Theresa May na gab da sanin makomarta

Asalin hoton, AFP/getty
'Yan Majalisar Burtaniya na shirin soma jefa kuri'ar da za ta tabbatar da goyon bayansu ga daftarin yarjejeniyar Theresa May na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai ko kuma akasin haka.
Zaben wanda ke da muhimmanci sosai, ya zo ne bayan kawo karshe kwanaki biyar da aka kwashe ana tabka muhawara a kan rabuwar kasar da Turai.
Misis May ta bukaci 'yan siyasa da su ba ta hadin-kai, wanda ta ce akasin haka tamkar ana gangancin jefa 'yan kasar a cikin hadari ne.
Ana ganin 'yan majalisa da dama za su hada kai da 'yan adawa wajen jefa kuri'ar kin amince da daftarin yarjejeniyar wanda ake saran zai fuskanci babban koma baya.
Sai dai kafin soma jefa kuri'ar, 'yan majalisar na da dama kawo shawarwari a kan abubuwa da suke ganin na bukatar gyara ko a sauya a cikin daftarin.
A kokarinta na karshe wajen ganin ta shawo kan 'yan majalisar musamman 'yan gaba-gaba wajen nuna adawa, firaminista Theresa May, ta roki goyon bayansu ga manufofinta, da ke kunshe a daftarin, da kuma makomar alakarsu ta siyasa a nan gaba.
Misis may ta ce ba abu ne mai sauki ba, amma nan gaba wadanda ake yi dominsu, za su dubi ko karanta litattafa tarihin, kuma abin da za su soma mayarda hankali shi ne shi ko an kare tattalin arzikin kasa da batun tsaro da kuma hadin-kai ko kuma an bar al'ummar kasar sun yi kasa a gwiwarsu.
Ko a wannan safiya ta talata firaministan na shirin gudanar da jawabi ga majalisar ministocinta, kafin a shiga muhawara.
Sai dai 'yan majalisa da dama musamman na jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya na ci gaba da dagewa a kan bakarsu da adawa da yarjejeniya.
Idan kuwa 'yan majalisar su ka yi watsi da wannan daftari, to wa'adin kwanaki 3 kawai za su bai wa Misis may ta sake gabatar da wani daftarin.










