Taron G7: Ana nuna wa juna yatsa tsakanin Johnson da Tusk kan ficewar Birtaniya daga EU

Boris Johnson da Donald Tusk za su tattauna kan Brexit a Faransa

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk da Firaministan Birtaniya Boris Johnson sun yi musayar kalamu game da wanda ke da laifi idan Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turai ba tare da wata yarjejeniya ba.

Mr Tusk ya ce tarihi ba zai manta da Boris Johnson ba matukar ya yi sagegeduwar da ta kai ga ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU ba tare da wata yarjejeniya ba.

Sai dai shi ma Firaminista Boris Johnson ya mayar da martani da cewa Donald Tusk ne za a fi tunawa matukar aka kasa cimma yarjejeniyar kafin ficewar Birtniya daga kungiyar.

Mutanen guda biyu dai za su yi wata ganawa ranar Lahadi a yayin da ake taron kasashe 7 masu karfin tattalin arziki na duniya a Faransa.

Amma a lokacin da ya yi jawabi bayan isar sa Faransa, Donald Tusk ya ce ba zai goyi bayan tsarin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ba tare da yarjejeniya ba.

Tun bayan da ya zama Firaminista, Boris Johnson ya sha nanata cewa babu makawa Birtaniya za ta fice daga a kungiyar a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2019.

Sai dai ya sha cewa zai fi son Birtaniyar ta fice daga kungiyar bayan cimma yarjejeniya.