Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kawar da manyan ƴan bindiga zai yi tasiri a harkar tsaron Najeriya?
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa wasu jerin tsararrun samame da dakarunta ke kaiwa a baya bayan nan, sun karkashe gaggan shugabannin ƴan bindiga, waɗanda ke jagorantar munanan hare-hare a garuruwa da dama a sassan yankin arewacin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa matakan da jami'an tsaron ke ɗauka cikin ƴan makwannin nan, sun yi nasarar halaka kimanin gaggan shugabannin ƴan bindiga 15 da suka addabi jama'a da sata don neman biyan kudin fansa, da miyagun hare-hare a jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina.
Sai dai kuma wata tambaya da ke faman waɗari yanzu, ita ce ko ire-iren waɗannan nasarori za su kai ga samar da mafita mai ɗorewa game da matsalar ta tsaro?
Tasirin kashe ƙasurguman ƴan bindiga
Tun bayan kisan da dakarun sojin Najeriya suka yi wa Kacalla Halilu Sububu, a ƴan kwanakin nan an kashe jagororin ƴan bindiga da suka haɗa da Ɗan Gora, da Sani Bulak da Kacalla Makori da Lawwali Gemu a jihar Zamfara.
Kuma Mannir Sani Fura-Girke, wani ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf kan harkokin tsaro, ya ce lissafin gaggan shugabannin ƴan bindigan da aka kashe bai tsaya a nan ba inda a cewarsa kafin waɗannan jerin ƴan bindigan da aka hallaka dakarun sun yi nasarar kawar da wasu da dama, da suka haɗa da Ali Kawaje wanda ake alaƙanta shi da addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
‘‘An kashe ƴan bindiga irinsu Sani Ɗangote wanda ke jagorantar hare-hare a yankunan jihar Katsina. Akwai kuma wasu manyan ɓarayin dajin da ba su yi suna ba da aka yi nasarar kashe wa a wannan yankin.’’ In ji shi
Mannir Sani Fura-Girke ya ƙara da cewa kisan shugabannin ƴan bindigan yana yin tasiri a lamarin tsaro a yankin.
Ya ce: ‘‘Wannan ba ƙaramar nasara ba ce domin duk wani kachalla yana da yara aƙalla 100 a ƙarƙashin ikonsa kuma shi ne ya san duk wasu abubuwan da suka shafi hare-haren da ake kaiwa da suka haɗa da safarar makamai, da samun bayanan sirri da sauransu, saboda haka daga an kashe shi sai ka ga dabar tasa ta mutu.’’
Akasari masana harkar tsaro kamar su Navy Captain Umar Abubakar Bakori mai ritaya, shugaban ƙungiyar Vigilante na ƙasa baki na Najeriya baki ɗaya na ganin akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wurin karfafa wa al’ummar yankunan da abin ya shafa gwiwa wurin bayar da bayanan sirri da za su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro a yaƙin da su ke yi da ƴan bindigar.
Ya ce: ''Waɗanda ke bai wa ƴan bindigan nan bayanai talauci ne ya ingiza su, za ka ga abin da ake bai wa mutum ba ya wuce naira 5,000 ko 10,000 amma zai bayar da sirrin da za a kashe maƙwabcinsa. Ya kamata gwamnati ta tabbata ta taimaka masu domin suma su taimaki kansu.''
Galibi dai ana ganin matakan murƙushe shugabannin ƴan bindigan da ake bi, wata alama ce ta gano bakin zaren, a ƙoƙarin magance matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.