'Ƙawayen Isra'ila sun fara ƙaurace mata': Ƙasashen duniya sun fara juya wa Netanyahu baya

Un enfant attend de la nourriture à Gaza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙananan yara na fama da yunwa sanadiyyar toshe hanyoyin kai agaji zuwa Gaza da Isra'ila ta yi
    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Rédacteur en chef pour l'International, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekaru biyu da suka gabata, Hamas ta tsara tare da ƙaddamar da hari kan Isra'ila. A Isra'ila kuwa Firaiminista Benjamin Netanyahu na da amannar cewa Falasɗinawa mutanen ne da suka kamata a yi maganin su.

Sannan kuma a ɓangare daya ya zargi Iran da kasancewa babbar barazana.

Netanyahu bai sassauta a wannan ƙuduri nasa ba, to sai dai ya bar Qatar ta riƙa narkar da kudi a Gaza.

Wannan ya ba shi damar mayar da hankali kan manufofinsa na ƙasashen waje: wato ci gaba da kalubalantar Iran da kuma koƙarin gyara alaƙa da Saudiyya.

A baya, Amurka ƙarƙashin shugabancin Joe Biden ta yi tsammanin cewa ta kusa samar da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Isra'ila da Saudiyya.

To amma ashe abin ba haka ba ne.

Netanyahu ya ƙi ya yi bincike kan kura-kuren da gwamnatinsa da sojojin ƙasarsa suka ya, waɗanda suka bai wa Hamas damar ƙaddamar da mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoba 2023.

Har yanzu ba a warware saɓanin da ke tsakanin Yahudawa da Larabawa ba kan iko da wani yanki da ke tsakankanin Rafin Jordan da Meditaraniya, wanda aka kwashe tsawon lokaci ana fama da shi.

Kuma wannan rikici na ƙara faɗaɗa yana neman rikiɗewa zuwa gagarumin yaƙi kwatankwacin wanda aka samu a shekarun 1948 da kuma 1967.

Gabas ta Tsakiya ta sauya tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, kuma a yanzu kimanin shekara biyu bayan harin, rikicin na Gaza ya kai wani mummunan mataki.

Des habitants de Gaza tiennent des casseroles pour tenter d'obtenir de la nourriture.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙungiyoyin agaji sun yi gargadi game da masifar yunwa da za a iya samu a Gaza

Ƙawayen Isra'ila na ƙaurace mata

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hatta ƴan jarida ma na shan wahala a koƙarin kawo rahoton abubuwan da ke faruwa a Gaza.

Isra'ila ta haramta wa kafafaen yaɗa labarai na ƙasashen waje ɗauko rahoto a Gaza.

Ƴan jarida na Gaza na bakin ƙoƙarinsu, kuma kusan 200 daga cikin su sun mutu a bakin aiki.

To amma a bayyane take cewa Hamas ta aikata laifukan yaki lokacin da ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila a ranar 7 ga wata, inda ta kashe mutum 1,200, mafi yawansu fafaren hula. Haka nan kuma Hamas ta yi garkuwa da mutane 251, inda har yanzu ake kyautata zaton cewa akwai guda 20 da ake riƙe da su a Gaza waɗanda ke raye.

A ɓangare ɗaya kuma akwai hujjoji ƙarara da ke nua cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi tun daga wannan lokaci.

Daga cikin irin waɗannan hujjoji akwai jefa fararen hula cikin ƙangin yunwa, kisan dubun dubatar mutane waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da lalata kusan ɗaukacin biranen yankin.

Yanzu haka akwai takardun umarnin kama Mista Netanyahu da tsohon ministan tsaro a gwamnatinsa kan zargin laifukan yaƙi, wadda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta bayar. Sun musanta laifin.

Haka nan Isra'ila ta yi Allah-wadai da shari'ar da aka shigar a Korun Duniya bisa zargin su da aikata laifukan yaki kan Falasɗinawa, shi ma Isra'ilar ta ce ba gaskiya ba ne.

To amma a yanzu Isra'ila na rasa ƙawayenta. Ƙasashen da suka goyi bayanta, bayan harin 7 ga watan Oktoba a yanzu hakurinsu ya ƙare kan abubuwan da ake aikatawa a Gaza.

Rahotanni na nuna cewa hatta shugaban Amurka, babbar ƙawar Isra'ila, Donald Trump ya ƙule da Netanyahu bayan da Firaiministan na Isra'ila ya mamayi Amurka wajen kai hari a Syria, kan sabuwar gwamnatin da Trump ya amince da ita.

Ƙasashe da dama waɗanda a baya suke goyon bayan Isra'ila yanzu sun daɗe da dawowa daga rakiyarta.

Une mère à Gaza avec son enfant souffrant de malnutrition.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata uwa dauke da yaronta da ke fama da tsananin yunwa a Gaza

Hada baki wurin yin Allah-wadai

A ranar 21 ga watan Yuli, ministocin harkokin waje na Birtaniya da akasarin kasashen Tarayyar Turai da Canada da Australia da New Zealand da kuma Japan sun sanya hannu kan wata sanarwa wadda ta yi tir da ayyukan Isra’ila.

Sun yi amfani da kausasan kalamai wajen bayyana abin da ke faruwa a kan fararen hula a Gaza da kuma muguwar hanyar da ale amfani da ita wajen rabon abinci wanda gidauniyar Gaza Humanitarian ke gudanarwa, wadda Isra’ila ce ta kawo ta domin maye gurbi tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ke amfani da shi.

Bayanin nasu ya ce”Wahalhalun da fararen hula ke sha a Gaza ya kai matakin da ba a tana gani ba.”

“Hanayr da Isra’ila take raba tallafin jin-kai na da hatsari, ana fama da karamcin man fetir”’ kamar yadda sanarwar ta nuna. Akwai kuma karancin man fetur, haka nan ana take wa Falasdinawa ’yancinsu da mutuncinsu na dan’adam.

“Muna tir da wannan rabon abinci da kisan rashin imani da ake yi wa mutane, ciki har da yara a lokacin da suke kokarin samun abin sa wa a baki. Abin takaici ne a ce mutane 800 sun mutu a kokarin samun tallafin abinci.”

”Matakin Isra’ila na hana shigar da kayan agaji a Gaza ya yi muni kuma abu ne da ba za a yarda da shi ba. Wajibi ne ga Isra’ila ta rika aiki tare da ita a lokacin hutu.

Dommages sur le terrain à Deir al-Balah dans la bande de Gaza

Asalin hoton, Reuters

”Harzuka"

Sakataren harkokin waje na Birtaniya David Lammy ya fitar da wata sanarwar bayan wannan.

Babban burinsu shi ne su amince da samuwar kasashen Larabawa.

Akwai alamun cewa za a iya samun matsaya kan yarjejeiyar tsagaita wuta ta yadda fararen hula da ke rayuwa a Gaza za su samu sa’ida da kuma samun damar sako ‘yan Isra’ila wadanda ake garkuwa da su.

Sai dai akwai yiwuwar babu daya daga cikin wadannan matakai da zai iya kawo karahen rikicin na dindindin.