'ar yanke kauna bayan ta sha kaye

Theresa May

Asalin hoton, UK PARLIAMENT/MARK DUFFY

Firai ministar Burtaniya Theresa May na fuskantar kuri'ar yanke kauna bayan da 'yan majalisa suka yi watsi da yarjejeniyar ficewar kasar daga tarayyar turai.

'Yan jam'iyyar Labour ne dai suka fito da kudurin sabon zabe bayan da 'yan majalisar suka yi watsi da daftarin da ke kunshe da yarjejeniyoyin ficewa daga tarayyar turai da kuri'a 230.

Ana dai sa ran cewa za a yi wannan kuri'ar yanke kaunar da misalin karfe 19:00 agogon GMT.

Mrs May dai ta shaida wa 'yan majalisar cewa za ta dawo majalisar wakilan makon gobe da wani shirin da zai maye gurbin wannan, idan har ta tsallake kuri'ar yanke kaunar.

A daren Talata Mrs May ta bayyana cewa " 'yan majalisa sun yanke hukunci kuma gwamnati za ta yi biyya,'' inda za a bar jam'iyyu su tattauna tsakaninsu domin a samu ci gaba.

Menene zai biyo baya?

Ana sa ran cewa 'yan majalisa za suyi muhawara a kan kudirin kuri'ar yanke kauna na kusan sa'o'i shida bayan tambayoyin da za'ayi wa Mrs May da karfe 12:00 agogon GMT.

Shugaban Jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya ce wannan zai basu dama su yanke hukunci a kan abinda ya kira "gazawar wannan gwamnatin."

Wakilin BBC a kan harkokin siyasa Iain Watson ya bayyana cewa idan Mrs May ta tsallake wannan kuri'ar, za ta shiga tattaunawa da shuwagabannin majalisa a ranar Alhamis.

Ya kuri'ar yanke kauna take aiki?

Theresa May

Asalin hoton, UK PARLIAMENT/JESSICA TAYLOR

Daga shugaba mai bincike a kan harkokin siyasa na BBC.

Karkashin dokar da take kayyade wa'adin mulki ta 2011, ana gudanar da babban zabe a Burtaniya duk bayan shekara biyar, zabe na gaba za'a yi shi ne a 2022.

Amma kuri'ar yanke kauna tana ba 'yan majalisa dama domin su tantance ko suna so gwamnati mai ci ta ci gaba da mulki ko a'a.

Idan mafi rinjayen 'yan majalisar suka amince da kuri'ar yanke kauna, za'a fara kirgar kwanaki 14 a kan gwamnati mai ci ta sauka.

Idan a wannan lokacin gwamnati mai ci ta kasa samun nasara a kan sabuwar kuri'ar da aka yi, za'a yi gaggawar yin sabon zabe.

Wannan zaben baza'a yi shi ba sai an kwashe a kalla kwanakin aiki 25.