Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me kashe Halilu Sububu ke nufi a yaƙi da 'yanfashin daji a Najeriya?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Ana cigaba da tafka muhawara kan nasarar da jami’an tsaro suka ce suna samu a yaƙi da ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Tun bayan kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Halilu Sububu a jihar Zamfara ne jami’an tsaron ke bayyana shirinsu na babu gudu babu ja da baya har sai sun ga abin da zai ture wa Buzu naɗi.
Shi ma Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce tun bayan kashe fitaccen ɗanbindigar sauran ƴanfashin da jagororinsu - irin su Bello Turji - suka shiga "tsilla-tsilla".
A cewarsa, sauran ƴanbindigar ƙananan ƙwari ne idan aka kwatanta su da Halilu Sububu.
"Shi ya sa duk suka rikice ciki kuwa har da Turji,” in ji gwamnan a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ranar Litinin.
A ranar Alhamis da ta gabata ne jami’an tsaron Najeriya suka sanar da kashe Halilu Sububu a Kwaren Kirya da ke ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Sububu fitaccen ɗan bindiga ne da ya addabi garuruwan da suke maƙwabtaka da dajin Sumke na ƙaramar hukumar Anka. A watan Mayun da ya gabata ne hedikwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da nemansa ruwa a jallo, sannan ta ba da sanarwar kashe shi a watan Satumba.
Shi ma Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kashe Halilu Sububu babbar nasara ce, amma ya ƙara da cewa somin-taɓi ne.
Ya ce aikin soji da za su ƙaddamar mai taken ‘’Fansar Yamma’’ zai yi amfani wajen ganin bayan sauran ƴanbindiga irin su Bello Turji tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
'Akwai sauran rina a kaba'
Kasancewar wasu na zargin an daɗe ana tafka ruwa ƙasa na shanyewa musamman a harkokin tsaro a Najeriya, wasu na fargabar ko wannan nasarar za ta zama ɗambar kawo ƙarshen matsalar tsaro a Arewa.
BBC ta tuntuɓi Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited mai nazari kan harkokin tsaro a Afirka ta Yamma da yankin Sahel, wanda ya bayyana cewa akwai sauran rina a kaba.
A cewarsa, a tsarin yaƙi da ƴanbindiga ko ƴanta’adda musamman waɗanda suke da ƙungiyoyi, kashe shugabansu yakan yi tasiri ne idan an haɗa da wasu abubuwa kamar haka:
- "Tsarin ƙungiyar na shugabanci. Idan tsari ne na mulki, to za ka ga kashe shugaban bai cika tasiri ba saboda akwai wanda zai maye gurbinsa.
- "Tsarin da ƙungiyar ke bi wajen tafiyar da ayyukanta; misali ta tsayar da ayyukanta ne a matsayin gwagwarmaya ga al’ummarta ko kuwa?. 'Yan bindiga suna cewa saboda abin da Hausawa da sauran ƴan ƙasa ke yi wa Fulani ne ya sa suka ɗauki makamai. To a nan za a iya samun wani ya ci gaba daga inda aka tsaya.
- "Gwamnati ko hukuma wadda ta kashe shi, shin ta gabatar da dalilai waɗanda za su gamsar da ƴan ƙungiyar cewa ya yi laifi? Ma’ana an yi amfani da shari’a wadda za a nuna cewa lallai abin da yake yi laifi ne kuma an gamsar da al’ummar da yake wakilta? To idan sun gamsu, wataƙila za su yi nadama kuma za ka ga ba za a samu wanda zai maye gurbinsa ba.
- "Hana ƙungiyar samun makamai da sabbin mayaƙa, da hana su ikon zalintar al’umma. Idan suka fahimci an daƙile wannan damar, yana hana su samun wani shugabancin.
BBC ta yi wa Dokta Kabiru misali da kashe Buharin Daji a baya, masanin ya ce rashin amfani da matakan da ya zayyana ne suka sa bayan kashe shi, wasu ƙananan ƴanbindigar suka ware suka zama shugabanni.
“Har yanzu hukuma ba ta ɗauki matakai na nuna cewa waɗannan ayyuka da suke babu amfani ba, kuma ba za su ci wata riba ba," a cewarsa.
"Sannan idan ba a magance asalin matsalar ba - wato rashin zamantakewa mai kyau tsakanin Hausawa da Fulani da kuma matsaloli na neman damar hanyoyin kiwo ga Fulani, su kuma Hausawa na so saboda noma - akwai yiwuwar matsalar na iya cigaba da faruwa.”
Me ya kamata a yi?
Kabiru Adamu ya zayyana wasu matakai da yake tunanin idan an bi za a iya samun zaman lafiya, kamar haka:
- Gwamnatin Tarayya ta ƙara haɗa kai da jihohi domin fitar da tsari na magance wasu matsaloli, kamar talauci da sauyin yanayi da sauransu
- Daƙile ɗaukar makamai a hannun waɗanda bai kamata ba
- Tsaro na iyaka domin kula da shiga da fitar mutane da kayayyaki
- Hukunta mai laifi saboda zargin da Fulani ke yi cewa shari’a na zalintar su
"Idan ba a yi haka ba, kashe shugabannin ba zai yi wani tasiri ba," in ji shi.