Amurka ta taya Buhari murnar lashe zaben 2019

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnan sake lashe zaben 2019.
A wata sanarwa mai dauke sa hannun Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ta yaba wa 'yan Najeriya kan yadda suka fito suka kada kuri'unsu."
"Muna sane da rahoton masu sanya ido na kasashen waje wadanda suka bayyana cewa zaben an yi shi cikin 'yanci da adalci duk da cewa an dan samu tashe-tashen hankula nan da can."
"Muna taya sauran 'yan takarar da su ma suka fafata a zaben murna musamman yadda aka yi zaben cikin lumana."
Haka kuma, sanarwar ta bukaci 'yan kasar da su "tabbata sun yi sauran zabuka a mako mai zuwa cikin nasara," in ji Mista Pompeo.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Amurka ta ce a shirye take wajen gannin ta yi aiki da Najeriya don samar da zaman lafiya da ci gaba tsakanin kasashen biyu.
A ranar Larabe ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Ita ma kasar Faransa ta bi sahun Amurkan, inda ta taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben a ranar Alhamis.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hakazalika Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz shi ma ya aike wa shugaban da irin wannan sako.
Shugaban mai shekara 76, na jam'iyyar APC, ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.
Sai dai Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben kuma ya ce zai kalubalance shi a kotu.











