Zaben Kenya: Dalilin da ya sa manoma ke son dan takara mai cike da buri

William Ruto

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Uhuru da mataimakinsa Ruto sun dade da raba gari

Mutanen da ke kai-komo a kofar karamin shagon sayar da kayan masarufi da ke tsakiyar garin Kosachei a yammacin kasar Kenya na bayyana mataimakin shugaban kasa William Ruto, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben da za a yi ranar 9 ga watan Agusta, a matsayin jajirtaccen manomi. 

Mista Ruto daya ne daga cikin manyan manoman masara na Kenya. Babbar gonarshi da ke kusa da katafaren katin sayar da kayayyaki alama ce da ke tabbatar da hakan.

Mata na sayayyar kayan amfani kamar na lambu da kayan marmari har da kwai a gonar Ruto, domin sayarwa a kasuwannin da ke garuruwa mafi kusa, yayin da maza ke ayyuka kamar na lebura a gonar.

Tsaye a bayan katuwar kofar shiga gonar da aka kewaye da karafa, ‘yan sanda ne da ke gadin gonar.

Mista Ruto ya mallaki manyan filaye da gonaki a sassa daban-daban na Kenya, ana kuma nuna damuwa kan hanyar da ya bi ya mallake su.

A watan Yunin 2013, babbar kotun kasar ta bukaci ya mika gonarshi mai girman eka100, ya kuma biya wani manomi diyya kan zargin kwace masa gona lokacin tashin hankalin da aka yi gabanin zaben shekarar 2017. Sai dai Ruto ya musanta aikata ba daidai ba.

A wannan zaben yana mara wa dan takarar shugaban kasa Raila Odinga ne, amma a yanzu suna kalubalantar juna a neman shugabancin Kenya, abin da ya bayyana karara yadda ‘yan siyasa ke kokarin hada kai a jam’iyyu domin yin kawancen da zai ba su nasara.

Jaridar Kenya Daily Nation, ta rawaito Mista Ruto yana jin dadin yadda magoya bayansa ke karuwa. Sai dai a kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya-bayan nan da Mista Ruto ya yi watsi da ita, ta nuna sun nuna babu rata tsakanin shi da Mista Odinga wato kashi 37 da 48.

Mazauna Kosachei, suna fatan zai yi nasara zai kuma taimakawa manoma domin fadada ayyukansu ta yadda Kenya za ta dogara da manomanta wajen samar da wadatacciyar cimaka.

"Makwabci na gari ne da ya koya mana yadda za mu yi noma. A lokacin da yake ministan noma, ya ba mu tallafin taki.

A lokacin farashin taki ya yi tashin da ba a taba gani ba. Shi ne kadai ya fahimci kukan manoma da bukatunsu ya kuma tsaya mana," in ji Mama Sasha, mai sayar da kayan lambu.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mama Sasha (dama) dauke da kaebeji a hannunta, da kawayenta a kasuwar garin Kosachei
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gonar Mista Ruto tana yankin Uasin Gishu, wadda tare da kasashe makwabta suke noma yawancin masarar Kenya.

Su ke kai wa kamfanin yin abinci da ake amfani da masara wajen sarrafawa, an kuma samu takaddama kan batun biyan kudi.

A shekarar 2018, aka yi wa kamfanin rajista da sunan matar Mista Ruto, sannan a lokacin dansa na gaban kotu kan batun sama-da-fadi da kudaden masara na miliyoyin kudin kasar Shiling, amma hukumar yaki da rashawa ta kasar ta wanke shi tare da cewa ana yi wa mahaifinsa bita da kullin siyasa.

Makwabtan Mista Ruto a Kosachei sun kare shi, inda suka ce ana tsangwamarsa ne shi. Sun ki amincewa da duk wata suka da ake yi a kansa, tare da dora laifin kan Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ya bayyana karara ya karkata ga Mista Odinga, bayan sun raba gari da mataimakinsa bayan zaben wa’adi na biyu.

A gare su, Mista Ruto shi ne silar habakar arzikinsu, "idan kuma ya yi nasara, ta su ce baki daya".

"Idan Maama mai sayar da kayan lambu ta samu jarin kasuwanci daga gonarsa, ta yaya ba za mu so shi ba," in ji Mama Sasha, lokacin da take nuna mana manyan kabeji da wani ganye da ake miyar gargajiya da shi, kuma duka a gonar Mista Ruto take sarowa.

Rumfar da take sayar da kayan ba ta da nisa da katafariyar gonar Ruto. Ya yi musu alkawarin zai kara taimakawa bunkasa noma a yankin, da rage farashin kayayyaki domin su wadata.

Mista Edward Barngetury

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manomi Edward na son a daukewa manoma haraje-harajen da ake kakaba mu su

Edward Barngetury, manomin masara, da sayar da madara da nama, gonarsa ta kai girman eka 40 a wajen yankin Nandi, ya ce tsadar taki ce ta sanya manoma suka rage amfanin gonar da suke shukawa.

"Babban abin da ke damunmu shi ne rashin tabbacin farashin taki zai koma yadda yake a baya ko a samu ragi. Idan an samu daidaiton farashi a kasuwa, mutane za su samu damar lissafin abubuwan da suke bukata," in ji manomin mai shekara 33, kuma mai ‘ya’ya biyu.

Ana kokarin ganin an rage farashin masara a yankinsu, "Za mu so Mista Ruto ya rage haraje-harajen da aka karba hannun manoma.

Abubuwa sun yi matukar tsada musamman kayan abinci, amma duk da haka muna son kara adadin da muke nomawa," in ji Mista Barngetuny.

Ya yi watsi da sanarwar baya-bayan nan ta cewa an ba da tallafi ga manoma masara, ya ce lamarin salo ne na ‘yan siyasa kan zaben da ke tafe a watan gobe.

"Salo ne kawai na jan hankalin ‘yan Kenya su fito kada musu kuri’a."

Wani fannin noman mai farin jini da bunkasa shi ne fannin madara, wanda mutanen yammacin Kenya irinsu Kalenjin suka yi fice ta wannan fannin.

A baya an jiyo Mista Ruto na jinjina musu, har da wani fitaccen nau’in kayan kwalam da ake yi da nono mai suna Mursik.

Nelly Kulei ya shafe shekara kusan 20 yana kasuwancin mursik, ya koka kan wannan shekarar ta zo da matukar tsauri.

Nelly Kulei

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nelly Kulei mai saida mursik

"Muna fama da karancin madara, da kuma tsadar rayuwa. Muna fatan abubuwa za su sauya bayan kammala zabe," in ji wata uwa mai ‘ya’ya biyar da ke bayanin yadda ake hada mursik.

Yankin Kalenjin sun fi samar da shugaban Kenya mafi dadewa kan karaga, wato tsohon Shugaba Daniel arap Moi, da ya mulki kasar na shekaru 24 .

‘Yan siyasa na amfani da garin Eldoiret domin tattaunawa kan batun siyasar abin da ake kira "Bunge la Mwananchi", na ‘yan majalisa jam’iyyar Swahili for People's Parliament.

Tsohon dan majalisa Dan Langat wanda shi ne jagoran da ya maye gurbin Mista Moi, ya ce al’ummar Kelenji su hada kai domin mara wa Mista Ruto baya.

"Muna fatan Mista Ruto zai zama shugaban kasa, zai kuma daga martabarmu a kasar nan," in ji shi lokacin da yake yi wa dandazon mutanen yankin jawabi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Eldoret ya zamo gari na hudu mafi bunkasa a Kenya. Garin cike ya ke da ‘yan kasuwa da yawanci ke sayar da amfanin gona.

Sannan akwai manyan masakun tufafi, masu dubban ma’aikata. Daya daga cikinsu ita ce masakar Zaritex, dan kabilar Luo mai suna Daniel Odhiambo ne ya mallake ta.

Ya ce duk da Eldoret ke cike da tashe-tashen hankula, ba shi da niyyar komawa mahaifarsa Kisumu, saboda baya fargabar za a far masa saboda kabilar da ya fito.

 Ya shaida mana kusan kashi 50 na ma’aikatansa ‘yan Kalenji ne, kuma suna aiki yadda ya dace.

"Hukumomin tsaro anan su na kokari matuka wajen fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya," in ji Mista Odhiambo, a lokacin da yake nunawa wani ma’aikaci yadda zai auna wani yadi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Tabitha Mumbi, mai shekara 40, ta ce fannin ya samarwa miliyoyin ‘yan kasar ayyukan yi.

"Ina sayar da mtumba, iyayena sun bani kyakkyawan ilimi har matakin difiloma, kuma da wannan kasuwancin na ke kula da karatun ‘ya’yana," in ji ta.

Ita da sauran ‘yan kasuwa ba sa son yin tsokaci kan siyasar Kenya, amma sun amince kasuwar na bukatar kyakkyawan tsari, domin tattabar ana shigo da ingantattun kayan gwanjo daga kasashen waje.

"An maida mu tamkar bola. Yawancin suturar da ake kawo mana tsummokara ne, ba su da inganci sam, da kyar muke sayarwa bare kuma samun riba," in ji Violet Nyambokho 50, wadda ta shafe shekaru 15 tana sayar da dan tofi na gwanjo.

,.

Su ma ‘yan wasan tsalle-tsalle na da kyakkyawan fata idan Mista Ruto ya zama shugaban kasa.

Har yanzu ba a kammala gyaran babban filin wasa na Kamariny, wanda Mista Ruto ya yi alkawarin za a karasa a shekarar 2017 ba.

"Yawanci ba a cika taimakawa fannin wasanni ba. Dalilin da abubuwa ba sa tafiya yadda ya dace ke nan a fannin.

Hatta wuraren wasannin musamman fannin tsalle-tsalle, babu wadatattun kayan aiki," in ji mai horas da ‘yan wasa Peter Bii, ya kuma dora alhakin hakan ga ‘yan kwangilar da aka bai wa aikin gina filin wasannin.

Ya ce yawancin ‘yan wasa idan sun zo atisaye ba sa iyawa." Mista Ruto na bukatar yin garanbawul a hukumwar wasannin Kenya, saboda a yanzu cike ta ke da tsofaffi, wadanda yawanci ‘yan ritaya ne, da ba sa iya kawo ci gaba a hukumar, ana bukatar sabbin jinni, da sabbin dabarun habbaka fannin.’’

Mai horas da ‘yan wasan ya ce, ya kamata Mista Ruto ya nuna musu shi cikakken dan wasa ne ta hanyar yin nasara a tseren da ke gabanshi na zaben shugaban kasa aranar 9 ga watan Agusta.