Abin da ya sa kiwon lafiya ke taka rawa a zaɓen Kenya

Kenya

Tsarin kashe kudi na Herima Mwakima ya fada cikin rudani, bayan tasowar wasu matsalolin rashin lafiya biyu.

Matar, 'yar Kenya, tana aiki a Dubai a matsayin mai riƙo, kuma tana ɗan samun abin da ba a rasa ba, da take amfani da shi wajen inganta rayuwar 'ya'yanta matasa biyu.

Amma sai wani ƙanenta ya yi rashin lafiya, kuma bayan wasu watanni ita ma ta yi.

Yana fama ne da ciwon koda mai tsanani, don haka yana buƙatar wankin koda, yayin da ita kuma aka gano tana da wata cuta mai sanya tsananin zafi a mahaifarta.

Rayuwa ta yi wuya a kasar da ke fama rashin tsarin kiwon lafiya mai inganci, don haka shiga irin wannan hali, na iya karar da duka ɗan abin da mutum ya mallaka.

Ba shakka Mwakima na cikin mawuyacin hali, yayin da muke magana a wani daki mai haske a gidan 'yar uwarta a Likoni, wani yanki na birnin Mombasa na gabar tekun Kenya.

Da alama matar, mai shekara 45, ta gaji sosai duk ta rame, tana cikin magana ta dakata ta yi tagumi.

Ta bayyana cewa dole ne ta dawo daga Dubai don ta taimaka wa dan uwanta, Sylass, ta hanyar amfani da kudin da ta tara wa ‘ya’yanta.

Sauran dangi sun ɗan agaza, ko da yake dama haka aka san iyali.

Sylass Mwakima ya zauna kusa da ita yana saurara. Yana murmushin godiya a yayin da take magana.

Zazzage bakin aljihu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan sanannen labari ne saboda yawancin 'yan Kenya ba za su iya samun sauƙin samun lafiya ba.

Kusan hudu cikin kowane ’yan kasar biyar ba su da kariyar lafiya kwata-kwata.

Kashi 20 cikin 100 na al'ummar kasar na cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIF) kuma kashi daya na iya biyan kudin kiwon lafiya da asibitoci masu zaman kanus.

Sauran kuwa ala tilas ne su yi amfani da tsarin da ake da shi duk da lalacewarsa, ga masu hali kuwa su zazzage bakin aljihunsu.

Ya zuwa yanzu ba dole ba ne shiga tsarin inshorar lafiyar, amma ana rijistar masu sha'awa a karshen shekara, idan har sabon shugaban kasa da gwamnati wanda za a zaba a ranar 9 ga watan Agusta sun tsaya kan tsare-tsaren gwamnatin mai barin gado.

Ms Mwakima ta ce shiga shirin na NHIF ba shi da sauki.

Watakila za ta iya samun shilling 200 a kowane wata, in ji ta. Amma ta ce dole ne sai ta koma bakin aiki kuma hakan ba zai yiwu ba sai an yi mata tiyatar ciwon da ke damunta a mahaifarta.

"Yana da wuya a gare ni saboda ina jin zafi, ga shi ina zubar da jini mai yawa. Don haka ba zan iya yin komai ba saboda ina jin rauni," in ji ta cikin murya mai ban tausayi.

Ta yanke shawarar neman taimakon kuɗi daga ƴan unguwarta

Filin yakin neman zabe

Manyan ‘yan takarar shugaban kasa William Ruto da Raila Odinga na da manufofin da suke fatan za su magance matsalar kiwon lafiya da Mwakima da sauran 'yan kasar ke fuskanta.

Mista Ruto ya ce zai rage tallafin da NHIF ke bayarwa duk wata zuwa shilling 300 ga kowane gida.

Mista Odinga ya yi alkawarin samar da abin da ake wa lakabi da Babacare, wata tsarin inshorar lafiya mai taken sunan da ake kiransa da shi na Baba.

Ya ce hakan na nufin samar da lafiya kiwon laiya mai araha, mai sauki da inganci.

Haka kuma tsohon Firaministan na son kafa asusun kula da masu bukatar gaggawa.

Amma duk wani sauyi da za a yi ba shakka zai zo wa Mwakima ne a makare.

"Ina dogara ga Allah ne kawai, zan iya samun taimako kuma zan iya samun sauƙi,'' in ji ta.

Tana gama fadin haka ta yi sallama, ta jingina a jikin wani buhun siminti, tana murmushi cikin tsananin ciwo, da yayanta a gefenta.

Bayan mako guda, na sami labarin cewa ta yi nasarar tattara kuɗin kuma an yi mata tiyata.

Ta ce: "An yi aiki lafiya, na gode Allah" kamar yadda ta rubuto mina WhatsApp.

Yanzu, watakila, za ta iya komawa don taimaka wa 'ya'yanta da burinsu, domin makomarsu har yanzu ita ce fifikonta.