Boris Johnson: Rufe majalisar Birtaniya ya haifar da martani mai zafi

Asalin hoton, AFP
Matakin da Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya dauka na dakatar da zaman majalisar kasar ya fusata 'yan majalisar da ma masu adawa da shirinsa na janye Birtaniya daga Tarayyar Turai babu yarjejeniya.
Matakin ya janyo zanga-zanga a fadin kasar, har wasu sun shigar da kara a kotu ban da matakin da wasu mutum miliyan daya suka dauka na rattaba hannu kan wata takarda koke.
Gwamnatin da Mista Johnson ke jagoranta ta ce hutun mako biyar da majalisar za ta yi a watan Satumba da Oktoba zai ba ta damar sake duba batun Brexit na ficewarta daga Tarayyar Turai.
Amma masu adawa da gwamnatin na cewa matakin da ta dauka ba na demokradiyya ba ne kuma ta fito karara cewa ana son hana majalisar yin aikinta ne.

Asalin hoton, EPA
Daya daga cikin ministocin gwamnatin, Michael Gove ya sanar da BBC cewa tura keyar 'yan majalisar hutu, wanda Sarauniyar Ingila ta yi a jiya Laraba, ba matakin ne na siyasa ba.
Ya kuma ce ba an dauki matakin ba ne domin Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai ba tare da kulla wata yarjejeniya ba.
Ministan ya kuma ce akwai isasshen lokacin duba dukkan batutuwan da suka shafi Brexit kafin ranar 31 ga watan Oktoba.
Firai minista Johnson ya ce Sarauniyar Ingila za ta yi wani jawabi na musamman ranar 14 ga watan Oktoba, daf da dawowar majalisar daga hutun na dole.
Amma jagoran jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya bayyana matakin da cewa yayi kama da fashi da aka yi wa kasar saboda hana majalisar kare muradun Birtaniya, kuma ya lashi takobin dakatar da matakin.
Mista Johnson ya ce ba ya son ficewar kasar daga Tarayyar Turai ba tare da an kulla yarjejeniya ba, amma ya ce idan hakan ya zama dole, zai janye kasar babu bata lokaci.

Yadda jama'a suka fito domin nuna rashin ji dadinsu
A ymmacin Laraba masu zanga-zanga sun hallara a gaban majalisar Ingila da ke Westminster, inda suka rika yin kira da a hana abin da suka kira juyin mulki.
Masu zanga-zangar na dauke da tutocin Tarayyar Turai da na Birtaniya.
Yawancin masu nuna fushin nasu sun nuna aniyarsu da cewa wannan ne matakin farko na zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin Mista Johnson.
Sun kuma ce za a ci gaba da wasu taruruka irin wadannan a karshen mako mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Kawo yanzu, mutum fiye da miliyan daya ne suka sanya hannu kan wata takardar nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin Birtaniyar.
Kuma an cimma wannan alkaluman ne a kasa da yini guda kawai.











