Rashin tsaro: Abin da ya sa gwamnatin Najeriya ta kasa maganin masu satar mutane

    • Marubuci, Halima Umar Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Matsalar rashin tsaro a wasu sassan arewacin Najeriya ita ce babban tashin hankalin da a yanzu haka mazauna yankin ƙasar ke ciki, idan ka ɗauke matsalar hauhawar farashin kayayyaki da ita ma ake fama da ita.

A wasu yankuna na jihohin yankin da dama kamar su Kaduna da Katsina da Naija da Zamfara da Sokoto, dubun-dubatar mutane ne ke barci ido a buɗe saboda tsoron ko dai a kawo musu harin da za a kashe su, ko a jikkata su, ko kuma a sace su tamkar kaji.

Al'ummar ƙasar da dama na dasa ayar tambaya kan me ya sa har yanzu gwamnati ta gaza shawo kan wannan "bala'i", babu isassun jami'an tsaro ne, ko kuwa kayan aikin tunkarar maharan ne suka yi ƙaranci?

Babu adadi na ainihi kan yawan jami'an tsaron Najeriya, saboda a kullum wasu suna ritaya yayin da wasu kuma ke mutuwa ko a fagen daga ko kuma ajali idan ya yi kira, da masu iya magana kan ce ko babu ciwo sai an tafi.

A rahotonsa na shekarar 2020, shafin Global Firepower mai tattara bayanai kan ƙarfin sojin ƙasashen duniya, ya sanya Najeriya a matsayi na 42 daga cikin ƙasashe 138 da suka fi ƙarfin soji.

Amma ƙiyasi ya nuna cewa akwai jami'an ƴan sanda 370,000 a ƙasar, da jami'an rundunar sojin ƙasa 310,900 da na rundunar sojin sama 18,000 da jami'an tsaro na Civil Defence 400, baya ga na wasu sassan tsaro daban-daban da ake da su a ƙasar.

Sai dai za a yi mamaki jin cewa duk da waɗannan dubban jami'ai, har yanzu ƙasar ta kasa magance matsalar satar mutane don kuɗin fansa da ta zama ruwan dare da kuma hare-haren ƴan bindiga a nan da can, baya ga matsalar rikicin Boko Haram da har yanzu ba a gama magance ta ba.

A wata tattaunawar sirri da BBC Hausa ta yi da wasu jami'an tsaro biyu a Najeriya, sun fayyace wasu abubuwa da ba kowa ne ya sani ba kan dalilin da ya sa ake samun koma-baya wajen magance waɗannan matsaloli.

Waɗannan jami'ai dai suna daga cikin waɗanda aka tura yankunan jihar Neja da yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna da Katsina da Zamfara. Mun ɓoye sunayen mutanen saboda tsaro.

"Babu haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro"

Wani jami'i a hukumar da ke kula da dazuzzukan da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayyar Najeriya, wata sabuwar hukuma da ake cewa Nigerian National Park Service, ya shaida wa BBC cewa akwai ɗumbin matsaloli da suka sa aka gaza murƙushe maharan.

Jami'in wanda aiki ya kai shi yankunan da matsalar ta fi ƙamari irinsu dajin Birnin Gwari da dajin yankin jihar Neja da ma na Katsina da Zamfara, ya ce jami'an tsaron da ke aiki na hukumomi daban-daban ba sa aiki tare da juna.

"Ya kamata jami'an tsaron da suke aiki a waɗannan yankuna da garkuwa da mutane ta yi ƙamari kamar jihar Kaduna da Katsina da Zamfara da Neja su yarda su yi aiki tsakaninsu da Allah.

"Akwai gyara sosai a salon yaƙin da muke yi.

"Ba ma aiki tare kwata-kwata, kowace runduna suna aikinsu ne daban-daban, sojojin sama na nasu daban, haka ma na sojin ƙasa, haka mu ma tamu rundunar, sannan ƴan sanda ma suna nasu aikin daban.

Ba a kai samame sai daƙile hari

Matsala ta biyu da wannan jami'i ya ambata ita ce batun rashin ƙwarin gwiwar jami'an tsaro ta kutsawa cikin daji inda maharan suke samun mafaka don far musu.

A ganinsa aikin da suke yi yawanci na daƙile hari ne maimakon kai samame maɓoyar masu satar mutanen da ƴan fashin.

"Ya kamata a ƙara yawan shiga daji wajen da maharan suke ɓuya domin kai musu hari ba sai an jira su sun fito hanya ba.

"A taƙaice dai kamar faɗan bayan fage muke yi maimakon zuwa fagen daga," in ji jami'in.

Wani abu da jami'in ya sake fito da shi fili shi ne batun rashin ba su irin tallafin da ya kamata.

Ya ce: "Muna buƙatar a dinga sa ido sosai a kan aikinmu tare da ba mu duk taimakon da ya dace a yayin da muke aikace-aikacenmu, wannan abu kuwa kamata ya yi a ce da gwamnati da ƴan siyasa da sarakunan gargajiya duk suna sa hannu a cikinsa.

Sannan ya ce akwai wata matsalar da ke ci musu tuwo a ƙwarya ta rashin samun bayanai daga al'ummomin da ke waɗannan yankuna.

"Harkar tsaro lamari ne da ya wanzu a kan kowa da kowa, ya kamata su ma fararen hula su dinga taimakawa da duk wasu bayanai da ba mu haɗin kai wajen sanar da mu shige da ficen al'ummar waɗannan yankuna.

Walwalar jami'an tsaro da tauye haƙƙinsu

Wani jami'in ɗan sanda da shi ma muka ɓoye sunansa saboda tsaro ya gaya mana irin abubuwan da suke jawo tarnaƙi wajen magance wannan masifa.

A ganinsa farkon duk abin da ke kawo koma-baya a wajen waɗannan ayyuka sh ine rashin kyautata walwalar jami'an tsaron da suke fuskantar masu garkuwa ko kuma duk wasu ƴan bindiga daɗi.

Ya ce: "Misali ko soja ko ƴan sanda za ka ga an ware kuɗin alawus na wani aiki kamar naira 10,000 a duk sati ga duk mutum daya.

"Suna da masaniyar an ware kuɗin da komai amma kafin kudin su zo hannunsu wancan ofisa ya yanka wancan ya yanka sai ka ga mutum da wuya ya tashi da naira 2,000 ko 3,000.

"Wannan a filin daga fa kenan, ga abinci da sauran kayan rayuwa ba su wadace su ba. Abu mafi muni kuma sai mutum ya rasa rayuwarsa.

"Kenan kowa na tafiya da zuciya biyu. Babu Wanda zai bayar da zuciyarsa ya yi yaƙi domin kare ƙasar da ba za ta kare mutuncin iyalansa ba idan babu shi," a cewar jami'in.

Ya koka matuƙa kan hakin ko in kula ɗin da jami'ai ke samun kansu ciki: "Sau da yawa jami'an da suka jikkata a filin daga su ke ɗaukar ɗawainiyar kawunansu, da wuya wasu ka ga an zo ko da dubiya daga manyan jami'ai.

"Abin da kawai suka iya su manyan shi ne su yi jawabi a ofis su yabi waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka ji rauni."Sau da yawa za ka ga mutum ya jikkata, gwamnatin jiha ko tarayya su bayar da gudunmawa domin kula da lafiyarsa sai wani ya cinye abin da aka bayar.

Rashin kishin ƙasa da muguntar manya

A ƙasashen duniya da suka ci gaba abu ne da kowa ya sani cewa jami'an tsaronsu suna da kishin ƙasarsu, suna iya bayar da rayuwarsu a kan ƙasar.

Sai dai jami'in ya ce: "Ban da a Najeriya, rashin kishi shi ne abu na farko da ke kawo tarnaƙi ga yaƙi da kowace irin matsala ta tsaro.

"Abu na biyu waccar matsalar da na faɗa ta watanda da kuɗaɗen ƙananan jami'an tsaro da ke filin daga. Hakan ya zama kasuwancin wasu daga cikin manyan.

"Idan ya zama kasuwanci kuwa ai ba za su so a bari ba, hakan ya sanya da kansu suke kawo cikas a ayyukan yadda za a ci gaba kullum ya zama ba a dawo zaman lafiya ba, don kar waɗancan kuɗaɗen da suke samu su yanke," in ji shi.

Ya bayar da misali da aikin riga-kafin Allurar Polio ta yadda wasu ba sa so a ce cutar ta mutu kwata-kwata don kar ya zama an daina samun waɗannan kuɗaɗen shirye-shiryen.

"Idan abun ya zama kasuwanci kenan dole a daɗe ana yi ba tare da an gama ba, waɗanda za su jagoranci abun ya zo ƙarshe su abin ke bai wa riba. Kuma kisa ba su ake kashewa ba, kullum ƙananan jami'ai suke rasa rayuwarsu.

Ƙarin labarai masu alaƙa

Mece ce mafita?

Masana tsaro da su kansu jami'an da ke fuskantar waɗannan al'amura sun bayar da wasu shawarwari ga gwamnati na shawo kan bala'in.

Barrister Bulama Bukarti, mai nazari ne a kan ta'addanci a nahiyar Afirka, wanda ya ce matsalar tsohuwa ce da ta samo asali daga sakaci da rashin adalci na shekaru masu yawa daga gwamnatoci.

Kazalika, Barista Bukarti ya ce za a iya magance matsalar idan gwamnati ta ɗauki wasu matakai na sha yanzu magani yanzu da kuma masu dogon zango, kamar:

  • Ƙara yawan jami'an tsaro a yankunan da matsalar ta shafa
  • Samar wa jami'an tsaro kayan aiki kamar bindigogi da jirage da kayan tattara bayanai da dukkan abin da suke buƙata
  • Lallai ne a magance talauci da rashin aikin yi da jahilci, kamar yadda Bukarti ya ce.

Su kuwa jami'an tsaron da muka yi hira da su sun bayar da matakan warware matsalar ne kamar haka:

  • Yawan sauya manyan jami'an tsaro masu jagorantar faɗa
  • Saurin sauya shugabannin rundunonin soji
  • Saurin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin cin amanar ƙasa, musamman yadda sojoji ke yin hukunci ga jami'ansu a lokacin mulkin soja
  • Sanya ido a kan haƙƙoƙin ƙananan jami'ai da walwalarsu da saurin biyan haƙƙoƙin waɗanda suka rasa rayuwarsu domin waɗanda ke raye su gani
  • Ɗaukar ɗawainiyar wanda ya jikkata a kowanne aiki da aka sami matsala.

A ƙarshe ɗaya daga cikin jami'an da ya ce: "Yanzu dubi labarin sace jami'an ƴan sanda da aka yi a kan hanyarsu ta zuwa aiki, amma sai iyalansu ne suka harhaɗa kuɗaɗen da za su karɓo su.

"Yanzu wane ne zai sadaukar da rayuwarsa ga tsaron waɗanda ba su san mutuncinsa ba?"