Yadda sojoji suka kashe babban ɗanbindiga Halilu Sububu

Lokacin karatu: Minti 3

Baya ga nasarar kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Halilu Sububu da rundunar sojin Najeriya ta yi, akwai kuma wasu abokan aikinsa da ta ce ta kashe su tare amma kuma ba a bayyana sunayensu ba.

Bayannan da BBC ta tattara sun nuna cewa ko a ranar da aka kashe shi yana kan hanyarsa ta komawa daga sulhunta dabobin ƴanbindigar da suke rikici a tsakaninsu.

Kafin a kashe shi ya fitar da wani bidiyo, inda a ciki yake cewa su daina kashe kansu, su haɗa kai su fuskanci waɗanda suke faɗa da su.

Masana na cewa Sububu babban jagora ne a fagen sata da kuma kashe-kashen mutane, kuma shi ne mai gidan Bello Turji.

Tuni rundunar sojin ƙasar ta ce za ta ƙaddamar da wani aikin soja na musamman da ta yi wa laƙabi da "Fansar Yamma" da zimmar zaƙulowa da kuma kashe sauran 'yanbindigar da ke damun arewa maso yammacin Najeriya.

'Jagororin da aka kashe na da yara sama da 200 kowanne'

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar game da kisan Halilu ta ce dakaru sun kashe shi ne tare da wasu mutum 30 a lokacin.

Mannir Sani Furagirke ɗanjarida ne mai bincike kan ayyukan 'yanfashin daji kuma ya shaida wa BBC cewa an kashe ƴanbindiga sama da 50 tun daga lokacin.

"Daga cikinsu akwai fitattun jagorori waɗanda kowannensu na da yara aƙalla 200," a cewarsa.

Da aka tambaye shi kan ko ta yaya suka gane hakan, sai ya ce: “Daga baya ne aka yi bincike kuma aka gane waɗannan, kasancewar ana ta yaɗa hotunansu da bidiyo da an gani ake ganewa."

'Yan kwanaki bayan kisan Sububu ne kuma wasu rahotonni suka ce dakarun sun kashe Kacalla Ɓaleri, amma ɗanjaridar ya ce ba Ɓalerin da aka sani ba ne aka kashe. Wanda aka kashe sunansa Ɗan-Ɓaleri, in ji shi.

Furagirke ya bayyana sunayen sauran jagorori (Kacalloli) manya da aka kashe bayan Halilu Sububu kamar haka:

  • Kacalla Ɗan Baleri: Dabarsa na Sabon Mashekari da ke ƙauyen Batauna a ƙaramar hukumar Shinkafi
  • Kacalla Dogo Kwaɗɗi: Dabarsa na kusa da ƙaramar hukumar Isa
  • Lawalli Dodo: Dabarsa na ƙauyen Filinga a ƙaramar hukumar Shinkafi
  • Kacalla Naguru: Dabarsa na fFlinga a ƙaramar hukumar Shinkafi
  • Kacalla Ɗan-Babirki: Dabarsa na Fankama kusa da ƙauyen Rudunu a ƙaramar hukumar Maradun
  • Kacalla Hana-Zuwa: Dabarsa na Jajjaye a yankin Tubali a ƙaramar hukumar Shinkafi
  • Kacalla Adamu: Dabarsa na ƙaramar hukumar Maradun

Rikicin cikin gida na ƙamari a tsakanin ƴanbindiga

A wani lamarin kuma, rahotanni na cewa rikicin gida na ta ƙara ta’azzara tsakanin ƴanbindigar, abin da ya sa suke ta kashe kansu.

Furagirke ya ce ko a ranar Talata ma an samu rikici tsakaninsu.

“Yalo Mai Bille ya kashe Kacalla Zakiru a ƙauyen Ɗan Dundun da ke yankin Gimi a ƙaramar hukumar Maru da wani yaronsa, sannan ya jagoranci kashe Kacalla Ɗan Mai Suga a wajen," kamar yadda ya bayyana.

"Rikici ne da ya shafe wata uku ana yi. Yalo ne ya kashe Kacalla Nagala wanda mai gidan Zakiru ne kafin ya ware. Zakiru yana neman fansa ne, amma shi ma ya kashe shi ya kuma kwashe dabbobinsa da dukiyarsa."

Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za su ci gaba da bayar da gudunmuwa domin tabbatar da tsaro.

“Sai dai mu ce Alhamdulillahi domin tun bayan kashe Halilu Sububu Allah ya amsa addu’o’inmu, ana kashe manyan ƴanbindiga. Gaskiya ana samun nasarori masu yawan gaske domin ko ba komai Sububu ne shugaba, ko sauran waɗanda suka yi suna irin su Turji duk yaransa ne," in ji shi.

“Shi ma kansa Turji yana ta guje-guje ne yanzu, sannan sauran ƴanbindigar sun shiga taitayinsu.”

A game yadda aka daɗe ana fara yaƙin sai kuma a koma gidan jiya, Bala Idris ya ce wannan karon ba irin yadda aka saba ba ne a lokutan baya.

“Gwamnan Zamfara a shirye yake ya bayar da dukkan gudunmuwar da ake buƙata domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.”

Shi ma ɗanjarida Furegirke ya ce rikicin cikin gida zai yi tasiri matuƙa wajen rage ƙarfin harkar.

“Idan aka ci gaba da wannan rigimar, ƙarfinsu zai ƙare kuma zai yi sauƙi wajen yaƙarsu saboda tun yanzu suna ta kashe junansu.”