Yadda ake gwagwarmaya wajen karɓo mutanen da ƴan bindiga suka sace

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ƴan bindiga sukan sace mutane don neman kuɗin fansa, baya ga tashin hankali da iyalai da ƴan uwa da abokan arziƙi kan shiga a sakamakon hakan, wata gagarumar matsala da akan fuskanta ita ce, irin yadda za a yi a karɓo mutanen da aka sace.

Wannan lamari galibi yakan haɗa da biyan maƙudan kuɗaɗe, da samar da wasu abubuwa da ƴan bindigan kan gindaya a matsayin sharaɗi, kafin su sako waɗanda suka kama.

Wani wanda aka sace ƴaƴansa biyu tare da wasu mutane goma sha bakwai a garin Runka na yankin ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina, ya bayyana wa BBC yadda aka karɓo mutanen a dajin na Runka, inda ya ce bayan biyan zunzurutun kuɗin, sai da ƴan bindigan suka buƙaci a haɗa masu da babura kafin suka yarda suka sako mutanen.

''Gaskiyar magana ita ce kuɗi aka biya, da babura guda biyu da wani nau'in babur da ake kira 'Boko Haram' guda ɗaya, wanda farashinsa ya wuce Naira miliyan biyu, sai ma da muka sha wahala kafin muka sami wannan babur ɗin domin kamar an hana sayar da shi ne baki ɗaya a wannan yankin,'' in ji shi .

Ya kuma ƙara da cewa sun kashe sama da Naira miliyan ashirin kafin suka karɓo mutanensu.

Ya ce: ''Gaba ɗaya mun biya zunzurutun kuɗi Naira miliyan 22. inda da farko muka kai miliyan 10, muka zo muka ƙara bayar da miliyan 10 kuma daga baya muka sake kai miliyan biyu tare da wannan babur ɗin da suka buƙaci mu kai tun daga farko.''

Ya yi bayanin cewa bayan cika duka sharuɗɗan da ƴan bindigan suka gindaya sai da aka ci gaba da aka yi ta taƙaddama kafin suka amince suka saki mutanen da suke riƙe da su.

Ya bayyana cewa mutanen sun shiga wani irin mummunan yanayi sakamakon zamansu a hannun ƴan bindigan, ''Ba za ka taɓa tunanin cewa ɗan'Adam ne ya riƙe waɗannan mutanen ba, duk bala'in duniya da ka sani waɗannan mutane sun shiga cikin shi. Babu wanka, ga gashi kamar an fito da mutum daga rami ga matsalolin rashin lafiya, ban da kuma mummunan tashin hankali da suka shiga, '' in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa sun yi nasarar karɓo mutum 19, waɗanda suka haɗa da matan aure guda biyu da ƴan mata guda shida da ƙananan yara guda biyar da kuma matasa shida, wanda dukkansu sun yi kwana 84 a hannun ƴan bindigan.

Ya yi bayanin cewa an kai harin ne a garin Runka a ranar 7 ga watan yulin wannan shekarar inda ya ce ƴan bindigan sun sace matarsa da kuma ƙananan yaransa guda biyu. Kuma a halin yanzu waɗanda aka karɓo suna asibiti ana kula da su.

Matsalar rashin tsaro dai ta yi matuƙar ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya kuma duk da nasarorin da jami'an tsaro suke cewa suna samu wurin kawar da manyan ƴan bindiga har yanzu mazauna wannan yankin ba su kasance cikin kwanciyar hankali ba sakamakon hare haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa a yankunansu.