Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu sojojin Najeriya ke tura koke ta shafukan sada zumunta?
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Kafin ɓullar ƙungiyar Boko Haram a 2009, da wuya ka ji koke-koken ƙarancin walwala ko kayan aiki daga sojojin Najeriya, yanzu kuma lamarin na ƙara ta'azzara ne saboda matsalar ƴanfashin daji da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Tun bayan fara yaƙin na Boko Haram a jihohin arewa maso gabashin ƙasar ne kuma aka fara samun wasu sojoji na fitowa kafofin yaɗa labarai suna ƙorafi kan rashin kulawa da su a fagen yaƙi.
A baya, da dama daga cikin masu ƙorafin suna yi ne a ɓoye, daga baya kuma wasu suka koma yi a shafukan sada zumunta.
Duk da cewa hukumomi a Najeriya na bayyana cewa sojojin ƙasar na samun nasara a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap, ƴanfashin da suka fi addabar jihohin arewa maso yamma na cigaba da kashewa da kuma sace mutane kusan a kowace rana.
A ƙarshen makon da ya gabata ne wani bidiyo ya fara yawo a shafukan zumunta, inda aka ga wani wani mutum da ya yi iƙirarin shi sojan Najeriya ne yana zargin shugabannin ƙasar da cin gajiyar matsalar tsaron da ake fuskanta.
Ɗaya daga cikin mai magana da yawun sojin Najeriyar ya faɗa wa BBC cewa suna tantamar ko sojan gaskiya ne ko kuma a'a, amma suna bincikawa.
Sai dai abin da ya bambanta nasa ƙorafin da na baya shi ne yadda ya ɗora wa shugabanninsu na soja da kuma gwamnati laifi kacokan na gazawa wajen kawo ƙarshen ƴanbindigar amma kuma ya kauce wa magana kan walwala ko rashin kayan aiki da aka saba ji.
"Ku daina ganin laifin yaran sojojin Najeriya, mu aiki muke yi da oda [umarni]," in ji shi. "Da a ce shugabanninmu za su ce mu shiga dajin mu yaƙe su, wallahi sati ɗaya mun gama da su."
Kalaman mutumin sun yi daidai da irin zarge-zargen da wani ɓangare na al'umma ke yi kan cewa 'akwai sakaci a wani ɓangaren' shi ya sa aka kasa kawar da matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaure wa ƴan Najeriya kai shi ne yadda akan ga wasu masu bayyana kansu a matsayin ƴanfashin daji riƙe da bindiga, kai-tsaye a shafukan sada zumunta, suna alfahari.
Hakan ta sa wasu kan yi zargin kamar jami'an tsaro na sane suke ƙin ɗaukar mataki a kansu, duk da cewa gwamnatin da jami'an tsaro kan ce suna bakin ƙoƙarinsu.
A farkon shekarar nan ma an ga wani soja ɗauke da jakarsa a wani wuri da aka yi iƙirarin cewa jihar Borno ne yana kokawa kan yadda ya kasa biyan kuɗin motar zuwa gida bayan shafe shekara yana fagen yaƙi da Boko Haram.
"Da na je tasha sai aka ce mani kuɗin mota zuwa gida naira 35,000 ne. Da na lissafa sai na ga zuwa da dawowa ya kama 70,000 ke nan. Ni kuma albashina na wannan watan 50,000 ne. Shi ya sa zan koma daji kawai saboda ba ni da wani zaɓi yanzu," kamar yadda aka ji shi yana faɗa a bidiyon.
Kazalika, ana iya tuna bidiyon Birgediya Janar Olusegun Adeniyi, kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaƙi da Boko Haram, inda aka gan shi kewaye da sojoji yana ƙorafin rashin kayan aiki a wurin da suka fafata da masu tayar da ƙayar baya.
Sai dai wannan hafsa ne kuma kwamandan da ke fagen daga.
Cikin bidiyon da aka wallafa a watan Maris na 2020, an ji janar ɗin na cewa: "Yallaɓai, kamar yadda kake gani dakarunmu sun ji raunuka amma ba mu fasa yaƙar ƴanta'adda ba. Sun kawo mana hari da motoci masu ɗuke da bindiga kusan 15 daga kowane ɓangare.
"Saboda haka lissafin da aka yi na yanayin wurin nan ba daidai ba ne...Ka ga yadda tayoyin motarmu suka farfashe saboda harsasai, mun sauya tayoyi da yawa, ga dakaru suna ƙoƙarinsu amma babu kayan aiki."
Jim kaɗan da faruwar hakan rundunar sojin Najeriya ta cire shi daga kwamandan rundunar kuma aka mayar da shi Abuja. Zuwa watan Disamban shekarar kuma kotun soja ta yanke hukuncin rage masa muƙami da shekara uku bisa kama shi da laifin saɓa dokokin amfani da shafukan sada zumunta na rundunar.
Me ya sa ƙananan sojoji ke aikata hakan?
Manjo Bashir Shuaibu Galma MNI mai ritaya na ganin ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ƙananan jami'an tsaro yin irin wannan ƙorafi a bainar jama'a shi ne rashin kyautawar shugabanni.
"Amma kuma akasarin irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe a shafukan zumunta ba su fiya wani tasiri ba, har sai fa idan ƙorafe-ƙorafen sun yi yawa," in ji shi.
Shi ma Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya), wanda tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya ne, yana ganin ɗayan abubuwa biyu ne ke jawo ƙananan sojoji yin hakan.
"Na sani akwai tsarin kai koke. Lokacin da nake aiki, babban hafsan soja kan zauna da dakaru tun daga kan masu anini har zuwa kan wanda ba shi da anini ko ɗaya domin ya ji ko akwai wani ƙorafi," kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Wannan tsari shi ake kira "durbar". To ina kyauta zaton ko dai aiki ne ya yi yawa a yanzu tsarin ba shi tafiya yadda ya dace, ko kuma ƙananan sojojin ne ba su san makamar aikinsu yadda ya kamata ba."
Manjo Galma ya ƙara da cewa duk wani ofisa - tun daga kanal zuwa janar - akwai tasirin ƴansiyasa wajen naɗa shi muƙami ko kuma ƙara masa girma.
"Shi ya sa ake samun cin karo ko kuma haɗin baki tsakanin shugabannin soja da kuma ƴansiyasa, wanda ke jawo muzguna wa ƙananan soja har ma su yi irin wannan ƙorafin."
Me dokar soja ta ce game da hakan?
Janar Kukasheka ya ce kamar sauran rundunonin soja, ita ma ta Najeriya na da dokokin amfani da shafukan sada zumunta.
"Sharaɗi ne cewa kada sojan da ke kan aiki ya saka hotonsa sanye da kaki a shafukan sada zumunta," a cewar tsohon janar ɗin.
An san rundunonin soja a faɗin duniya da dokoki da kuma tsari, sai dai Manjo Galma ya ce babu wata doka "mai tsauri" ko kuma "sabuwa" game da kafofin yaɗa labarai a aikin soja.
"Abin da dokar aiki kawai ta ce shi ne haramun ne wani soja da ke bakin aiki ya fitar da wani bayani ba, ko ya yi mu'amala da wani mai kama da wannan a wajen rundunar ba tare da ya samu izinin shugabansa ba," in ji shi.
"Wannan shi ya sa muke da sashen hulɗa da jama'a a ɓangarorin sojan sama, da na ruwa, da na ƙasa. Babu wanda zai yi magana sai da izini."
Janar Kuka Sheka ya ce soja ka iya neman izini domin yin amfani da shafinsa ta wata hanya daban amma da zimmar yaɗa labarai.