Abin da janye tallafin jinƙai da Birtaniya ke shirin yi ke nufi ga wani asibitin Sudan ta Kudu

Kenya

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta daina bayar da agaji ga asibitocin jihohi tara a Sudan ta Kudu daga ranar 1 ga watan Agusta, lamarin da ke kara haifar da fargabar cewa matakin zai kara gurgunta tsarin kiwon lafiyar da dama can yana cikin wani hali.

Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga ta je daya daga cikin asibitocin da lamarin ya shafa domin ganin ko wane irin bambanci yanke ba da tallafin zai haifar.

Marasa lafiya na kwance a gadajen marasa galihu suna lullube kansu da wata guntuwar rigar gargajiya, wadda aka fi sani da kitenge.

Ganin yadda asibitin ya lalace, da mamaki yadda komai ya sauya tun daga 1964.

Amma a cikin shekaru hudu da suka gabata an dan samu ci gaba.

Dr Dut Pioth ya zama likita na farko a Sudan ta Kudu da aka tura wurin.

Yayin da yake jagorantarmu zagayen duba yadda abubuwa ke tafiya a sashen tiyata, Dr Pioth ya ce: “Lokacin da nake aiki a matsayin likita, na san cewa akwai majinyata da yawa da suka rasa rayukansu saboda babu wani likitan fiɗa da zai yi ƙoƙarin taimaka musu”

An haifi Dakta Pioth a Aweil ta arewa, da ke arewacin Bahr el Ghazal, ya samu horon zama babban likitan fida a Juba, babban birnin kasar, sannan ya dawo don taimaka wa al’umarsa.

Har yanzu dai wannan shi ne asibiti daya tilo a jihar da ke da mutane miliyan daya da dubu dari uku, kuma Dakta Pioth ne kawai likitan fida na gwamnati da aka dauka don gudanar da ayyukan gaggawa.

Yanzu dai ya fuskanci matakin da ba zai taba yiwuwa ba na ko dai ya tafi, saboda za a yanke tallafin da Birtaniya ke bayarwa a asibitin, wanda ke nufin ya yi asarar kusan dukkan kudaden shigarsa.

Kenya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sudan ta Kudu ta samu ‘yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011 kuma tun daga shekarar 2012, kasar Birtaniya ke gudanar da asusun kula da lafiyar kasar HPF don tallafa wa kanana da manyan cibiyoyin kiwon lafiya a kasar.

Tana samun ƙarin tallafi daga sauran masu ba da gudummawa kamar Tarayyar Turai EU, da Kanada da Amurka da Sweden.

Bayan shawarar da gwamnatin Birtaniya ta yanke a shekarar 2020 ta rage kasafin tallafinta daga kashi 0.7 na yawan kudin shiga na kasa zuwa kashi 0.5 an rage yawan shirye-shirye a duniya.

A Sudan ta Kudu, HPF, wacce ke ba da magunguna, da kayan aiki da kuma bayar da gudummawa wajen biyan albashi, na shirin yanke tallafi ga asibitocin jihohi tara nan da 1 ga watan Agusta, ciki har da na Aweil.

Data Pioth yana samun dala 1,700 kowane wata daga HPF yayin da gwamnatin Sudan ta Kudu ke biyansa dala biyar kacal, ba zai iya ci gaba da tallafa wa matarsa ​​da ’ya’yansa ba da zarar wannan matakin ya fara aiki.

“Idan ba na nan, galibin majinyata musamman ma masu fama da larurar gaggawa za su sha wahala. Zan iya yi wa mutum 50 tiyatar gaggawa sannan in yi 70 wadda ba ta gaggawa ba, don haka ban san me zai faru ba idan na tafi’’.

“Ban san wanne mataki zan dauka ba,” in ji dakta Pioth, yana magana idonsa ya yi ja.

Asibitin farar hula na Aweil ya sami jigilar magunguna na karshe daga HPF a watan Yuni, kuma Jackson Atak, majinyaci mai ciwon kafa, ya ce yanzu dole ne ya rika sayen magani da kudinsa.

Kenya

Kasar Birtaniya ta fara janye tallafin jin kai kan lafiya da take ba wa Sudan ta Kudu a watan Afrilun bana.

Fiye da ƙananan cibiyoyin kula da lafiya 200 sun rasa kuɗinsu, kuma ana jin tasirin hakan.

Na yi tukin sa’o’i biyu a arewacin garin Aweil duk da laka a manyan titunan zuwa iyakar Sudan ta Kudu da Sudan, inda na isa wata cibiyar lafiya ta Manyiel.

Daraktan lafiya na gundumar, Joseph Atem, ya yi mini jagora zuwa ofis ɗin da ke cike da kura kuma zuwa wurin da ake ba da magunguna a baya.

Yayin da muke buɗe tagogin, muna iya jin ƙarar jemagu.

Saboda janye tallafin na HPF, babu komai a cikin kwalayen magungunan, sai wasu tsirarun magungunan rigakafi, da na zazzabi da ruwan gishiri da suga.

Asibitocin haihuwa ma da alama na cikin wani yanayi mafi muni, don hatta gadajen ma sun yin duƙun-duƙun.

Dakta Atem ya gaya mani ma’aikacin Lafiyar da ke kula da asibitin ya bar wajen, lokacin da HPF ta daina biyansa.

A kan hanya, na ziyarci Angelina Akuec wata ungozoma.

Daya daga cikin wadanda take yi wa aiki Mary Adua ’yar shekara 27 na tare da mu, tare muka sunkuya muka shiga bukkar Akuec.

Kenya

Ta riƙe wani ƙarfe na gargajiya a cikin Adua don sauraron bugun zuciyar jaririn sannan ta yi amfani da hannayenta don jin halin da jaririn ke ciki.

Duk cikinsu ba su san tsawon lokacin da Adua ta kwashe da fara nakuda ba, amma ungozomar na tunanin ta zo nan ba da jimawa ba.

"Asibitoci basu da kayan aiki, yin gwajin ciki na da matukar wahala, haka kuma, a lokacin nakuda ya fi muni saboda asibitoci masu kyau sun yi nisa daga inda nake sauka," inji Adua.

To, ko me gwamnatin Sudan ta Kudu take yi game da wannan kalubale?

Tuni dai ake zargin shugabannin da ke babban birnin kasar da yin sakaci sosai bayan yakin basasar da aka kwashe shekaru biyar ana yi wanda ya durkusar da kasar.

Kuma a yanzu bayan cin hanci da rashawa, da tabarbarewar tattalin arziki, babu kudi a asusun gwamnati.

Sabon ministan lafiya Yolanda Awel ya ce har yanzu kasar na bukatar taimako.

"Gwamnatin Sudan ta Kudu na son inganta fannin lafiyar, kuma ta fara shirin yin hakan, ta hanyar samar da kudade," in ji Awel daga babban ofishinta da ke Juba.

"Za mu yi hakan ne ta hanyar kula da yawancin cibiyoyin kiwon lafiyar mu amma har yanzu muna bukatar taimako’’.

Mun tura sakamakon rahotonmu da tasirin da muka gani na rage kudaden zuwa Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya.

Wani mai magana da yawunsa ya shaidawa BBC cewa "Birtaniya na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan masu bayar da agaji a Sudan ta Kudu kuma a bana asusun kiwon lafiya mai samun goyon bayan Burtaniya zai tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya 577 a fadin kasar."

Da muka koma asibitin Aweil, Dakta Pioth bai yanke shawarar ya zauna, ko ya tafi neman wani aiki ba, amma yana fatan gwamnatin Birtaniya ba za ta rage kudaden ba.

"Waɗannan mutanen suna buƙatar taimakonsu da gaske, suna buƙatar taimakonsu da yawa. Ba mu da ƙarfin da za mu zauna mu kaɗai," in ji shi.