Shugaban kasar da tasirin addini ya taimaka masa cin zaɓe

Mista Ruto

Asalin hoton, DP OFFICE

William Ruto, wanda ke shirin karbar rantsuwa a matsayin sabon shugaban ƙasar Kenya a ranar Talata, shi ne shugaban kasar na farko Kirista dan Ikilisiyar bishara.

Kuma ana ganin hakan zai sa ya bayar da fifiko sosai a kan addini, saboda addini ya taka muhimmiyar rawa wajen cin zaɓensa.

Ruto, mai shekara 55 ba ya shayin bayyana akidarsa ta addini a fili, kuma ba ya kame bakinsa a kan batutuwa irin su 'yancin masu neman jinsi ɗaya da zubar da ciki, wadanda duk ana ganin za su taso a lokacin mulkinsa.

Mista Ruto ya saba da karanto ayoyin Baibul da yin addu'a har ma da kuka a bainar jama'a.

A lokacin yaƙin neman zaɓe 'yan hamayya har lakabi suka yi masa da 'mukaddashin Yesu'' - abin da magoya bayansa nan da nan suka dauka.

Abu na farko da ya yi lokacin da Kotun Kolin ƙasar ta tabbatar da nasararsa a zaɓen watan da ya gabata shi ne ya durkusa guiwa kasa ya yi addu'a tare da mai dakinsa Rachel da sauran shugabanni da ke zauren kotun.

Mr Ruto da matarsa har coci suka gina a harabar gidansu da ke unguwar Karen a babban birnin Nairobi.

Wani jagoran Musulmi ma ya yi addu'a a harabar bayan hukuncin kotun, abin da ke nuna cewa duk da kasancewarsa mai bin addinin Kiristanci sau da kafa, Mista Ruto zai kasance shugaba ga mabiya kowane addini.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Al'ummar Kenya da ke bin addinai daban-daban na zaman lafiya da junansu, kuma sabon shugaban ya samu goyon bayan Musulmi da yawa.

Bishop David Oginde na cocin Evangelical Alliance ta Kenya ya ce yana fatan gwamnatin Mista Ruto za ta tsaya kai da fata kan mutunta dabi'u da al'adun kasar wadda ke martaba addini.

Kenya kasa ce ta mutane ke bin addini sau da kafa, domin hatta Babbar Mai Shari'a ta kasar Martha Koome ta danganta hukuncin Kotun Kolin da kasancewa wani hukunci na Ubangiji, mai makon hukuncin Kotun ita kanta.

A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, tasirinsa na addini a kan shugaban kasar mai barin-gado, Uhuru Kenyatta - wanda shi kuma ɗan darikar Katolika ne, ya nuna a wa'adin mulkinsu na farko, musamman a kokarin wanke sunansu a Kotun Hukunta Manyan Laifukata Duniya, kan zargin da aka yi musu game da tashin hankalkin da ya biyo bayan zaɓen 2007.

Mutanen biyu sun rika halartar cocin Ikilisiyar bishara wadda Mr Ruto ke bi inda suke addu'a da kuma neman goyon bayan jama'a a kokarin da suka rika yi na kaucewa gurfanar da su a gaban Kotun.

Abin da a karshe suka yi nasara a kai, inda masu gabatar da kara na Kotun suka bar tuhumar Mr Kenyatta a 2014, shi ma kuma Mr Ruto aka yi watsi da tuhumar tasa a 2016.

Kasancewar iyayensa mabiya darikar Furotesta ne, Mr Ruto ya kasance Kirista mai bishara inda har kafafen watsa labarai da jaridu na kasar suka riƙa wallafa hotunansa a lokacin ya na matashi mai wa'azi.

Matarsa ma takan shirya taron addu'a, kuma ta wani fannin ya ta'allaka nasarar da ya samu ga irin jajircewarta ga addini.

William Ruto's wife Rachel shares her husband's religious beliefs

Asalin hoton, Getty Images

Tsarinsa na amfani da addini wajen yaƙin neman zabe ya samu karfafuwa inda matar mataimakinsa Rigathi Gachagua wato Dorcas, wadda tsohuwar ma'aikaciyar banki ce da ta zama mai wa'azin Kirista.

Kusan kashi 85 cikin dari na al'ummar Kenya Kiristoci ne - daga ciki kashi 33 cikin dari 'yan darikar Furotesta ne, kashi 21 cikin dari mabiya Katolika ne, kashi 20 cikin dari masu bin ikilisiyar bishara ne, sai kuma kashi 7 cikin dari da ke bin darikun gargajiyar Afirka na.

Sai kuma kashi 11 cikin dari mabiya addinin Musulunci, kamar yadda sakamakon kidayar da aka yi a 2019 ya nuna.

Akwai kuma 'yan kasar kaɗan da ke bin wasu addinan yayin da 'yan kalilan masu bin akidar kin yarda da wanzuwar Ubangiji ne.

Mai fashin bakin siyasa Macharia Munene ya gaya wa BBC cewa karbuwar da Mista Ruto ya yi ga kusan dukkanin mabiya darikun Kirista daban-daban ta sa ya samu nasara a zaɓen.

Abokin hamayyarsa Raila Odinga ya yi katobara lokacin da ya ce addinin Kirista wata hanya ce da ake amfani da ita wajen karkatar da ra'ayin jama'a da kuma lokacin da matarsa ta furta cewa idan suka ci zaɓe za su dauki matakan sanya ido da takaita ayyukan coci-coci.

Mista Munene ya ce dukkanin wadannan abubuwa sun taimaka wa Mista Ruto a zaben.

Wani mai fashin baki kan harkokin siyasa Herman Manyora ya ce ba zai yi mamaki ba idan Mista Ruto ya naɗa shugabannin addinai a mukamai a gwamnatinsa domin su taka rawa wajen yakin neman zaɓe da nasararsa.

wasu Kiristoci na kwatanta gicciye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin 'yan Kenya masu bin addinin Kirista ne sau da kafa

Ana sa ran Mr Ruto ya dauki tsattsauran mataki a game da 'yancin masu neman jinsi ɗaya.

A shekara ta 2015 yayin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka na lokacin John Kerry, ke shirin ziyartar kasar, an ruwaito Mr Ruto yayin wani taron addu'a a coci a Nairobi yana cewa, ''Kenya kasa ce mai 'yancin kanta da ke bauta wa Ubangiji. Babu wuri ga dabi'ar neman jinsiu daya a Kenya.''

A yayin wata hira da tashar CNN bayan da ya ci zabe ya ce ba zai so ya yi wasu kalamai na ba gaira ba saba ba, amma ya kara da cewa, ''idan har batun masu neman jinsi daya ya zama wani abin magana a Kenya to zai bar wa jama'a su yi wa kansu zabi.''

Mr Manyora ya ce babban kalubale da gwamnatin za ta iya fuskanta shi ne idan aka bullo ta bangaren shari'a domin bai wa masu neman jinsi daya 'yanci.

A shekara ta 2019, Babbar Kotun Kasar ta yanke hukunci inda ta ki amincewa da yunkurin masu raji da ke neman tabbatar da matakin hana wa masu neman jinsi daya 'yanci. Amma duk da haka masu adawa da dabi'ar sun lashi takobin ci gaba da yakar dokar.

Haka kuma Mr Ruto ya yi fice wajen yaki da 'yancin zubar da ciki, inda da goyon bayan cocin ya tsaya sai dai idan har akwai hadari ga lafiyar mai juna biyun ne kawai za a yarda a zubar.

Wannan akida tasa ta kin yarda da 'yancin masu neman jinsi daya da kuma batun zubar da ciki ta sa yake da magoya baya da yawa daga cikin Musulmi.

Ya samu gagarumin goyon baya da tagomashi bayan zaben, lokacin da jam'iyyar United Democratic Movement (UDM) - wadda take da magoya baya Musulmi da yawa ta bar hadakar Mr Odinga ta mara baya ga jam'iyyar Mr Ruto, ta sa kawancen ya samu mafi yawan kujeru a majalisar dokokin kasar, bayan da aka kasa samun wanda ya yi nasara kai tsaye a zaben.

Sai dai Mr Manyora ya gargadi shugaban kan ya kiyaye da akidar Musulmi: Ya ce zai kwantar musu da hankali idan ya ja shugabanninsu a jika. To amma kuma muddin bai sassauta a kan akidarsa ta Kiristanci ba zai iya samun sabani da wasu Musulman.

Musulmi ne na biyo a mabiya addinai a Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmi ne na biyo a mabiya addinai a Kenya

Bishop Oginde ya ce idan dai har Mr Ruto zai nada shugabannin addini a mukamai a gwamnatinsa to dole ne dukkanin addinai su samu wakilci.

Ya ce, '' za mu mara masa baya da ba shi shawara inda za mu iya kuma ba shakka za mu yi masa addu'a.''

Limamin cocin ya kara da cewa, suna fatan zai yi shugabanci na gaskiya tsakaninsa da Allah.

Babban abin da ya sa ya yi nasara a zaben shi ne kusan yadda ya gabatar da kansa a matsayin talaka mai fafutuka, tare da yakar kokarin manyan gidajen siyasa biyu na kasar - gidan Odinga da kuma Kenyatta na dawwama a kan mulki.