'Masu so Birtaniya ta fita daga EU 'yan wuta ne'

Asalin hoton, Reuters
Shugaban kungiyar Tarrayar Turai Donald Tusk ya bayyana wadanda suke so Birtaniya ta fita daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin '''yan wuta.''
Ya bayyana haka ne bayan tattaunawar su da Ministan Ireland Leo Varadkar a Brussels.
Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar Ireland a bude ko da kuwa akwai batun ficewar Birtaniya domin a samu zaman lafiya.
Amma Mista Tusk da kuma Mista Varadkhar suna da shirin ko ta kwana a kan batun ficewar Birtaniya daga Tarrayar Turai.
'Yan majalisar dokoki a Birtaniya kamar irin su Andrea Leadsom tuni suka fara mayar da martani a kan irin wadannan kalamai na Mista Tusk.
Misis Leadsom, wadda tana daya daga cikin wadanda suka yi ta kiraye-kirayen ficewar Birtaniyan, ta bayyana kalaman nasa a matsayin ''kalaman da na sani'' kuma ''kalaman da ba za su taimaka ba.''
'Yar majalisar, wadda kuma 'yar jami'iyyar Conservative ce ta shaida wa BBC cewa ''ba shi da da'a.''
A kwanakin baya ne dai 'yan majalisar Birtaniya suka fitar da wasu sabbin shawarwari domin sauya makomar kasar a kan batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai wato Brexit.











