Abubuwa biyar da suka sa Buhari ya doke Atiku

Asalin hoton, Presidency
- Marubuci, Naziru Mikailu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu kan Atiku Abubakar ta zo wa wasu da mamaki, yayin da wasu kuma ta zo daidai da hasashen da suka yi tun farko, sai dai ganin yadda yakin neman zaben ya yi zafi musamman a yankin Arewacin kasar, inda 'yan takarar biyu suka fito, an zaci fafatawar za ta fi haka zafi a gaban akwatu.
Sai dai daga bisani Buhari ya yi nasara da gagarumin rinjaye, inda ya ba da tazarar kusan kuri'a miliyan hudu.
Ga dalilai biyar da suka sa shugaban mai shekara 76, ya yi nasara kan tsohon aminin siyasar tasa, wanda ya taimaka masa wurin samun nasara a 2015.

Rashin alkiblar jam'iyyar PDP
Ganin yadda jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben 2015 bayan shafe shekara 16 a kan karagar mulki, an yi zaton cewa za ta kimtsa tare da hada kanta da yin nazari kan matsalolin da ta fuskanta.
Amma kuma sai akasin haka ya faru, inda wasu manyan 'ya'yanta da wadanda suka amfana da mulkinta suka ja baya, suka bar ragamar a hannun baki irinsu Ali Modou Sharif, abin da ya jefa ta cikin rudani.
Ba su farga ba sai dab da zaben na bana. Hakan kuma a cewar Dr Suleiman A Suleiman na Jami'ar Amurka da ke Yola (AUN), ya sa sun rasa wata takamaimiyar alkibla, kuma sun yi kamfe maras armashi da kai-da-gindi.
"Manufa da tsarin yakin neman zabensu bai sauya ba daga na 2015, wannan shi ne ya sa nasararsu ta kasance ne kawai a mafi yawan jihohin da suka lashe a zaben da ya gabata, ban da wasu 'yan kadan".
Ya kara da cewa masu kada kuri'a da dama "na yi wa jam'iyyar kallon ta 'yan jari-hujja, kuma duk da cewa ba lallai ba ne hakan ya zama gaskiya, hasashe da shaci-fadi a siyasa yana da tasiri".

Asalin hoton, Getty Images
A fahimtarsa wajibi ne jam'iyyar ta "sauya taku, da manufa da tsari" domin sake sayar da kanta ga 'yan Najeriya idan tana so ta sake lashe zabe a kasar, abin da ya ce "ba su yi ba a wannan zaben".
Haka kuma shi ma Atikun bai fito da wata fayyatacciyar manufa ba ga yankin Arewa duk da cewa nan ne matattarar magoya bayan Buhari, kuma masana da daman a ganin wajibi ne duk mai son yakarsa ya kassara shi a yankin.
Amma duk da haka PDP ba ta fito da wata manufa ta musamman ga yankin ba, kamar farfado da masana'antu ko kawar da matsalar rashin ayyukan yi.
Ganin yadda jama'a suke matukar son Muhammadu Buhari a wannan yanki, kamata ya yi a ce PDP ta mayar da hankali sosai kan yankin musamman ganin yadda shi ma Atiku daga nan ya fito. Amma ba ta yi hakan ba.

'Yan Arewa sun masa halacci
Wani abu mafi muhimmanci da za a iya cewa ya taka rawa a nasarar Shugaba Buhari shi ne kyakkyawar alaka da kaunar da take tsakanin shugaban da magoya bayansa duk da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta a shekara hudun da ya shafe a kan mulki.

Masoyansa sun tsaya kam a bayansa a zaben 2019 kamar yadda suka saba yi masa tun shekarar 2003.
Mafi yawan kuri'un da ya samu sun fiuto ne daga yankin Arewa maso Yamma da maso Gabas, inda kuma a nan ne Atiku Abubakar ya sha mummuna kaye, kuma anan ne ya rasa damarsa ta karshe ta zama shugaban kasa.
A cewar Dr Suleiman, wannan ya nuna cewa har yanzu suna fatan zai yi musu abin arziki duk da gazawar da wasu ke ganin ya yi kawo yanzu.
"Na tattauna da jama'a a sasan Arewacin Najeriya da dama a shekara biyu da ta gabata, kuma na fahimci cewa suna da yakinin zai taka rawar da ta fi ta baya, adon haka suka sake bashi kuri'unsu".
Tasirin zaben 2023
Batun yankin da zai karbi ragamar shugabancin kasar a zabe na gaba idan Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu na daga cikin abubuwan da suka taka rawa wurin samun nasararsa.
Tsarin zaben kasar dai ya dogara ne kan karba-karba tsakanin Kudu da Arewa.
Kuma abokanan huldarsa na siyasa da suka kafa jam'iyyar APC tare na Kudu maso Yamma na da yakinin cewa su zai mika wa idan ya kammala wa'adinsa.
Wannan ta sa sun fito sun sake zabarsa kamar yadda suka yi a baya, duk da cewa ya sha kaye a jihohin Oyo da Ondo, wanda ya lashe a 2015.

Asalin hoton, Getty Images
Ba ya ga kuri'a, sun tallafa da kudade da basirar da Allah ya hore musu wurin shirya yakin neman zabe da dabarun siyasa.
Sai dai masu sharhi irinsu Dr Suleiman na ganin za a iya kai ruwa-rana idan aka zo batun fitar da dan takara a zaben na 2023.

'Yan jam'iyyarsa na Kudu sun yi ta maza
Wani abu da ya bayar da mamaki a zaben shi ne karin kuri'un da shugaban ya samu a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da ma tsakiyar Najeriya - adadin da bai taba samun irinsa ba a tarihin siyasarsa.
Ya samu kashi 25 cikin dari ko fiye da haka na kuri'un da aka kada a jihohin Abia, Ebonyi, Bayelsa, Delta, Akwa Ibom, abin da ba wai kawai ya kara adadin kuri'unsa ba ne, har ma da fadada tasirinsa.
Duk da cewa wasu na ganin hakan na da alaka da karfin gwamnati, dole a jinjinawa jami'an da ke mukami a gwamnatinsa, da kuma wasu 'yan jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC irinsu Godswill Akpabio, Orji Uzor Kalu da kuma Emmanuel Uduaghan.
Wannan da kuma rabuwar kan al'ummar Igbo sun taimaka wuirn sauya mummunan kallon da ake yi masa a wadannan yankunan, kuma babu shakka hakan ya yi tasiri a zaben.
Sakon yaki da cin hanci
Wani abu da ake ganin ya taka rawa wurin sake zaben Shugaba Buhari shi ne sakon ya nuna cewa na yaki da cin hanci da rashawa, wanda kuma yana tasiri a zukatan talakawa, duk da cewa wasu na ganin babu wata gagarumar nasara da ya cimma a fannin.

Asalin hoton, Getty Images
Jama'a na yi masa kallon mutumin da yake fafutuka domin su, kuma wanda za su iya amince wa kan amanarsu.
Ba ya ga arewacin Najeriya, sakon yana kuma tasiri a wasu sassan kasar.
Sannan kuma yana da 'yan-baka - masu tallata sabgoginsa a shafukan sada zumunta da ma kafafen yada labarai na gargajiya.
Da kuma wannan batu na cin hanci suka yi amfani wurin bata Atiku Abubakar da kuma jam'iyyarsa ta PDP.












