Matar da ta tsaya takarar gwamna 'duk da kushe ta da maza ke yi'

Asalin hoton, WAVINYA_NDET
Wavinya Ndeti ta dage, duk da yunkurin muzanta nasarorin da ta samu a fannin ilimi da kuma kalaman ƙyamar baƙar fata kan aurenta, inda ta zamo kan gaba cikin masu neman kujerar gwamnan wata babbar karamar hukuma a babban zaben kasar Kenya da ke tafe.
Matar 'yar shekara 54 da ke da ƴaƴa huɗu, ta shaida wa BBC cewa dole ne ta "dage" saboda mazan da take fafatawa da su na kallon mata a matsayin ragwaye.
Madam Ndeti ta kara da cewa yunkurinta na zama gwamna a gundumar Machakos da ke kusa da Nairobi babban birnin kasar, ya yi ta gamuwa da cikas.
Ta ce mutane da dama sun rika jifan ta da bakaken maganganu da kushe iri-iri, amma duk da haka ba ta ja da baya ba.
“Sa’ad da duk aka nufo ni da irin wadannan, sai in ji na kara samun ƙwarin gwiwa, suna kara karfafa min tunanin cewa lallai a kan dai-dai nake’’in ji ta.
A shekarar 2007, Ndeti ta doke maza 17 inda ta zama 'yar majalisa ta farko a Machakos, mai wakiltar mazabar Kathiani.
Yanzu tana fafatawa da maza uku a zaben da za a gudanar a ranar 9 ga watan Agusta, tare da zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa.
Gwamnoni ne ke kula da makudan kudade, kuma ana sa ran za su jagoranci ci gaba a kananan hukumominsu.
Wannan dai shi ne karo na uku da Ndeti za ta yi yunkurin neman kujerar gwamna.
Idan aka zabe ta, za ta zama gwamna mace ta farko a gundumar Machakos.
Tafiyarta ta siyasa ba ta da sauƙi domin ta sha fuskantar matsi da tambayoyi game da sahihancin takardun karatunta da rayuwar iyali a tsakiyar maza masu adawa da ita.
Ta yi digiri a fannin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa daga Jami'ar South Bank ta Birtaniya.
Sannan ta yi digiri na biyu a fannin nazarin tsarin kasuwanci da zane-zane daga Jami'ar City, ita ma a Burtaniya.

Asalin hoton, WAVINYA NDETI
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta auri wani Bature dan Najeriya Marigayi Dolamu Henry Oduwole, wanda ta hadu da shi tun lokacin da take karatu a Landan.
Masu suka dai sun yi mata lakabi da bakuwa saboda aurenta da wani bako amma ta dage a kan cewa ita ‘yar Machakos ce.
Machakos na ɗaya daga cikin larduna 47 na Kenya kuma kusancinsa da Nairobi ya sa jagorancinsa na da muhimmanci.
Ndeti ta shaida wa BBC cewa "Abu daya da zan iya bayar da tabbacin za a samu shi ne daidaiton jinsi a gundumar Machakos idan aka zabe ni gwamna."
Garin, gida ne ga dumbin al'ummar Kamba, da yawancin shugabannin siyasar kasar, ciki har da Ndeti, da kuma jagoran 'yan adawa kuma dan takarar shugaban kasa Raila Odinga.
Sauran ‘yan siyasa mata da suka sha suka saboda aurensu da wasu da ake kira ‘yan waje sun hada da Cecily Mbarire, wacce ke neman takarar gwamna a karamar hukumar Embu.
An haifi Mbarire a garin Embu da ke gabasshin kasar kuma ta auri dan Kenya daga Teso a yamma.
Ta taba kai karar wani mutum da ya aika mata da sakon kar ta kwana yana barazanar kashe ta kuma ya kira ta karuwa.
Ita ma 'yar majalisar dokokin yankin Suba ta Arewa, Millie Odhiambo ta sha suka kan aurenta da wani dan kasar Zimbabwe.
Maza ’yan siyasa kuwa da suka auri ‘yan kasashen waje ba sa fuskantar irin wannan barazana.

Asalin hoton, @WAVINYA_NDETI
Wani dattijo na al’ummar Kamba, John Mutua, ya ce ana sukar mata domin a yawancin al’adun Kenya ana ganin suna ficewa daga gidajensu na aure.
Ana samun cin zarafin mata hatta a majalisar dokokin kasar.
A yayin wata zazzafar muhawara da aka yi a majalisar dokokin kasar kan gyare-gyaren da aka yi wa dokokin tsaro a shekarar 2014, Ms Odhiambo ta zargi abokan aikinta maza da marinta.
Ta ce wani dan majalisa ya cir rigarta, wani kuma ya yaga, yayin da wani ya cire mata wando.
Daya daga cikin ‘yan majalisar da ake zargi ya musanta hakan.
Ms Odhiambo ta ce ta rubuta takardar korafi ga shugaban majalisar amma ba a dauki mataki ba.
Duk da wadannan munanan al'amura, Kenya ta samu gagarumar nasara wajen sanya mata a shugabanci.
Kasar ta samu mace ta farko mai shari'a, Martha Koome, a watan Mayun 2021.
An kuma zabi mata uku Anne Waiguru, da Charity Ngilu da kuma marigayiya Joyce Laboso a karon farko a matsayin gwamnonin kananan hukumomi a shekarar 2017.
Sama da mata 10 ne suka tsaya takara a wannan zabe kuma shida ne ke kan gaba a kananan hukumominsu.
Kuma a matakin kasa, uku daga cikin ’yan takarar shugaban kasa hudu na da mataimaka mata, abin da masu sharhi suka bayyana a matsayin wani ci gaba mai cike da tarihi.
Sun hada da tsohuwar Ministar Shari'a Martha Karua, wacce za ta zama mataimakiyar shugabar kasa mace ta farko a Kenya, idan Mr Odinga ya doke mataimakin shugaban kasar William Ruto.

Asalin hoton, Getty Images
Ms Karua ta shaida wa BBC cewa nuna banbancin jinsi ya kasance babban kalubale a tsawon shekaru uku da ta yi a fagen siyasa, kuma har yanzu akwai matsala.
"Irin zagin da muka fuskanta shekaru 30 da suka wuce na nan tare da mu amma abin ya dame mu," in ji ta.
Ms Karua ta kara da cewa tana magance zage-zagen ta hanyar yin watsi da su da kuma "maida hankali kana bun da take hankoro ".
Ta ce adadin matan da suka tsaya takara ya karu a tsawon shekaru amma har yanzu bai kai ga inda ake so ba, la’akari da cewa mata su ne kashi 50.5% na al’ummar kasar, kamar yadda kidayar 2019 ta nuna.
Hukumar zabe ta ce adadin mata masu kada kuri’a ya kai kashi 49%.
Mista Ruto dai shi ne dan takarar shugaban kasa daya tilo da bai zabi mace domin yi masa mataimakiya ba, amma ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta tabbatar da cewa an nada mata kashi 50% cikin dari na mukaman gwamnati.
Wani manazarci Nerima Wako ya ce an samu gagarumin sauyi a siyasar Kenya.
Ta shaida wa BBC cewa, “Yanzu da yawa daga cikin mata ne ke neman mukaman siyasa kuma suna tunanin daukar nauyin shugabancin siyasa sabanin yadda suke a baya a lokacin da suke jin tsoro saboda cin zarafi da tsangwama,”











