Yadda mai sayar da kaji ya zama shugaban ƙasa

Daga Evelyne Musambi,

BBC News, Nairobi

Ruto

Asalin hoton, Getty Images

William Ruto - wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Kenya mai cike da ce-ce-ku-ce - rayuwarsa irin ta yawancin ƴaƴan talakawa ce a Kenya.

A lokacin da yake firamare, haka yake tafiya makaranta babu takalmi, har sai da ya kai shekara 15 sannan ya mallaki takalminsa na farko a duniya.

Sannan ya yi sana'ar sayar da kaji da gyaɗa a bakin titi a ƙauyensu da yake yankin Rift Valley.

Don haka ba abin mamaki ba ne don ya nuna kansa a matsayin gwarzon talakawa, a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasa na 9 ga watan Agusta.

Mr Ruto ya tsaya takarar ne a ƙarƙashin gamayyar jam'iyyar Kenya Kwanza, wacce ta yi alkawarin haɓaka tattalin arzikin Kenya.

Rashin aikin yi a tsakanin matasa masu shekara 18 zuwa 34 ya yi kusan kashi 40 cikin 100, kuma tattalin arzikin ba ya samar da isassun ayyukan da za su taimaka wa matasa 800,000 da ke neman aiki a kowace shekara.

Hakan ne ya sa ya ƙirƙiri wani take "Hustler nation" wato "Ƙasar matasa masu fafutuka", yana mai alaƙanta ta da matasan da ke ƙoƙarin samun na rufin asiri.

Mr Ruto ya yi alkawarin ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki daga ƙasa zuwa sama, yana mai cewa hakan zai amfani talakawa waɗanda su ne suka fi shiga tsanani na hauhawar farashin da ke addabar duniya sakamakon ɓarkewar annobar cutar korona da kuma yaƙin Ukraine.

Wannan ne karo na farko da Ruto mai shekara 55 ya tsaya takarar shugaban ƙasa, kuma ya bai wa masu sukarsa mamakin nasarar da ya yi - duk da cewa dai mafi yawan mambobin hukumar zaɓen sun yi watsi da sakamakon suna mai cewa cike yake da maguɗi.

Sai dai shugaban hukumar zaɓen Wafula Chebukati, ya ce zaɓen sahihi ne, inda ya ayyana Mr Ruto a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 50.5 na yawan ƙuri'un.

Ruto

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mr Ruto ya dinga jan hankalin mutane a wajen yaƙin neman zaɓe

Ya fara shiga harkokin siyasa a shekarar 1992, inda shugaban ƙasar a wancan lokacin Daniel arap Moi ya zame masa jagora.

Mr Ruto yana daga cikin matasa na gaba-gaba a jam'iyyar Mr Moi da take da tagomashi a lokacin, kuma yana daga cikin masu fafutukar da aka ɗorawa alhakin haɗa kan masu zaɓe a zaɓen jam'iyyu da dama da aka yi a karon farko a ƙasar a waccar shekarar.

Ya yi fice wajen iya tsara kalaman jawo hankalin jama'a a wuraren yaƙin neman zaɓe, kuma ya taka rawar gani a hirarrakin da ya dinga yi da ƴan jarida.

Ya kan fara jawabi ne da cewa "Abokina", abin da ke taimaka masa wajen ƙulla kyakkyawar alaƙa da masu kaɗa ƙuri'a da kuma rushe aƙidun masu suka.

Sauya sheƙa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan riƙe muƙaman minista a fannoni kamar na ilimi da ɓangaren noma - sai ya zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2013.

Mista Ruto ya tsaya takarar wannan zaɓen ne a lokacin da yake riƙe da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin, abin da ya bai wa ƴan Kenya da dama mamaki saboda yadda suke hamayya da juna a siyasance musamman a zaɓen da ya gabata.

Gamayyar Shugaba Kenyatta da William Ruto ta buƙata ce, saboda dukkansu Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta ICC tana tuhumarsu da laifukan cin zarafin bil adama, bayan zarginsu da hura wutar rikicin da ya jawo aka rushe zaɓen 2007, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,200.

A wancan zaɓen, Mista Ruto ya goyi bayan ɗan jam'iyyar hamayya Raila Odinga - wanda ya kayar a wannan karon - yayin da shi kuma Mista Kenyatta a lokacin ya goyi bayan Shugaba Mwai Kibaki a tazarcen da ya nema.

Kawancen da suka yi wanda aka yi masa lakabi da bromance, ya yi nasarar yadda suka kafa gwamnati har suka haɗa ƙarfin da suka ga bayan tuhumar da Kotun ICC ta yi musu, inda masu gabatar da ƙara suka haƙura da tuhumar da suke yi wa Shugaba Kenyatta a 2014, sannan shi ma Mista Ruto alkalai suka yi watsi da tuhumar da suka yi masa a 2016.

Kenyatta

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mr Kenyatta (daga dama) da Mr Ruto sun haɗa gamayya mai ƙarfi amma daga baya sun ɓata

Sai dai ƙawancen nasu ya kawo ƙarshe a shekarar 2018 lokacin da Mista Kenyatta - ya sake shiryawa da Mista Odinga, inda ya rusa fatan Mista Ruto na ganin shugaban ƙasar ya goyi bayansa a matsayin magaji a wannan karon.

Abokan shugaban ƙasar sun zargi Mista Ruto da rashin biyayya, zargin da ya musanta, amma ya yarda cewa akwai matsala tsakaninsu yana mai cewa "yadda yake kallon siyasa ya sha bamban da kallon da shugaban ƙasar ke mata."

Mista Ruto ya ci gaba da kasancewa mataimakin shugaban ƙasa, saboda dokokin kundin tsarin mulki.

A wannan zaɓen, Mr Kenyatta ya taya Mista Odinga yaƙin neman zaɓe sosai, yana mai cewa Mista Ruto ba shi da amana don haka bai cancanci zama shugaban ƙasa ba.

Mista Ruto ya mayar da martani, inda ya ce Mr Kenyatta na son Mista Odinga ya zama shugaban ƙasa ne don ya dinga juya shi son ransa.

A gaba ɗaya lokacin yaƙin neman zaɓen, ya dinga nuna kansa a matsayin mai faɗi tashi, yana mai yaƙi da abin da yake ganin ƙoƙarin mutanen biyu ƴan manyan gidaje da ke son su yi ta mulkar Kenya.

Mamallakin ƙatuwar gona

Goyon bayan da ƙabilun ƙasar suke bayarwa na taka rawa sosai a siyasar Kenya kuma Mista Ruto ya fito ne daga ƙabilar ƙasar ta uku mafi girma, Kalenjin, wacce sau daya kawai aka taɓa samun shugaban ƙasa daga cikinta, marigayi Mista Moi, wanda shi ne shugaban ƙasa mafi daɗewa a Kenya.

A yanzu ko shakka babu, shi ne jagoran al'ummarsa a siyasance.

Mr Ruto yana auren Rachael, wacce ya fara haɗuwa da ita a wani taron matasa a coci.

Suna da ƴaƴa shida. Babban ɗansu mai suna Nick, ya taɓa samun albarkar dattawan Kalenjin, lamarin da ya jawo kun ji-kun jin cewa ana shirin tsayar da shi wata takara ne, yayin da ƴarsa June, ke aiki da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar.

Kenya

Asalin hoton, Kenya Deputy President Office

Bayanan hoto, Mr Ruto ya raba wa matasa wulbaro don tabbatar da batunsa na cewa shi mai faɗi tashi ne

Mr Ruto yana ƙaunar harkokin noma don har yana noman masara da kiwon kaji da shanu.

Yana da wata tafkekiyar gona a yammacin Kenya da kuma gaɓar teku, sannan ya zuba jari sosai a harkokin yawon buɗe ido.

An alaƙanta Mista Ruto da laifukan cin hanci da rashawa a gwamnati, sannan ana yawan yaɗa jita-jita kan dukiyarsa.

A watan Yunin 2013, Babbar Kotu ta umarce shi da ya miƙa wata gona mai girman eka 100, sannan ya biya wani manomi da ya zarge shi da ƙwace masa gonarsa a lokacin rikicin bayan zaɓen shekarar 2007.

Ya yi watsi da aikata ba daidai ba, ya kuma roƙi masu zaɓe da su ba shi dama ya inganta rayuwarsu.